Sashe 13
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bilki ta ringa dariya su Bara'atu dai se murmushi da haka suka qarasa dakin Goggo Fadi sun tarar da ita da Aminu wanda tun Asuba daya shigo gidan yana can kome suke tattaunawa se Allah.
Cike da girmamawa suka gaidata ta amsa itama basu jima ba suka basu guri, bayan sun fito Bara'atu ta kalli Balaraba tace
"Muje kiga dakina nima" suka rankaya Bilki ta wuce gurin Inna Hasiya data kirata.
A dakin Balaraba ta ringa santin kayan Bara'atu, hira suka shiga tabawa Bilki ta dawo nan ta tasasu gaba da tsokana suka ringa hira gwanin dadi kafin qawayen Bara'atu suka fara zuwa yan kwadayin ragowar kazar Amarya.
Kazar ta basu Balaraba ma taje ta dakko musu sauran tata dan ita qawayenta tasan yanzu sun kai gida tunda Asubanci me motar da ze mayar dasu yace zasuyi ze wuce Kano dakko kaya.
Wuni guda tsakanin bangaren Balaraba da dakin Bara'atu sukayi shi, Inna Hasiya kuwa bata gaji da hidimta musu ba wanke wanke da shara babu yanda basuyi ta basu ba taqi tace su huta.
Haka aka ci sati Angwaye da Amare na tsinkar furen qauna hankali kwance.
Dukkaninsu sunyi bulbul abinsu kana kallonsu kasan basu da damuwa banda ma matsalar rashin sirri da take hana Audu yanda yaga dama wannan yasa ya quduri a ransa dole idan ya koma Kano kafin ya dawo ya gyara musu bangare a katange kamar na Yakubu dan gaskiya wannan zaman na kwarar sa.
Seda akayi sati hudu da biki kafin hankalinsa ya fara komawa Kano dalilin yan kudaden hannunsa sunyi qasa ga hidimar yauda kullum a wannan rutsin kuma ya sake fahimtar cewar a yanzu ne ma yake da dalilin tashi tsaye ya nemi kudi ka'in da na'in kodan Iyalan da suka fara ajiyewa.
Ya fara shirin tafiya, da daddaren ranar ana saura kwana uku ya koma Kano ya samu Dada da zancen ya kamata Yakubu ya koma yaci gaba da karatunsa.
"Dada yanzun nauyi ya hau kanmu, bazan so mu qare rayuwarmu cikin wahala tamkar ta mahaifinmu da sauran yan uwanmu ba kina kallo dai yanda suke fama basu da wata tartibiyar madogara se Noman da sukeyi.
Karatun Yakubu nada muhimmanci na farko Burinsa ne na biyu kuma idan ya kammala ze samu madafar da ze riqe kansa tunda shi ya gaza maida hankali akan Kasuwanci kamar ni kuma gaskiya bazan zuba ido ina kallo da quruciyarsa aikin wahala ya kashe shi ba dan haka kiyi masa magana ya bar duk wani abu daya dauka yazo mu koma Kano ya zana jarabawa yaci gaba da karatunsa".
Dada tayi shiru tana nazarin maganganun Audu tabbas gaskiya ya fada yanzun nauyi ze qarar musu kuma baze yuwu ace shi kadai zeci gaba da daukar ragamar gidan gaba daya ba.
Ta numfasa tace
"Zanyi masa magana babu damuwa da yardar Allah".
Hakan kuwa akayi Dada tayiwa Yakubu magana take ya nuna rashin Amincewa da maganar a cewarsa idan duk suka tafi Birni waye ze ringa Kula da Dadan da yaran mutane da suka Auro?
Dada tayi dariya tace
"Kai dai kace bazaka iya tafiya kabar matar kaba" Yakubu ya sunkuyar dakai kamar ya nutse dan kunya ya kasa cewa komai se Dada ce taci gaba da cewa
"Kodan saboda su karatun naka nada muhimmanci Yakubu a yanda Audu yayi mun bayani.
