Sashe 31
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ki gwada wannan dinma tayi dadi wlh zaki iya ci"
"Dama mana tayi dadi a bakin daya sbaa cin gabza dole kice wannan tayi dadi" Binta ta fada tana harararta, Bara'atu ta miqe jiki babu kwari mutane duk sun tsaya suna kallonsu ga Bintan bata magana a hankali, da qafa ta tunkuda kwanon miyar ya fallatsarwa Bara'atu a jiki tana cewa
"Zoki kwashe shiyarki banma san me kika zuba a ciki ba da kike ta nacin se naci".
"Amma kedai anyi yar marasa mutunchi, yanzu da miyar da zafi ta qona mata fata fa?" Hashimu daya shigo yana saba babbar riga ya fada, Binta ta kama qugu tana masa kallon banza, sedai ta gaza ce masa komai dan yanda yayi maganar cikin hayagaga ta tabbata ze iya rufeta da duka.
Mata aka dauki surutu caaa kowa da abinda take fada.
Hashimu nata bala'i yana qundumawa Binta da Iyayenta da basu san anyi ba zagi.
Ya kalli Bara'atu dake hawayen wannan cin mutunchi data mata cikin taro, tacu kwalliyarta da Shadda Ruwan omo Bintan ta mata wankan Miyar taushe
"Ke kuma sakarya kin tsaya kina mata kuka, k wuce ki kwase me zafi a tukunya ki watsawa yar banza a wannan kodaddiyar fuskar tata" Hashimun ya sake fada daidai nan Audu ya shigo yana fama da tasa babbar rigar ya tarar dasu cirko cirko, Binta na ganinsa ta saka kukan zallar kirsa da makirci tana cewa
"Saboda ni ba yar cikinku bace shine zaku tsaneni?
Me nayi muku?
Wani abu ya taba hadani da wani a cikinku ne balle ku qwafeni kuke neman halakani"
"Wace irin magana ce haka babu dadin ji wa yake neman halakaki?" Audun ya fada yana qarasawa kusada ita.
Ta sake rushewa da kuka tace
"Ina zaune kawai Bara'atu tayo kaina gadangadan da wuqa a hannunta, a garin na tureta ta taka kwanonmiyar nan ya fantsalar mata shine cikin su babu wanda yabi kadin ba'asin nufoni da tayi da wuqa sena miyar sata fantsamar mata suka hau zagina har wannan yayan naka yana cemun jinin shadanu" ta nuna Hashimu daya qame tsabar yau yaji wadda tafishi iya hada guri bashi kadai ba gurin kaf shiru sukayi suka daskare da mamaki, Audu ya kalli Bara'atu ya kalli wuqar dake yashe a gefenta ya sunkuya ya dauka yana nuna mata yace
"Me zakiyi da wuqa da kika nufota"
"Wallahi tallahi qarya take mun" Bara'atun ta fada tana saka kuka, Baba suwaiba wadda qanwace ga goggo Fadi ce tace
"Amma kedai wannan yarinya duk yanda akayi Abokanan wasa kuke da Shaidan, yanzu wuqar da ni kika tambaya na baki kika bare muruci shine zakice ta nufo ki da ita?
Gaskiya bakya tsoron Allah yanzu ke ko kunyar idanun jama'a bakiji ba ki lafta wannan uwar qaryar da zata iya kashe Aure Allah wadaranki wlh tir da masharrancin harshe irin naki"
Nan aka sake daukar surutu kowa nayiwa Binta tofin Ala tsine.
Audu ya kalli Bara'atun dake kuka kamar me sannan ya kalli Binta data sunkuyar da kai qasa kunya ta dabaibayeta kamar qasa ta tsage ta shige ciki takeji.
Ta manta shaf a inda suke, Tsabar yanda idonta ya rufe tana neman dalilin da ze saka Audun sakin Bara'atu ya sakata hada wannan zancen da bata ma san sanda Dabarar tazo mata ba ta kwakwalwar kuma ta gaza kawo mata kalaman kare kai.
Gaba daya sun kasa kunne suji hukuncin daze sauka akan Bintan da abinda tayi sabanin haka se ji sukayi yaja tsaki ya juya buguzun buguzun ya fice daga gidan.
"Kin shiga uku Bara'atu ke kuma taki jarabawar kenan a gidan Aure to Allah yasa ta zame miki kaffara"
"Bantan uba, yau naga abinda yafi qarfina ni yasu, Bara'atu dama haka kike zaune?
Dole ki rame ai kinyi dakyau ma har yanzu kike cikin hayyacinki wannan makirci har ina?"
"Wlh bazan iya zama da irin wannan matar ba, dama ace Audun tsayayye ne da sauqi to da alama ta shanyeshi Allah sarki Dada Allah yayi bata da rabon shan takaicin suruka shiyasa ta mutu kafin a aurota dan wlh wannan tsaf zata raba Da da uwarsa kutusi"
Haka suka saka Bara'atun a tsakiya kowacce ta ringa surutunta, Binta kuwa jiki babu kwari kamar wadda aka kama da kayan sata ta shige dakin Bara'atun can qurya ta lafe a gado.
Tana jiyo surutai ana zaginta amma babu damar tankawa ta rigada ta kwafsa.
Haka ta wuni sir a daki ana ta shagalin Biki, Allah sarki Bara'atu, dukda abinda tayi mata haka ta zuba abinci da rana ta bawa Abdullahi ya kai mata bata daije da kanta ba.
Bata ma sake shiga dakin ba dan ko kaya da zata sauya Bilki ce ta dauko mata ta kuwa yiwa Binta tatas kamar zata doketa dan bata gidan abin ya faru ta tafi gidanta ta dakko abu.
Haka suka kwana.
