← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 91

Sashe 74

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tambayarsa yayi akan me yake faruwa tsakaninsa da Bara'atu ya ringa zana masa maganganu marasa lissafi bare kan gado, a duk abinda ya fada masa babu guri daya dayaji laifin illa tsantsar Zalunci da Azabtarwa da ita suke mata, ya mayar da ita tamkar Baiwar daya siyo da kudi a cikin gidansa shin wai me Bara'atu tayiwa Audu ne a rayuwa dayake daukar fansa akanta yanzu?

"To Audu kasan dai Aure anayinsa ne bisa yarjejeniyar Mutum biyu Mace da Namiji, haka nan idan har ya zama da cutarwa kowanne bangare yana iya neman sauqi ta hanyar rabuwa idan har babu wata hanyar samun daidaito bayan wannan din, ni Ina ganin tunda dai zaman ku ya zamana da cutarwa ku rabu hakan ze fi Alkhairi akan kuci gaba da zama daya yana daukar Alhakin daya" cewar Yakubu.

Audu ya dago a fusace yace
"Wato ce maka tayi kasa na saketa kenan dazun?"
"Haka tace, ta gaya mun ta gaji da cutar da ita da kakeyi kaida matarka dan haka tana neman sauqi ka sawwaqe mata auranka taje tayi rayuwarta ta samu wani can ta Aura wanda ze sota tsakani da Allah ya san darajarta kaje kaci gaba da zama da matarka da kake ganin tafi maka kowa" Yakubun shima ya mayar masa cikin daga murya.

Se Audu ya miqe yana cewa
"Bazan saketan ba, ka gaya mata idan tana da qarfi tazo ta kwaci sakin ko kuma ta saki kanta"
"Ai kuwa idan baka saketa ta Arziqi ba zaka saketa ta tsiya dan wallahi maka ka zanyi a kotu qaryar taurin kai kakeyi Audu zan nuna maka jini daya ne yake gudana a jikinmu yanda kake jin ka gado Taurin kai seda na fara gada kafin ka samu ragowa, karka kawo mun takardar sakinta kafin nan da gobe kaga yanda zamu kwashe dakai" daga haka ya shige ciki ya bar Audu a tsaye yana tsuma, Bara'atu tace ya saketa?

Ita da kanta ko kuwa wannan matar Yakubun ce ta zugata?

Kwanaki uku aka kwashe cikin wani yanayi mara dadi, kwana biyu da Audu yaje gidan Yakubu bayan ya dawo ya samu Bara'atu yayi mata cin mutunchi da tijara ya kuma jaddada mata sedai ta mutu amma baze taba sakinta ba washe gari da safe yana kamfani se ga magatakarda daga Kotun Musulinci an aiko masa da sammaci, ya karba ya duba kiransa akeyi daga kotu matarsa ta shigar dashi qara ya wuto gida Afujajan sedai be tarar da Bara'atu ba tun safe yana fita itama ta fice ta tafi gidan Yakubu tare dashi sukaje Kotun da kanta ta shigar da qarar bayan Yakubu ya sake tambayarta ko zata yi haquri ta bada lokaci su sasanta ta rantse masa akan wallahi ta gama zama da Audu muddin baso suke wata rana a wayi gari zuciyarta ta buga ta mutu ba su qyaleta jin haka yasa yace su tafi Kotun take kuma aka rubuta takadda aka kaiwa Audu.

Ranar Jajiberin sallah Bara'atu ta karbi takardar sakin igiya daya data rage tsakaninta da Audu, a ranar ya kamata suyi zaman kotu, tun Asuba daya dawo ya kulle kansa a daki yaqi fitowa, besan yanayin da yake ciki ba wani irin qunci da zafi zuciyarsa takeyi masa.

Binta da duk abinda akeyi a kunnenta da idonta amma tayi biris tamkar bata san wainar da suke toyawa ba tana tsakar gida tana aikace aikacenta tana waqoqi Musbahu yazo, bayan sun gaisa yake ce mata gurin Baba yazo ta masa magana qarfe Goma ne zaman kotun nan gashi Tara da rabi tayi, dataje ta gaya masa beko waiwayo ba ya miqa mata farar takarda, duk yanda taso ta daure bayan ta karanta abinda yake ciki ta kasa seda ta rangada guda kamar wadda take saka Amarya a lalle.

Tana bawa Musbahu takardar ta hau taka rawa a gabansa se ya rasa abinda zeyi kawai ya tsaya yana kallonta kafin jiki a sanyaye ya juya ya fice daga gidan ya kaiwa Yakubu saqon Audu.

Sanda takardar ta shiga hannun Bara'atu ji tayi kamar an mata bushara da gidan Aljanna, da Ajami ya rubuta dan haka ta gane komai abu daya daya dameta a ciki shine cewar da yayi karta tafi masa da Da ko daya, ta yaya zata barwa Binta yaranta?

Matar data tsaneta kuma zata iyayin komai akanta da yaranta.

"Karki sakawa ranki damuwa akan yara babu abinda ze same su sannan kina nan a matsayinki na mahaifiyarsu babu abinda ze goge hakan komai daren dadewa kuma zasu nemeki.

Ki fuskanci rayuwarki ta gaba, ki tashi kinemi ilimi ki tsaya da qafafunki in sha Allahu ubangiji zeyi miki sakayya a gaba da Mafi Alkhairi kinji" Yakubu ya tausheta.

A ranar suka tafi Bechi gaba daya dan dama can zasuyi sallah.

