← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 91

Sashe 52

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mu bamu saba fadace fadace da kuka iya har ana fidda jini ba a gidan nan dan haka ki san a inda kike" daga nan yasa kai ya fita ya barta tsaye kamar ya dasata tana juya kalamansa.

Ita da suwa suka saba fadace fadacen da zubar da jini?

"A bariki mana yake nufi" zuciyarta ta bata amsa, dabas ta zauna dafe da kunci hawaye suka shiga mata tsere, wato abinda yake nufi kenan, a fakaice yana gaya mata cewar nan ba irin gidan daya dakkota bane kenan da suka saba Fada kamar Kaji suna jiwa junansu rauni Yau Audu da kansa yae goranta mata wani al'amari daya shude a rayuwarta kenan.

Wannan abu yasa gaba daya jiki ta yayi sanyi, sararin data samu ta fara baje kolin sharholiyarta duk karsashin ya barta shima kuma be bi takanta ba yana ta tattalin Binta da hannu ya saka a gaba har ya saukar mata da zazzabi me zafin gaske seda ta kwana uku a kwance kullum kuma is Zubaidan ta shiga ta dubata safe da dare idan yana nan zata amsa cikin sakin fuska idan baya nan kuwa har Lantana samun damar yaba mata magana take suce mata mayya wai ta kama mata hannu to kurwarta kur.

Ita Binta ko abinda take mata ma sam be dameta ba irin na Audun, qiri qiri yaba ganin gaskiya amma ya take yabi qarya shin wane irin mutum ne shi haka?

Ya za'ayi rayuwa ta yuwu a haka ace duk abinda aka gayawa mutum walau shine gaskiya walau qaryane se ya hau ya zauna kuma idan ya gano gaskiyar daga baya girkan kai da izza su hana shi karbar kuskurensa ai ko baze furta da baki ya karbi gyara ba se ya nuna hakan a aikace amma shi babu daya daga ciki da yakeyi sedai ya dora fushi wannan ai ba daidai bane.

Data lura da gaske fushi yake da ita kuma bashi da alamar sakkowa dan har ranakun girkinta da suka zagayo bacci ke shigar dashi dakinta safiya nayi ze fice dole ta sauke nata fushin ta sake samunsa ranar ta tattara duk wata wayo da dabarar da take dasu ta wanke kanta a gurinsa ta hanyar karban laifin da bata aikata cikin sani ba ta kuma tabbatar masa da ba za'a sake ba har da kukanta tace kuma ya rakata a gabansa ta baiwa Bintan haquri sukaje ta bata haqurin ganin idonsa yasa Binta tace ta haqura ai ita komai ya dade da wucewa a gurinta daman wannan tasa ya sakko daga fushin da yake suka koma zamansu lafiya abinda yayi mugun batawa Binta rai.

A zaman tsamar da sukayi ba qaramin qara samun kan Audun tayi ba, a wayo da dabara take dada kwarkwarashi shi kuma dake kan keke ne ya hau daram ya zauna.

Shiryawarsu da Zubaidan se ya zama silar warewar nata shirin musamman da taga kamar Zubaidan ta ganota duk irin tuggun data hada mata a gurin Audun ta dena musawa zata amsa laifinta ta durqusa har qasa ta bashi haquri tana hawayen munafunci a cewar Bintan shi kuma me son girma kansa ya sake fasuwa shikenan kome ta shirya ya wargaje.

Tun daga wannan kuma Zubaidan ta hankaltu duk laifin da Binta ta dora mata zata amsa ta bashi haquri tunda ta fahimci abinda yake so kenan babu ruwansa da jin ainihin magana yanda take hakan kuwa da takeyi ya sama musu zaman lafiya se a dade ba'aji kansu ba idan ba kuma Bintan ta shammaceta ta tunzuro shi ta yanda harta gaza kare kanta ba.

A haka aka kwashi watanni biyar da Auro Zubaida a kuma wannan yanayi ta fara laulayi wanda yazo mata da zafin gaske ga Amai ga Zazzabi lalurori dai iri iri ba qaramin Jiki take ji ba, wannan cikin ya sake gigita Binta, wato Zubaida zama tazoyi ma kenan tunda gashi har tayi ciki ita tana me haka ta faru yama za'ayi Mata suyita haihuwa a gidan Audu Bara'atu tayi biyu ita tana da daya kamar rai kuma a auro wata a bayanta tazo ta goga da ita wannan baze yuwu ba ta shiga takalar masifa kala kala fatanta Zubaida ta tanka mata ta samu dalilin lakada mata na jaki ta yanda cikin zebi rariya tun be gama samun gurin zama dakyau ba sedai bata samu hakan ba, Zubaida da ko a baya bata biye mata ba balle yanzun da take ta kanta.