Tun a daren ranar Abokanansa da matansu suka kai musu tsogwamin abinda ya faru suka tareshi da zancen,
"Gaskiya ka gyara gidanka Audu tun kana da hali.
Wannan hanyar da ka dakko bazata bulle maka ba, idan baka dauki mataki yanzu ba kana ji kana gani gidanka ze ruguje, ba kuma iya matanka abin ze shafa ba harda yan uwanka seta rabaka dasu.
Wlh banda qaddara ma wannan ba matar aure bace, mace babu komai a ranta se fitina da tada zaune tsaye?
Wai me ka gani a gurin yarinyar nan harya rudeka Audu?" Shamsu Abokinsa ya fada.
Audu yasha kunu yana kallonsu daidai dan kowa ya tofa ta bakinsa.
"Ana magana kayi shiru kana muzurai da hada fuska, mu nan babu wanda fushinka ze tsorata dan kar muke kallonka kasan mu mun sanka tun muna yawo babu wando, kuma gaskiya ce se mun fada maka ka dauka ko karka dauka wannan ruwanka mudai mu fita haqqin zaman tare" Iliyasu daya fi sauran zafi ya sake fada se sannan Audun ya budi baki yace
"To me kuke so nayi ko nace?
Dani daku fa duka labari mukaji babu wanda abin nan ya faru a gabansa balle ya fadi haqiqanin gaskiyar yanda akayi"
"Amma Audu baka tsoron Allah, ta yaya Mutum sama da Ashirin zasu hada baki su fadi qarya?
Idan duka matan gurin sun goyi bayan Bara'atu kana tsammanin Hashimu ma ze bi bayanta ne?" Iliyasun ya sake taso masa, saboda a bar maganar yace musu
"Naji, zan mata magana"
"Daga baya kenan, ai take a gurin ya kamata ka nuna mata kuskurenta ba wai daga baya ba yanzu ai ka bata qofar da zata taka koma wane tunda ko zakayi fada badai a gaban mutanen data muzanta wancan ba.
Wlh ni mamakinka nake Audu, a tasowarmu idan wani yace ko a mafarki ya ganka Mace tana juyaka wlh duk se mun qaryata se gashi a gaske da ranmu muna gani ka zama solobiyon banza a gaban wadda ma bata isa ba" cewar Musa.
"Ya isa haka, nace zan mata magana ko, nifa ba wai wani abu yasa nake daga mata qafa ba.
Idan na duba matakin dana taka a yanzu Mahaifinta ne sila, shi kuma a duniya bashida abinda yake so kamarta ya gayamun babu abinda zan yi na saka masa irin na kula masa da Binta wannan ne kadai dalili"
"Ai shikenan" kusan dukansu suka hada baki gurin fada tsabar takaicin da maganarsa ta qunsa musu daga haka suka watse suka barshi da Muzammilu shine be gaji da magana ba.
Washe gari kuwa da farar safiya Audu yace su fito su tafi.
Bata san da su Bara'atu zasu koma ba seda taga ana loda kayansu a mota tayi qwafa bata dai ce komai ba dan babu fuska a gurin Audun, tun jiyan dai bece mata komai ba haka kuma be sakar mata fuska ba.
Bara'atu dai duk a darare take har suka isa Kano ta wuce sabon dakinta har tsalle seda tayi saboda murna tayi dakin yan gayu.
Haka aka cigaba da rarrafa rayuwa, sauqi daya ta samu shine na aikace aikacen Binta saboda masu aiki har biyu data tarar ta dakko wanda taja musu kunne akan ko gaisuwa ta shiga tsakaninsu da Bara'atun a bakin aikinsu.
Ko a jikin Bara'atu daman me zata saka suyi mata ita?
Gaisuwa kuma babu dole a ciki ita a zauna lafiya babu ruwan kowa da kowa yafi mata.
Lantana me share share itace Mara mutunchi a masu aikin ta kuma lura tafi fada a gurin Bintan sama da Mairo me mata girki wadda Bintan ta santa ta taba zuwa gidanta kitso sau daya can qasan layinsu take Lantanar ce bata san a inda ta kwasota ba.
Matar sam batayiba, a suffa ma Astagfirulla kalar munafukai ne da ita kuma haka take a zahiri.
Ita take zuba gishiri akan ciwon zaman su da Bintan.
Yanzu da cikinta yayi nauyi ta kusa haihuwa tadan rage hayaniya da hayagagar da take mata shiyasa har take dan samun damar fita tsakar gida tasha iska.
Randa Lantana ta kunno Bintan kuwa ruwa ba zata barta ta hadiye da dadinrai ba, masifa zagi cin mutunchi da gori babu wanda bata mata, tun ba da Hadiza qanwarta tazo, ita take binta an mata aure shekara biyu baya zaman yaqi dadi suka rabu da Mijin nan ma babansu ya tasata gaba shine ta gudo gurin Bara'atun ta kwana biyu tareda Addu'ar ko Allah ze fito mata da Miji a Kano tayi aure ta huta da Fadan Babansu.
Nan fa Binta ta samu nayi, gori da yana fita a jiki da bazasu samu sararin shan iska ba, sauqi daya da bata samu goyon bayan Audu ba da tace ya kori Hadizan, da haka zasu tattaro su cika masa gida to da yake har sannan ba a koma daidai ba tun abinda ya faru a Bechi dukda da fatar baki be mata magana ko fada akan abinda tayin ba kawai ya dan dauke mata wuta ne yanda yake rawar jiki yana mata abubuwa ya rage wannan ma na bala'in mata ciwo tadai barine zuwa ta haihu dan ta kanta take yanzun shiyasa ma take sararawa Bara'atun amma da zarar ta haihu zata qaddamar da shirin da tilas ta bar gidan da kareren qanwar tata data kwaso.