Sashe 47
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka suka sha tafiyar bata ko kula Audu sedai shine yake tankata lokaci lokaci daya gaji da yanda ta shareshi yayi shiru har sukazo Kano, yana Ajiyeta ya fita itama bata zauna ba jakarta kadai ta shigar daki ta fice gidan Turai.
"Wlh Turai ko a jikinsu, babu fa wanda ya daga maganar Asalin matar daya aura din kamar ma basu fahimta ba haka suka share zancen har a gabansa Dady yana wani jaddadamun duk kudin daya bashi ba Aro bane kyautace kuma ba saboda ni ya masa ba, wlh da na shirya rabuwa dashi amma wannan dalilin yasa na fasa.
Babu yar iskar dazan tafi na barwa gida tazo ta wataya da kudin ubana".
Duk da yanayin jimamin da suke ciki seda Turai tayi dariyar maganar Bintan ta kuwa sake harzuqa tace
"Au ga mahaukaciya ko ina magana dariya ma kike mun"
"Ba haka bane, ke dince da abin dariya waini in tambayeki Binta tsakaninki da Allah Audu kike so ko kuma Dukiyarsa?" Turai ta fada tana kallonta.
Ta zabga tsaki kafin tace
"Duka gaba daya, kinga Audu yayi mun daidai da tsarin Mijin da nake burin na Aura cikas dinsa daya rashin wayewar Boko amma abinda yaja hankalina harna yarda na Aureshi saboda yanda Dady ya ke labarinsa na san gobensa zatayi kyau zeyi Arziqi.
Turai ina son kudi ina so kuma na auri me Kudi, dukda nayi samari masu kudi yayan masu kudi abinda yasa na zabi Audu a cikinsu saboda shi be waye ba, zan iya masa wayo na samu abinda nake da buqata a gurinsa sannan na hana kowa rabar sa ya zamani ni kadai zan moreshi se yayana, ba qaramin takaici naji ba dana samu labarin yana da mata harda yaya kuma tun sannan na daura Aniyar seta fita ta barmun gidan, bayan nayi nasara sannan ga Arziqi nan yana qara habaka se kuma na bari wata tazo ta tayani ci?
Wlh baze yuwu ba dole koda tsiya koda Arziqi matar nan ta koma inda ta fito babu yanda za'ayi na zauna da kishiya a gidan Audu".
"Yanzu dai plan A ya ruguje se mu tafi ga shiri na biyu, kuma ina so ki kwantar da hankalinki qawata shi yaqi akace fan zambo ne, yanda kikayi da Bara'atu haka zakiyi da wannan ma koda ace ta shigo cikin gidan, yanzu abinda zakiyi, lambo lambo zaki masa ki nuna masa kinyi nadamar abinda kikayi ki bashi haquri kisan duk yanda zakiyi yabyarda dake ta haka ne zaki yi komai ba tareda ya zargeki ba, kamar dai lokacin Bara'atu ai kinga kin nuna masa kina sonta harta fita be taba sanin irin gallazawar da kika ringa mata ba" Turai ta fada
"Turai!
Wannan fa ba Bara'atu bace, kefa kika ce mun kilaki ce ta ina zan iya goga kishi da yar Bariki Turai?" Bintan ta fada cikin yanayin dake nuna tabbas ta tsorata da Amaryar da Audun yayiwo mata.
Turai tayi murmushi tace
"Dadi na dake Damusar takardace, ga tsoro ga ban tsoro, yanzu har akawai wata kisisina da matar bariki ta iya waddda mu bamu iyata ba?
Meye a cikin barikin ne da har zata naki tsoro?
Kinga fa yaqin nan dole se kin dage idan ba haka ba kina zaune zata shigo kuma ta kwace Mijin"
"Allah ya rufa asiri, wlh ko zan mutu bazan bari naga wannan rana ba" Binta ta fada tana fashewa da kuka Turai tayi dariya tace
"Bama zaki mutu ba sedai ita me shirin yi mana kutse ta mutu, yanzu dai kamar yanda na gaya miki kije ki lallabashi ku daidaita, da an kwana biyu kic zaki Bechi ki gaishe su a can zaki kwarkwance komai ki gaya musu wacece ita son samu ki fara sanar da Yayansa na Lagos nasan ko beji maganar na qauyen ba shi baze qijin ta tasa ba" da wannan shawara suka rufe ta koma gida ta yi matuqar qoqarin danne zuciya tayi duk abinda Turai tace.
Kuka wiwi ta ringayi tana bashi haquri da rantsuwar ba zata sake ba yanzun ma sharrin shaidan ne tayi iyayinta har seda ya sakko shima ya bata haqurin yanda Al'amuran suka kasance a qaryarsa wai besan za'ayi haka ba.
"Amma banji dadin yanda kika kwanceni a gaban Dady ba, na dauka ko abinda kika fada gaskiya ne ke me rufamun Asirice a ko ina" ya fada in relevant to zancen yawonsa data gayawa Dady.
Kanta na qasa tana share hawayen kissa tace
"Kayi haquri, wlh bansan abinda ya shiga kaina ba kan yafemun Mijina kaji dan Allah"
"Ya wuce, Allah ya yafe mana gaba daya sannan in Allah ya yarda nan da kwana Goma Zata tare, ina so ki lissafa duk abinda kike da buqata da wanda za'ayi amfanin yinin Biki a can Bechi"
Wani abu ya caki ranta amma ta shanye tace
"Shikenan zan lissafa, yaushe zamu tafi Beechin toh?"