Abin ya hadewa Binta biyu dan Audun shima yanzu duk ya maida hankali kan Zubaidan sosai wannan yasa ta kasa jurewa ta fiddo haukarta fili take baje musu ita watarana ya tanka mata wata rana kuma ya qyaleta a haka abinda ya sassuta lamarin ganewar da tayi itama tana da shigar ciki saboda batan wata da tayi amma tayi shiru bata gayawa Audu ba sannan kuma cikin Zubaida yayi watanni uku a lissafinsu na daga sanda ta fara laulayi kenan ita kuma nata yana wata daya.

Koda Zubaida sukaje Asibiti likita ya tambayeta yaushe rabon da tayi Al'ada ce masa tayi watanni uku, tayi lissafi da watan data fara laulayi dukda maganar gaskiya ba zata iya cewa ga lokacin da tayi al'ada ta qarshe ba tun zuwanta gidan sau daya tayi watanninbaya da suka biyo idan Al'adar tazo kwana daya ne kuma dan kadan ba kamar yanda ta sabayin kwanaki Bakwai ba kuma ba se qarshen wata ba ko yaushe tana iya ganinsa kuma ya dauke har ta fara zaton ko Sanyi ne ya kamata to tunda tasha magani kuma jinin be sake zuwa ba babu dadewa kuma ta fara laulayi.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number
08129249549*
07011401314*
Bayan tabbatar da lafiyarta data abinda take cikinta aka bata sati hudu ta dawo daga Asibiti, kafin zagayowar sati hudun nan tamkar wadda aka bugawa iska cikinta yayi wani girma na ban mamaki.

A watanni ukun da tayi muddin ba wanda ya karanci yanayi na masu ciki ba shine ze iya tantance samuwar cikin a jikinta dan idan ka cire Laulayi babu wata halittarta data canza kota nuna samuwar wani abu tattare da ita.

Cikinta na nan yanda yake be qara tudu ba haka nan batayi qiba ba se gashi a sati hudu cikin ya bude yayi girma haka jikinta da fuskarta duk sun sauya idan ka ganta seka dauka in kun rabu yanzu anjima za'ace maka ta haihu.

Binta bata nan ta tafi Kaduna sanadin jikin Alhaji Zakariyya daya motsa harya kwanta a Asibiti dan haka suka tafi tareda Audu ya kwana biyu ya barota a can kuma zuwan yayi daidai da bikin yaye su Baballiya da akayi dan haka suka hada tafiyar harda Yan Bechi duk sunje sun duba jikin Alhajin kuma a gidansu Bintan aka musu masauki suka kwana biyu suka juyo tare aka baro Binta a can satin ta uku kafin ta dawo Kano.

Ranar da Binta ta dawo ita kuma Zubaida bata nan taje gidansu yini se dare Audu ya dakkota koda suka shigo kuma bata ma san Bintan da dawo ba dan be gaya mata ba se da ya shiga tareda Zakariyya wai yaje mata sallama sannan ta sani ta kuwa cika da mamaki amma batace masa komai se fatan wayewar gari lafiya tayi kwanciyarta ita kadai.

To washe garima bata fita ko tsakar gida ba dan a yanayin da take yanzun tafi ko yaushe buqatar samun hutu da nutsuwar zuciya bata shirya dibar hauragiyar Binta ba dukda tana so taje su gaisa tayi mata yame jiki amma ta bari akan se da dare idan yana zaune seta shiga ko ganinsa ze rage kaifin duk rashin mutunchin data so yi mata.

Hakan kuwa akayi, bayan isha ta shirya taje Audu na zaune yana cin abinci tareda Zakariyya Binta na cikin daki tana buruntu tayi sallama ya amsa yana tsokanarta da cewa
"Uwar biyu kin shigo?" Haka yake ce mata tunda cikin ya fara wannan girma me ban mamaki yace kodai yan biyu ne shi yasa wata hudu cikin ya ninka girmansa se tace masa to qilan tunda ita ba sanin ya cikin yan biyun yake tayi ba.

"Baquwa mukayi?" Binta data fito ta fada tana zama akan kujera idonta akan Zubaidan, Audu ya murmusa yace
"Baki ganeta ba?
Chapter 52 · 0% Book details