Sashe 59
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zancen da akeyi yanzu rabi da kwatan Gonaki da filayen da suke a Bechi mallakinsa ne saboda duk wanda ya daga fili ko gona ze siyar da an tallata masa ze siya a farashi me daraja kuma shiyasa wasu ma haka nan suke siyar masa suje wani gurin su sake siya ragowar kudinsu susha shagali yanzu idan wannan magana taje Bechi ace matarsa ta bata da tsohon ciki la shakka cewa zasuyi yayi tsafi da ita kawai.
https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 23*
Sati guda ya shude Audu na bulayin neman Zubaida sedai sama ko qasa babu ita babu kuma wanda ya ganta bare asan labarin inda tayi.
Har Zariya sukaje da Bashir gidan daya dakkota suka tarar an tashi gidan ma gaba daya titi ya biyo ta kan hanyar haka suka juyo Kano babban abinda ya qara daga masa hankali ya bazama nemanta zuwan da Baba Zayya tayi akan taje duba Zubaidan Allah ya taimake shi yana gida ranar, daya rasa abin fada mata dole ya rangada mata qaryar Zubaidan tana Bechi, kuma daman yaso yaje ya sanar dasu tana can har se bayan ta haihu zata dawo Kano to Allah be nufa ba.
Dake akwai yarda da Amana sam Baba Zayya bata kawo komai a ranta ba tunda ana hakan mace ta tafi garin su Miji haihuwa dan haka tayi musu sallama ta koma gida ta shaidawa Malam Hassan yanda akayi.
Wannan dalili ya qara zaburar da Audu ga neman Zubaidan, nadama mara amfani ta dirar masa biya hukuncin daya yanke ba tareda zurfin tunani ba.
Haka ya ringa raba kudi wa malamai akan ayi masa Addu'a Allah ya bayyana Zubaidan ya kuma kareta a duk inda take.
Cikin wannan yanayi Alhazai suka fara tashi, Binta taje gida tayi sallama da danginta ta dawo tana ta shirin tafiya sauke farali bacci ragagge takeyi saboda jiran ace su fito.
Ita sam ta manta ma da wata Zubaida balle batun ba'a ganta ba, yanda Audun be cika nutsuwa ba a lokacin yasa ta tsahirta masa, ita kadai take ta shirinta tunda dai ya sallameta ya bata Guzuri me auki ita kam ya gama da ita se jiran ranar tashi kawai takeyi.
Acan gidan Yakubu kuwa hankali kwance Zubaida ke zamanta, tsakanin Balaraba da Yakubun ba zata tantance wanda yafi tattalinta ba.
Duk wani abu da zata buqata suna mata haka nan basu barinta ta zauna shiru balle ta fada tunani ko wata damuwa a koda yaushe cikin hikima sukanyi mata nasiha akan rayuwa da qalubalen da yake tattare da ita.
A dan taqin zaman ta fahimci banbance banbance masu tarin yawa da suke cikin rayuwar Haske data duhu ma'ana rayuwar da akeyinta cikin sani da wayewa ta Addini da kuma rayuwar Bidin bidima irin wadda tayi a baya ta koma dora yinta a gidan Audu.
Yakubun jajirtaccen Namiji ne wanda yake tsaye akan lamuransa dana iyalinsa.
Ga daishi be tara dukiya tamkar dan uwansa ba amma rayuwar gidansa ta zamo abar sha'awa wadda duk me hankali idan aka bashi zabin kudi ko nutsuwa irin ta gidan Yakubun tabbas baze tsallaketa ba.
A kullum da Asuba seya dorawa matarsa da Yayansa karatu haka bayan sallar Isha'i idan sun zauna a maimakon hirarrakin banza na duniya sukan yi tasu hirar ne akan karatuttukan da sukayi.
Ya tambayesu su tambayeshi, hatta da Qaramin dansu Tijjani me shekaru uku a sannan Alqur'ani ya fara zama a bakinsa, haka qananan Hadisai da ake dorawa Yayinsa yana tsinta har idan Yakubun yana tambayarsu sukayi kuskure Tijjanin da suke kira da Alhaji ze gyara musu ga wayewa ta boko turanci yafi hausa Nuna a bakinsu kodan inda suke zaune yaren da suka fi amfani dashi kenan? wannan abin ya matuqar birgeta ya kuma zaburar da ita kan cewar itama bata makara ba tana da damar da zata nemi ilimi tana kuma burin abinda zata haifa ya tashi cikin irin wannan rayuwar ta ilimi ba irin ta gidan ubansa ba.
Zata iya bada shaidar Audun yana salloli na farilla kuma yana qoqarin yinsu akan lokaci kuma cikin jam'i, a zamansu daya tasamma shekara a watan Azumi kadai zata bada shaidar yana zuwa sallar Tarawi da kuma Qiyamullaili tun bayan daya shude kuma a ranakun girkinta dai bata sake ganin yayi ba bata sani ba ko idan yana dakin Binta.
Dama shi bame jurar Ibadar Azumi bane domin Ramadanan ma da qyar yake kaishi, bayan Alqur'ani bata tsammaci ya karanta wani littafi ba bata taba ganinsa dashi ba haka ko a magana ba zatace ga inda ya kawo misali daga cikin Hadisi ko wani littafi na Addini ba.
Ba zata manta ba akwai sanda ta taba shawartarsa shiga karatun Asuba da akeyi a masallacin dake cikin layinsu wani baqon babban Malami ne yazo yake bada karatun Fiqhu da Hadisi se Tauhidi take yace mata ai ya gama karatu, seda ya shekara biyar yana qolanta to wane karatu ya rage masa da beyi ba kuma?
