← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 91

Sashe 1

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
Default Paragraph Font
Normal Table
No List
https://chat.whatsapp.com/Hi7n2ddpUxZ24e1tJyREqZ
*GARGADI*.
*Wanna Labarin qirqirarrene dan haka bashida alaqa da wani ko wata, idan kinci/kaci karo da abinda yayi daidai da rayuwarka to Arashi ne, bana nufin cin mutunchi ga wani ko wata ina kuma fatan idan kinci karo da abinda yayi daidai da wani kuskure da kike aikatawa zakiyi qoqari gurin amfani da gyaran da kika gani/ka gani a ciki*.
*MAMANA TA KAINA HAJJAJU IKON ALLAH, MALAMA UMMA ISHAQ ALLAH YACI GABA DA DUBA LAMURANKI, NI NAKE RUBUTUN AMMA QARFIN GUIWAR NAKI NE*
*YABO DA JINJINA GA FIKIRARRUN MATA NA QUNGIYAR DA BABU KAMARTA, INA ROQON UBANGIJI YACI GABA DA RIQO DA ALQALUMANMU MUCI GABA DA RUBUTA ABINDA AL'UMMA ZATA YABA KUMA TAYI AMFANI DASHI.

ALLAH YASA ABINDA MUKE RUBUTAWA YA AMFANE MU DUNIYA DA LAHIRA*
*HALIN KISHI COMMENENT SECTION MUTANEN KWARAI MUTANEN AMANA, UBANGIJI YA JIBANCI LAMARINKU, MASOYAN RUBUTUNA A FADIN DUNIYA GABA DAYA INA GAISHE KU, IDAN NACE ZAN RUBUTA SUNAYE LITTAFI GUDA YAYI KADAN AMMA KUSANI, INA SONKU SABODA ALLAH KWATANKWACIN YANDA KUKE SONA NA KUMA GODE DA QAUNA*
*IYAYEN DAKI NA INA GAISUWA INA KUMA GODIYA, KU DIN KUNA DA MATSAYI NA DABAN A ZUCIYATA*
*LITTAFIN NAN DUNGURUNGUN SADAUKARWA NE GAREKI YAR UWATA AMINIYATA HAJIYA SUMAYYAH, IDAN KIKA CE KE KADAI ZAKI KARANTA LITTAFIN NAN TA ZAUNA REFUND KAWAI ZAMUYI, UBANGIJI YA JIBANCI LAMARINKI, YA TAYA MIKI, ALLAH YA JIQAN DEAR YA RAYA MIKI YARANKI*
*JAMA'AR TASKIRA IYALAN CHAIRLADY, INDAI COMMENT NE KUDIN QARSHE NE.

A TSIGE WRITER TAS IDAN TAYI KUSKURE A YABETA HAR TAJI KAMAR KANTA ZE FASHE IDAN TAYI ABIN KIRKI NA GAISHE KU*
*BAN YARDA WANI YA JUYA MUN LABARI TA KOWACCE SIGA BA TAREDA AMINCEWA TA BA.

AUDIO VISUAL, MALLAKIN ZARIA TV NE, DUK WANDA YAYI KUSKUREN DAUKAR MUN LITTAFI BA TARE DA IZINI BA TABBAS ZAMU GURFANA GABAN SHARI'A*
*YAN BATI NA GAISHE KU KYAUTA, MASU SIYAN LITTAFINA DAN SU FITAR NA ROQE KU SABODA ALLAH KU BARI, KASUWANCI MUKEYI ABINDA KUKEYI MANA KASSARAWA CE DUKDA BABU WANDA YA ISA YA HANA MU SAMUN ABINDA ALLAH YA QADDARAH AMMA KU SANI AMANA DAYA CE, IDAN KINSAN ZAKI SIYA DAN KI FITAR KI BAR KUDINKI, KUCI GABA DA YANDA KUKEYI IDAN DAIDAI NE KUN SANI IDAN MA KUSKURENE DUKA KUN SANI*
*MASU HADA MIN DOCUMENT NA HADA KU DA GIRMAN ALLAH KU BARI IYAKAR ABINDA ZAN IYA YI KENAN NAGODE*
*MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*LITTAFIN MATAR MUTUM NA KUDI NE 500 KACAL VIP (MASU SO A TURA MUSU TA PC 1K*
*PROMO PRICE 400, KI HANZARTA BIYA KAFIN FREE PAGES SU QARE ZE KOMA NORMAL PRICE DINSA*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
KO KUMA
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*MARYAM FAROUK UMAR*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA TA LAYIN 07061838488*
*IDAN KATI NE ZA"A DAUKI HOTONSA A TURA TA LAMBAR SAMA*
*VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*NAGODE*
*Free page 1*
"Wallahi Allah shine shaidata bani da masaniya akan yanda akayi kudin nan suka bata.