Shiya kaita har gidansu ya kuma yiwa Inna Hajara bayanin komai, bayan tafiyarsa kuwa wuta ce kadai Inna Hajara bata hura ta jefa Bara'atu a ciki ba, ta kasa hango rayuwar da yarta take ciki da ta sa ta haqura da daular da ita hange, damuwarta kadai mutane zasuyi mata dariya, zasu rasa tallafin da suke samu a gurin Audun tunda ya kwace Yayansa, ita da take saka ran idan Bara'atun ta sauke farali Bana badi kuma a sakata a lissafi shine tayi mata baqin ciki shin Bara'atu wace irin yarinya ce ne?

An gaya mata da akwai Auran da ake jin dadi dari bisa dari ne a ciki?

Wace Macece zata samu Miji kamar Audu daula iya daula tayi wasa da damarta ai se sakarya irin Bara'atun gashi yanzu Auran ya mutu murus babu damar gyarawa.

An cinye watan Shawwal Mahajjata suka fara shirye shiryen tafiya qasa me tsarki, Audu ya rigada ya biyawa Bara'atu, Bilki da Aminu se Balaraba matar Yakubu, a hannun Aminun ya damqa duk wani abu daya kamata na Bara'atun, babu wanda beyi mamaki ba dukda sun san da ita cikin jerin matafiyan amma abinda ya faru yasa suka dauka za'a fasa tafiyar da ita sedai Audun ya basu mamaki.

Lokacin tafiya yayi suka shirya sunyi bankwana da yan uwa da Abokanan Arziqi, dalilin su Bilki da Aminu ya saka Audu yi musu rakiya Iyafot dukda qasan ransa badansu yaje ba, haka nan zuciyarsa ta kasa nutsuwa a kwanakin, kullum ya kwanta se yayi mafarkin Bara'atun haka da rana wuni yake da tunaninta a ransa yana jin kamar ta cancanci ya nemi afuwarta koda har yanzun be yarda da cewar ya cutarda ita ba kamar yanda mutane suke fada amma kuma haka nan zuciyarsa take ingizashi ga neman afuwar da besan ta mecece yake da buqata ba.

A iyafot Mahajjata sun hau layin karban tikitin shiga jirgi, yana daga tsaye can gefe dan ya sake zama baqo a cikin danginsa tun da ya rabu da Bara'atu ya sake rasa karsashin sakewa musamman a gaban Yakubu yanzun ma ganinsa tsaye suna sallama da matarsa yasa duk ya kasa sakewa gashi yana so yayi magana da Bara'atu amma shegiyar zuciyarsa me masa hudubar tsiya tana gaya masa girmansa ze zube idan aka ga ya mata magana a nan gurin.

"Be kamatu na tafi muna riqe da juna a zuciya ba, ina roqon da ka yafe mun idanna maka wani laifi a zaman da mukayi da kai, daga bangarena na yafe maka, iyakar wannan Alkhairin da kayi mun ka zama silar da zan ziyarci ma'aiki ya wanke duk wani laifi naka da yake cikin zuciyata sannan idan ka koma gida ka gayawa Matarka in har taji tsoron Allah ta gaya maka gaskiya ta wankeni daga zargin data saka mutane sukemun na kisan kai na yafe mata idan ba haka ba idan harna mutu ko ita ta rigani mutuwa tabbas shari'armu sedai a qarqareta a gaban Allah dan bazan yafe ba bayan raina a ringa aibata Yayana ana jifansu da abinda ban aikata ba" Bara'atu da be san sanda ta dawo gurin ba ta fada tana kuma gama maganar ta koma cikin Ayari tana daga masa hannu, kamar wanda aka matsawa Remote haka shima ya shiga daga mata hannun, zuciyarsa ta ringa tsinkewa wata faduwar gaba da besan dalilinta ba ta saukar masa haka ya tuqa motarsa ya koma gida yana maimaita zancenta na matarsa ta wanketa daga zargin data dora mata.

A karon farko ya tambayi Binta gaskiyar abinda ya faru?

Ya akayi tasan Bara'atu ce ta kashe mata Da?

Bintan dake cike fam da tafiyar Bara'atun tayi tsaki kawai ta tashi ta bashi guri.

Bara'atun nema take ta zame mata qajaga, ta tunkudeta amma ba zata bar zuciyarta ta huta ba kenan?

Abu daya ke sanyaya mata rai idan ta tuna aure ya qare tsakaninta da Audu duk Bala'i dole su haqura sannan ga Yayanta nan zube a tsakar gida suna watangaririya iya rabata dasu da tayi tasan zuciyarta ta quntata, jira takeyi Tagwayen Zubaida su shekara biyu suma tasa ya karbo su subi sahun yan uwansu domin tasha Alwashin babu wata mace da zata mori Audu bayan ita, yaya dai da suka haifa sun samu sedai su jira idan ya mutu su yafici abinda suka samu amma badai a yanzu da yake raye ba.

An kammala aikin Hajji lafiya Mahajjata nata lissafin kwanakin daya rage musu su dawo gida haka nan yan gida nata shirye shiryen tarbar yan uwansu, kwanaki biyu ya rage Jirgin su Bara'atu ya sauka, a daren ranar da zasu tafi Jidda inda daga can za'a maido su Nigeria suna shirye shirye dan sun gama daure kayansu cikinta ya fara murdawa, kamar wasa tun tana jinsa kadan kadan har ta kai ga ta kasa zama cikin abinda be gaza Minti talatin ba da fara ciwon cikin rai yayi halinsa Bara'atu ta amsa kiran Mahaliccinta.

Mutuwarta ta girgiza yan tawagarsu gaba daya bama su Bilki kadai ba.
Chapter 74 · 0% Book details