Da tace ita zata ringa zuwa gurin matar Malamin da take karantar da Mata a cikin gida harya yarda bata san ya akayi ba ya dawo yace babu maganar ta tambayi dalili kuma yace babu dole ta haqura badan taso ba domin Allah ya sani tana sha'awar ta nemi ilimi shiyasa yanzun data samu wannan damar tayi amfani da ita.
Dada take ja tana biya mata karatun, dayake tasan baqi dan haka karatimu da takardar Alqur'ni be bata wahala sosai ba dukda tafi gane rubutun warshu amma da yake ta saka kanta se gashi tana ganewar in ta biya mata kuma ta ringa nanatawa kenan har seta haddace.
Balaraba ce ta sameta akan ta ringa fitowa suna daukar karatun tare bayan da Dada ta sanar mata tana yiwa Inna Zubaidan qarin karatu, daga nan itama ta zama yar Aji ta kuma maida hankali sosai akan abinda ake koya mata.
Irin nutsuwar da take tsintar kanta a ciki ta qara tabbatar mata da cewar tabbas akwai banbanci me tarin girma tsakanin rayuwar da akeyinta cikin sani da kuma ta jahilci.
Satinta uku a gidan wata safiya ta tashi da naquda, kafin nan sunje Asibiti har sau biyu Yakubu da kansa ya kaisu tareda Balaraba an dubata an kuma tabbatar da lafiyarta data abinda yake cikinta suka basu kwana goma daya zagayo suka koma kwanaki biyu kenan da zuwan nasu da safiyar ranar Laraba ta tashi da naquda nan da nan suka wuce Asibiti da ita, daman Yakubu yana nan ya jinkirta komawarsa Ikko saboda yana taraddadin ya zasuyi idan haihuwr tazo mata cikin dare gida babu Namiji daga ita se Balaraban dalilin daya saka ya daga tafiyarsa kenan saboda a Asibiti zuwansu na farko sun bashi tabbacin ba zata qara sati biyu nan gaba bata haihu ba gashi kuwa kwanaki goma sha biyu kenan da wanacn zuwan haihuwar tazo.
Cikin taimakon Allah bata dauki lokaci mai tsaho ba ta sauka, ta haifo wasu runtuma runtuman tagwaye wanda ko a Da guda daya aka haifi wannan tabbas se an jinjinawa wadda ta santaloshi se gashi har biyu ubangiji ya bata a sauqaqe cikin Aminci.
Lokacin da aka nunawa Yakubu yaran kasa cewa komai yayi se tasbihi daya ringayi a zuciyarsa.
Duk wanda yasan Ahalin gidansu baya buqatar a fada masa yaran tsatsonsu ne ze iya cewa ma ba'a taba haifar Jarirai masu kama da Mahaifinsu Malam Tijjani Kwabo da kwabo irin wadannan ba har hasken fatarsa basu bari ba abinda ya banbantasu da Audu kenan saboda shi yana da duhu kadan.
Ya rasa ta ina ze fara ma, Balaraba nata murna ta kasa tsayuwa guri daya shi kuwa tunanin waze fara shaidawa zancen haihuwar yake tayi.
Gadai Arziqi Allah ya basu wadannan ne tagwaye na farkoba zuri'ar gidansu amma haihuwar su tazo cikin rudani.
Seda ya tabbatar babu abinda ake da buqata a Asibitin kafin yacewa Balaraba zeje ya dawo.
Can kamfanin da Audu yake ginawa inda kuma nan su Musbahu suke zama ya nufa.
Yaci sa'ar tarar da Musbahun be tafi gidan Mai ba, bayan sun gaisa yace yazo ya rakashi gidansu Zubaida Amaryar Audu babu musu ya hau mota suka tafi a ransa yana mamakin meyake faruwane domin a kwanakin nan gaba daya sun lura da Baba Audu baya cikin hayyacinsa dukda be fada musu komai da yake damunsa ba amma ko gidan Mai seya kwana biyu be fito ba aikin Kamfanin ma an dakatar dayi kamar yanda ya fada yana cikin wani dan uzuri ne.
Da suka isa gidan a Mota ya bar Musbahu ya qara qofar daya nuna masa a mazaunin ta gidan Malam Hassan.
Yayi sallama cikin sa'a Malam din ya fito ya amsa a shirye yake da alama wani gurin zashi, be taba ganin Yakubu ba amma jini da kamannin fuska yasa ya gane dan uwan Audu ne dan haka yayi masa iso cikin gida bayan ya saka Baba Zayya tayi musu shimfida ta kawo masa ruwa a mutunce suka gaisa suna tambayarsa iyali.
Cikin nutsuwa da kuma sanin makamar aiki irin nasa ya warwarewa Malam Hassan duk abinda ake ciki be boye masa komai ba hatta da sakin da Audun yayiwa Zubaida da zamanta a gidansa zuwa yanzun data haihu be rage komai a ciki ba.
Malam Hassan yayi shiru cikin tsantsar jimami kafin yace
"Tabbas nayi zargin wani abu ya faru saboda irin zaryar da dan uwanka ya ringayi a gidan nan kuma alamu na rashin gaskiya sun bayyana tattare dashi sedai na kyautata masa zato na cewar koma menene nasan baze cutar mun da Zubaida ba na saka a raina dai wata matsala ce qila da yake jin nauyin sanar dani.