Kowa a nan ya gani ga lissafi nan na duk abinda ya shigo kuma ya fita saga duka companies dinmu tun farkon shekara zuwa yanzu.

Idan har duka lissafin da accountants dinmu suka kawo daidai ne tayaya za'ayi ace yanzu an sake lissafi an rasa wasu kudade?

Nidai ban ci ba sedai a sake lissafi tun daga qasa ta yuwu a nan aka samu kuskuren lissafi" AMINU BECHI ya fada cikin tsananin tashin hankali.

Sati biyu kenan da al'amura suka rikice a BECHI GROUP OF COMPANY lokacin lissafin shekara yayi bayan daya gama hada komai a matsayinsa na AG lissafi yasha banban da abinda aka bashi a rubuce da kuma tsurar kudi da suke a qasa inda aka samu rarar naira na gugan naira har Miliyan dubu biyu da dari biyar (2.5Billion) wadda bayan bashi damar yayi bincike da MD da kuma Chairman sukayi yauce ranar da aka taru duk wani daya isa a company domin jin ta yanda akayi aka haihu a ragaya.

Alhaji ZAKARIYYAH BECHI dake ta jujjuyawa a kujerarsa yana wani miskilin murmushi da babu wanda ya tantance kona menene ya kalle shi yace
"To Aminu kaida kanka kace dukka lissafin da aka gabatar maka daidai suke kuma baka karba ka saka hannu har seka bincika komai ka tabbatar da haka yake.

Sannan a iya saninmu ku biyu kuke da access da central account dinmu dakai da Chairman duk wani wanda ze shigar ko fitar da kudi bayan ku biyun seya samu approval a gurinku to tayaya kake zaton zamu yarda idan kudi ya bata kuma kace mana bakada masaniya akai kenan Chairman ne da kanshi ya kwashi kudaden ko kuma me kake nufi?"
Aminu ya kalli Chairman din da tun zamansu bece komai ba ya tallabe haba da hannaye biyu yana bin duk wani da yayi magana a cikin su da kallo, Dattijo ne da a qalla zeyi shekaru 70 zuwa sama, dukda a zaune yake amma kana kallonsa zaka san Zabgegen mutum ne Jindadin rayuwa yasa har yanzun yake da sauran kwarinsa.

Aminu ya hadiye yawu muqut saboda yanayin fuskar Chairman daya gani, bashi da yawan fara'a daman amma kuma yanayinsa na yau ya banbanta da kullum kana gani kasan zuciyarsa a kusa take koda yake ai dole, batun kudi akeyi fa, kudin daya qare rayuwarsa yana nemansu ya tara ace lokaci daya wasu su ringayi masa zari daidai dole hankalinsa ya tashi.

Seda ya daidaita nutsuwarsa kafin ya kalli MD dake jiran jin ta bakinsa yace
"Nidai na gama magana, ban ci kudin nan ba ban kuma san wanda ya dauke su ba.

Amma dai kamar yanda nace kowanne gida (sector) su sake turo mana da lissafinsu na shekara a qaramun lokaci zan sake bin komai daki daki zan zauna da duka Bank Managers dinmu in Allah ya yarda za'a gano duk ma inda kudin suka shiga" ya qarasa muryarsa na rawa kuma cike da roqo da yaqinin Alhajin ya yarda dashi ya bashi wannan damar.

Idan ya rasa besab ina ze dosa ba, abu biyu ne dole daya ya faru, dukda kasancewar Dan Chairman na cikinsa a sabgar Company basa kawo wannan relation din, ya sani kodai yayi Aman kudaden nan tas Miliyan dubu biyu da dari biyar wanda ko an siyar dashi da matarsa da yayansa da abinda ya mallaka baza'a hada wannan kudi ba abu na biyu kuma in wancan be samu ba yasan garqameshi za'a yi a prison still kuma A siyar da duk abinda ya mallaka Company ya rage Asara maganar aikin sa daman tun ranar da kudin sukayi batan dabo ya rubuta resignation letter ya ajiye dan ko be bari ba korar sa za'ayi.

