Sashe 66
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wannan abin ne har yasa yayarda ze maido da Bara'atun a ganinsa hakan ze wanke laifinsa a gurinta sannan ya daidaita tsakaninsa da yan uwansa qarfin guiwar sa kuma daya samu hadin kan Binta.
Kai shi kansa ma ya sake qullewa kuma, Binta ta nuna tana son Bara'atu batayi kishi da ita ba ya auro Zubaida ta kusa haukace masa balahira babu kalar wadda be gani ba sannan yanzu kuma da kanta ta sake cewa ya maido da Bara'atu wai menene hakan ma tukunna?
Shine a birkice ko kuwa Binta ce bata da alqibla????
To duk yanda ake ciki madai ya himmatu ze maido Bara'atu, kuma kamar yanda aka saba inya nausa baya jin kira dan haka baya tsammatar akwai abinda zesa ya canza wannan qudurin.
Cikin satin ya shirya yaje Bechin, ya tara yan uwansa ya sanar dasu qudirinsa Yakubu da Baballiya ne kadai basa gurin se Hashimu da yace bashida lokacin saurar Soki burutsunsa ba kuma ze yarda dan da aka
haifa a gabansa saboda yayi kudi ya zauna yana masa fadanci ba dan haka babu shi akayi zaman
Dukkaninsu sunyi matuqar farin ciki da Al'amarin kamar yanda ya tsammata ya san kuma Yakubu se yafi kowa jin dadin maganar har ya qagu yaga farin cikin da zeyi, ya bawa Yaya Baba kudaden daya ware matsayin na sadaki sannan ya sake ware wasu akan a bata tayi shirue shiryen da zatayi.
"Aa, wannan ai kai ya kamata ka bata hannu da hannu bamu ba" Yaya Baban ya fada masa amma ya dage akan su hada duka su kai saboda ya shiryawa ransa bazasu hadu ba harse an maida Auransu tukunna saboda gani yake zama ta rainashi idan yaje gurinta yanzu, amma idan yayi haka se abin yayi kamar yan uwansa ne ma suka tursasa dawowartata karma ta gane zumudinsa tazo tace zata rama abinda ya mata.
Dasu ka kai kudi kuwa ba'a tashi daga gun ba Mala Sadi yace a shafa fatiha kawai tunda ba sabon Aure bane, a karo na biyu Audu ya sake qullo Aure Binta bata sani ba se bayan daya koma ya fada mata maganar cikin Yaren da ya ke so ta fahimta a sannan cewar "Su Babangida zasu dawo nan da sati biyu".
Ta nuna jin dadi da murnarta a fili a zuciyarta kuwa dariyar mugunta takeyi tana shirya yanda zata kwarzabi rayuwarsu a ruwan sanyi kuma ba zata sake bari su koma Bechi ba balle Bara'atu taci Arziqinsa ta silarsu.
"Se a gyara musu dakin nan na tsakar gida ko, amma harda Abdullahi zasu dawo dukda dai ya nuna mun ni ba uwarsa bace tunda Bara'atu ta bar gidan nan ko hutu ne sake zuwar mana ba" Bintan ta fadi cikin kissa, Audu yayi murmushi yace
"Hardashi duk zasu dawo shi za'a gyara masa dakin tsakar gidan dai tunda yanzu ya zama saurayi su kuma su zauna dakin Mamarsu".
Bata kawo komai ba haka bata tambayeshi dawa zasu zauna ba to ina ruwanta?
Su zauna dakin su kadai ita bataqi ma wuta ta tashi cikin dare su qone ba kowa ya huta da lissafinsu.
Haka aka fara shirye shiryen gyaran tsohon dakin Bara'atu inda kuma Zubaida ta zauna, duk a salon kissa da kisisinar data qaro kwas yasa tayi shiru tana gani ana kankare kankare da liqe liqe har qofofi aka irin wanda aka canza na dakunanta da saman Audun babu jimawa sababbin shigowa na zamani se tayi tsammin ya canza ne saboda gidan duk yayi kala daya.
Aka sake fente tsajar gida, ana ya saura kwana uku Bara'atu ta tare su Bilki da wasu yan uwan Bara'atu uku harda Hadiza qanwarta suka zo mata danki na neman magana.
Tarkacen kayan jere kadai suka taho dasu dan Audu ya fada musu ze saka mata Gado da Kujeru, Binta na daki tana baccin bayan Azahar suka iso Lantana da Mairo su na tsakar gida, Mairo na kai kawo tsakanin Kitchen da bakin famfo ita kuma Lantana tana daga jikin katanga inda Inuwa ta sauka tana zaro zance wanda duk gulma da tsegumin matan unguwa ne takeyiwa Mairon ita kuwa tafi ki mutu bata ce mata amma hakan be saka tayi shiru ba se zuba takeyi.
"Barka barka, baqi mukayi a gidan?
Daga ina?" Lantana ta fada tana miqewa sanda su Bara'atu suka shigo da ubannin buhubhuna da suka lodo su kwalla da Samiru.
Mairo ma tayi musu sannu da zuwa, ta gane Hadiza a zaman da tayi a gida dukda ta dan qara jiki amma kamanninta basu bace mata ba sannan kuma ga kamannin me gidan a fuskar Bilki hakan ya ankarar da ita cewar daga Bechi suke.
"Bismilla ku shiga tana ciki Hajiyar" ta fada musu bayan data gaidasu a mutunce, kafin suyi magana Lantana tayi tsugul tace
"Ban gane su shiga ba?
Ke haka akeyi kawai daga ganin mutane kice su shigar mata daki kina ganinsu yarkace yarkace da wasu uban buhunhuna kamar yan gudun Hijira qilama mabarata masu neman mafaka ko kinga sun miki kalar qawayen Hajiya balle kice su shiga daki kai tsaye?"