Da mamaki ya kalleta jin yau anyi zancen zuwa Bechi salin Alin ba ta fadi mara dadi ba, ransa ya qarayin fari yana qara gasgata da gaske tayi nadama dan haka yace mata se saura kwana uku zasu tafi da anyi yini yau washe gari au dawo gaba daya da Amarya ta amsa da Allah ya nuna mana a Ranta tana ayyana Bura'ubar da zata tafka a Bechi idan sunje.
Haka ko akayi, tana kallo aka ringa fenti aka shigo da sababbin kayan gado da kujeru aka saka a tsohon dakin Bara'atu baqin ciki kamar ya murqusheta ta mutu wato cikin dukiyarsu yayiwa Tsinanniyar Amaryar kayan daki, takaicin kanta ya sake rufeta datayi wautar cewa ya barshi bata buqatar komai duk a salon wanke kanta gurinsa.
Ranar Laraba suka tafi Bechi ita da Direba daya hadata dashi tareda kayayyakin amfanin girkin da ba za'a samu a can ba, Juma'a za'a kai Amarya can ayi yini su Kwana Asabar su juyo.
Wai se ga Binta na bi gida gida daki daki na yan uwan Audu da sunan taje su gaisa abin dariya ita ce har gidansu Bara'atu.
Duk gidan data shiga bata fitowa seta kwance Amaryar Audu ta fada musu tsohuwar kilaki ya auro, Bilki da tun sakin Bara'atu ta fita a sabgar Audu da gidansa farko cin mutunchin Binta taso tayi da ta je mata gida amma zancen data kai mata ya tayar mata da hankali.
Me yake damun Audu?
Wace hau ce ta haushi da ze auri Karuwa?
Hankali tashe ta tafi gida ta samu su Yaya Babba duk sun tattaru dan kowanne na komawa gidansa da yamma ya samu saqon da Binta ta bari shiyasa suna idar da sallar Isha suka tattaro suka taho gidan gaba daya ita ko Binta tana masaukin su da aka qara gyareshi, rabon su duka ya siye banda na Yakubu dan nan yake sauka idan yaje se ya qara fadada nasan yayi dakuna manya da bandaki a ciki.
"Nifa tun ranar da mukaje neman auran kun tuna sanda na fita zagayawa a lokacin naji wasu suna qus qus din wai anya wadannan sun san labarin Yarinyar suka zo nema dansu aure?
Basu dai fadi komai ba amma wannan magana tasu ta jefani a wasi wasi sedai tunda shi ma'auri wakilci kawai ya nadamu shi yasa nayi shiru bance komai ba" Yaya Baba ya fada, Aminu yace
"Haba Yaya, menene amfanin girman idan ba zaka ga abin da ba daidai ba ka gyara mana?
Yanzi da kaji wannan magana ai ko a tsakanin mu seka gaya mana idan yaso mu basu kudin Aure mu tafi ba zamu yarda a daura ba har se an bincika munji dar din maganar halin nata, na tabbatar shima be sani ba yanzu ya za'ayi?"
"Amma ku kuna ganin gaskiya wannan yarinyar ta fada, kun manta sharrin ta kenan?" Hashimu da be manta kitimurmurar Binta ba ya fada.
Bilki tace
"Bana jin qarya ne, tunda ga Yaya Baba ma yace yaji wata magana, yanzun dai mu jirayi Yaya Yakubu ya iso gobe idan Allah ya kaimu in yaso se mu san abinyi kafin Audun ya qaraso shima" inji Bilki, haka taron ya tashi, washe gari ko da Rana Yakubu da Iyalansa suka sauka Bechi.
Binta batayi qasa a guiwa ba ta shige ko gajiya bata barshi ya ware ba yana aje haqarqarinsa a kujera ta zube a gabansa ko kallon inda take Bakaraba batayi ba taja yaranta suka shige daki.
Bilki tayi turus da kayan abinci a hannunta tana kallon Binta dake rusa kuka a gaban Yakubu tana masa bayani se ta fara jin anya maganar nan da gaske ce kuwa kodai wasan kwaikwayonta data saba ne ta hadashi?
"Yanzu saboda Allah ba zaki barshi ya ko huta ba zaki tasashi a gaba da wannan maganar?" Bilki ta fada taba harararta.
"Zauna Bilki" ya bata umarni kafin yaci gaba da cewa
"Menene gaskiyar abinda ta fada?"
"Yaya muma ita tazo mana da maganar, amma Yaya Baba yace..." Ta fada masa abinda Yaya Baba yaji sanda sukaje neman aure.
"Shikenan tashi kije, zamuji ta bakinsa idan ya qaraso"
"Dan girman Allah kar kuce masa ni na gaya muku"
"Dama ba zamu fada ba tashi kije abinki" da haka ta fita rai fes dan koda Yakubu beyi wata magana ba daga fuskarsa ta fahimci ya kadu da maganar.
Tana fita Balaraba ta fito daga daki tace
"Yanzu kun yarda da maganar wannan annamimiyar matar?
Matar data laqawa wata sharrin kisan kai sena Bariki ne ba zata dorawa wata ba?
Koda yake Allah ya kawoshi gara yaji abinda ta hada ko idonsa ze washe ya gane da wadda yake zaune ai".
Yamma Lis Audu ya isa Bechi, seda sukayi sallar Isha kafin Yakubu ya tareshi a wajen dan baya so sauran yan uwan su fara masa magana ta yanda laifin Binta ze fito.
Cikin siyasa da kwarewar aikinsa ya saka masa maganar a baki, yana da labarin yawace yawacen da yakeyi da wannan yayi amfani yace an gaya masa acan ya hadu
da Amaryar tasa.
"Haka ne, amma ban aureta ba seda na maida ita gidansu tayi Istibra'i tukunna" ya bashi amsa kai tsaye.