"Maganar wani lokaci ko a sake bincike duk bata taso ba dan a tsayin faruwar abun zuwa yanzu da da wani abu da zakiyi tuni kayishi, just admit it Aminu kai kaci kudaden nan ka dawo dasu baki alaikum base magana tayi tsayi ba" NAZIRU BECHI ya fada yana wani zazzare masa ido
"Nima dai abinda na gani kenan, idan kuma yayi taurin kai Maigirma Chairman ina ganin a barshi da Legal department suyi aikinsu nasan su zasu sna ta yanda zasu tirsasashi yayi aman kudin ko kuma su miqashi inda ya dace" Alhaji Zakariyya ya qarasa miyar gishiri, cikin Aminu ya kada, ya ringa raba ido tsakanin Alhaji BABANGIDA BECHI da kuma YAKUBU BECHI da yake matsayin mataimakinsa AAG wanda tun fara taqaddamar kamar ma baya gurin wayarsa yake dannawa kunnensa saqale da Bluetooth tabbacin ba jinsu yakeyi ba hakan yasa ya tsayar da idonsa kan Alhaji Babangida cike da roqon ya saka baki amma seyaga ya saukar da kansa qasa bece komai ba.

Dakin ya sake daukan shiru na wani lokaci kafin cikin murya me cike da Izza irin ta wanda suka ci suka tada kai Chairman, Alhaji AUDU BECHI ya fara magana yana cewa
"Duk naji bayanan ku kuma na duba takaddun da aka rigada aka gabatar mun tuntuni.

Account general, ina so daga yanzu zuwa qarfe biyu ka gabatar da takaddar barin aikinka da kanka saboda idan muka koreka zamu bata maka career be zama lallai ka sake samun aiki a wani gurin ba, kudi kuma duk wanda ya dauka yaje dan kansa" yana gama fadar haka ya tsuke bakinsa yana kallonsu daidai.

Aminu ya sauke ajiyar zuciya me nauyi tamkar wanda ya hadiyi kunama, jiki da bakinsa suna rawa ya zame daga kan kujerarsa ya durqushe yana cewa
"Nagode Alhaji, Allah ya qara girma nagode nagode".

Naziru da Zakariyya wanda farkon maganar Alhaji yayi musu dadi, sun dana kuma ta kama suka kalli juna tareda yin signa akan idon Alhaji Babangida dake lura da duk wani motsinsu ya girgiza kai kawai.

Bazeyi kaffara ba idan ya rantse cewar shirinsu ne saboda sun nuna baqin ciki qarara da kujerar ta Aminu amma baze saka baki a cikin maganar na domin rayuwar gidansu rayuwa ce irin ta kowa tasa ta fishsheshi shida Yan dakinsu.

Tunda Aminu ya samu wannan matsayi qarara mutane da yawa a gidan suka nuna qyashi da hassada bayan rasuwar Mr Adekunle Balogun wanda shine AG na BECHI GROUP din tun kafuwarsa Alhajin bisa shawarar Legal Department da sukaga cancantar Aminun aka dorashi, shekaru biyu kenan tun kuma hawansa abubuwan da ba'a saba dasu ba suke faruwa amma wannan al'amari shine mafi girma wanda baze yuwu a dauke kai ba.

Cikin zafin ran dake nuna hassada qarara Alhaji Zakariyya yace
"Ranka ya dade (haka suke kiransa muddin sabgar data shafi aiki ce) naji kace yayi resigning kawai banji maganar dawo da kudi ba ko wani hukunci da za'a dauka akansa?"
"Da alama kunnenka ya soma samun matsala ko?

To ka tambayi na kusa da kai su maimaita maka abinda nace, maganar wanda ze maye gurbinsa for now Yakub should take over kafin mu sake zama muga abinda ya dace da ayi ina ganin mun gama abinda ya taramu you can all dismiss" Alhajin ya fada ba tareda ya kalleshi ba.

Alhaji Zakariyya ya hadiye yawun takaici ta wani bangare kuma yaji dadin cewar YAKUB BECHI ne zeyi taking over dukda sunso ace anyi confirming nasa ne take as the newa AG amma hakan ma nasarace sunyi nasu Hajiya zata qarasa aikin a gida.
Chapter 1 · 0% Book details