"Hayaniyar me akeyi ne haka?
Lantana keda su waye?" Binta da subadadin lantana ya farkar da ita ta fada tana leqowa ta tagar uwar dakanta dake cikin tsakar gidan.
Tayi sak ganin Bilki wadda suna hada ido ta tamke fuska tam.
"Kune tafe cikin ranar nan?
Sannunku da zuwa aiko be sanar mun kuna tafe ba ku shigo" ta fada iyakar dauriyarta a qoqarinta na janyo su a jiki da kirki kamar yanda Turai ta bata shawara Bilki kadai ta sani cikinsu ko kuma ta gane tunda tasan Hadiza sedai sanin babu abinda ze kawota gidan yasa bata ma kawo a ranta ta santa ba.
Dankwalinta ta shiga nema dan ta fito falo ta jiyo Bilki na cewa
"Da yake zuwan namu ba naki bane shi yasa be gaya miki ba, bari mu shiga can mun gode da tayi" daga haka suka ja kayansu zuwa dakin Bara'atun.
Bi ta tabi bayansu da harara tareda sakin tsaki kafin ta daure kanta ta fito ranta na suya.
Tsabar isa da samun guri ne yasa zasu kwaso jiki rabe rabe suzo mata gida kuma be gaya mata ba ko kuwa shima besan zasu zo ba sannan wadannan uban kwanukan da suke tafe dasu na menene ko daga Kasuwa suke?
Take tambayar kanta harta fito tsakar gidan Lantana na tsaye guiwa tayi sanyi saboda yanda taji Hajiyar ta musu magana ya nuna mata sudin ba banza bane kamar yanda ta tsammata.
"Ashe baqinki ne Hajiya" ta fada tana sosa kai, Binta ta wuceta tana cewa
"Qannen megidan ne"
Seko ta dafe qirji ta zare ido, amma data tuna suda banza a gun Binta duk daya se ta dan saki ranta sedai mamaki ya kamata da har Binta tayi musu tayin shiga dakinta, to shiri suka fara haka ko kuwa duk cikin wasan kwaiwayon data fara ne?
Binta kitchen din tsakar gidan ta shiga ta tarar da Mairo na kwashe Shinkafar data gama dafawa Miyar na kan wuta tana idasa soyuwa.
"Idan kin gama akai musu abinci kafin nan a hada ruwa da lemo idan da Alkaki ki hada musu" ta bata unarni ita kuma ta amsa da
"Toh Hajiya".
Dakin da suka shigan ta wuce, sun shimfida tabarma cikin kayan da sukazo dasu Mata biyu na zaune Bilki na tsaye taba duban dakin daya qara kyau dalilin sabon fenti da qofofi harda Abun sak kwan lantarki duk aka canza se gurin ya qara haske da kyau.
Daga bakin qofar ta tsaya ta aika musu gaisuwa rai babu dadi kamar an mata dole suka amsa banda Bilki data shige daya daga cikin dakunan gurin, Binta tayi kyacci a ranta tana ayyana yanda zataci kan uwarta kafin ta kalli yar dattijuwar da ta fisu shekaru Qanwar Inna Hajara ce tace
"Bari a kawo musu ruwa, bamu san da zuwanku ba ai da an muku shiri me kyau"
"Ba komai yar nan hakan ma mungode" matar ta fada a ranta tana mamakin rashin kirkin Bintan da ake fada ita dai bata gani ba.
"Munafuka" Bilki ta fada bayan ta juya, matar da ake kira da Inna Habi tace
"Kai Bilkisu, niko banga abinda kuke fada akan matar nan ba.
Yanzu wace macece zata tari dangin kishiya sunzo danki haka?"
Mairo ta aje Try data doro su ruwa da Lemo da kayan tabawa, seda ta zabura jin maganar Inna Habin ta kalli Bilki da tayi wata dariyar mugunta tace
"Karkiyi saurin yanke hukunci Inna ki dai jira kiga qarshen wasa dan in akayi wasa babu tabbacin ki fita da qafafunki daga cikin gidan nan muddin ta gano wacece ke".
Mairo ta hade yawu ta miqe tana gasgata zancen Bilkin tabbas Hajiya bata da wannan baqin Labarin, wato shi Alhaji baya gudun rigima ya ringa zuwa yana daura Aure matarsa bata sani ba dadi daya data ji da taga Alamar Bara'atu ce zata dawo dalilin ganin Hadiza.
A can daki kuwa Binta na zaune kan kujera ta harde qafa Lantana na daga qasa suna magana,
"Ku tabbatar da basu buqaci komai ba komai suke so a musu, so nakeyi idan sun koma dukda nasan waccen shegiyar ba zata taba fadar Alherina ba amma saura da yau suka fara zuwa dole dai suce na musu Kirki" Bintan ta fadawa Lantana ta miqe cikin rawar jiki tana cewa
"An gama Hajiya, kin san dama ni indai Ladabin Kule ne nan na fi kauri laka laka zanwa mutum kamar zan kwanta masa idan ina son abu".
Binta ta bita da kallo tana fassara maganarta a zuciyarta kafin taja tsaki a fili tace
"Kar nake kallonki ai karki dauka wawiyace ni kice zaki shammaceni".
Bajewa su Bilki sukayi suka kwashi Abinci abinsu, Hadiza ta tattaro kwanukan da suka gama dasu ta fito dasu waje gurin wanke wanke ta tarar da Lantana na wanke tukwanen da akayi abincin rana Mairo kuma na qoqarin dora na dare ta aje kwanukan hannunta tana musu sannu suka amsa Lantana ta qureta da ido tana si ta tuna inda ta santa bata tuno dinba Hadizan ta juya ciki.