Idan ka duba kwanannan nauyi ze qarar mana, badi iyanzu idan muna da rai kun dauki Yayanku akwai buqatu marasa yankewa da zasu qaru kaga dan uwanka yana matuqar qoqarinsa akan mu, idan ka gama Karatun zaka samu madogara tunda ga Fa'izu (yaron me gari da shima ya kaishi Kano yayi karatu) kaga yanzu maganar da akeyi yayi hanyar da Gwamnati zata gina mana Firamare a nan qauyan dole za'a nemi malamai, kaga ko wannan aikin ka samu tunda ance biya akeyi ai an samu madogara seka hada da yar sana'ar da kakeyi Asiri ze rufu kodan saboda dan uwanka ka daure ka cika burinka wanda har ya fika damuwa da hakan".
Haka dai Dada da Audu sukayi nasarar tausarsa ya yarda ze koma Kano ya ci gaba da karatunsa, tafiyar Yakubu data taso ya saka Audu qara kwankin tafiyarsa dan su shirya a tsanake.
Ana saura kwanaki biyu su tafi da daddare Hashimu da yayi balaguro tun daurin auran su Audu da kwana hudu ya dawo gari.
A daren ranar suna zaune a dakin Dada Malam, dan gurin Mairo ne yayi kiransu inji Baba Hashimu.
Audu da Yakubu ne sukaje, yana zaune tareda Goggo Fadi suna hira gabansu Kaza ce gasashshiya suna ci Audu da Yakubun suka samu guri suka zauna suka gaishe su.
Hashimu ya cire tsinken da yake sakace dashi ya kalli Audu yace
"Naji labarin kuna shirin Tafiya Birni shine nace kafin ku wuce ya kamata mu zauna muyi magana, so nake yi ku siyar mun da barin gonarku ya zama mallakina tunda dai ba nomawa kukeyi ba, abincin ma idan an baku saidawa kuke kun koma cin kalar na Birni se shinkafa da Taliya ko?" Ya qarashe cikin sigar tambaya.
https://chat.whatsapp.com/Hi7n2ddpUxZ24e1tJyREqZ
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*HALIN KISHI*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*NAGODE*
*FREE PAGE 6*
Yakubu ya nisa yace
"Ban fahimce ka ba Yaya, kaji labarin muna somu siyar da gonar ne ko yaya?"
"Ko daya, ina dai so ne nasiya kuma a shirye nake ko nawa kukayi mata kudi zan biya" Hashimun ya sake fada, Yakubi ze sake magana Audu ya tareshi yace
"Shikenan zamu siyar, Allahya kaimu safiya se a kira su Malam Audi suyi mata daraja daga nan se muga yanda za'ayi" yana gama fadar haka ya miqe dole Yakubu ya bishi ze fara masifa Audu yayi masa alamar da yayi shiru, daga cikin dakin suka jiyo dariyar Goggo Fadi Hashimu kuma yana cewa
"Sunyi kyan kai dan ko basu siyar munta arziqi ba to zasuyi Asararta a banza"
Wannan magana ta daurewa Yakubu kai ya kasa fassara abinda yake nufi a haka suka koma dakin Dada take Audu ya gaya masa dalilin kiran, Dada tayi shiru kafin tace
"To me kuka ce masa?"
"Nace masa zamu siyar da safe zan nemo au Malam Audi ayi mata kudi"
"Amma meyasa Hashimu duk gonakin da suke garin nan se tamu zece ze siya kuma..."
"Dada, dan Allah kar a tada maganar nan, gona yake so ko za'a siyar masa daga nan a raba kudin kowa ya kama abinda zeyida kasonsa" Audu ya katse Dadan se sannan Yakubu yayi magana yace
"Wannan ma ai maganar banza ce, ta yaya zamu siyar da abinda ita kadai muka mallaka ciki muke ci muke sha?
Kai me yasa baka lissafi ne kawai abinda kwakwalwarka ta gaya maka kakeyi?"
"Kadaiji da kunnenka abinda ya fada shawara ta rage taka ko ka bari a karbi kudin ko kuma ta salwanta a banza kaga munyi asara da hujja" Audun ya fada yana miqewa yayi musu sallama ya fice daga dakin yana tafe yana tuna Gonar Baffaye wani tsohon Abokin Malam ne da gonarsa take gabas da tasu, bara waccen shekaru uku kenan Hashimun ya nemi ya siyar masa dan harkoki suna ta bude masa babu kuma wanda zece ga inda yake samun kudi Baffayen yaqi, daminar Bana yayi shuka lafiya har ta fara yabanya haka kawai aka wayi gari komai ya bushe shekarar haka ta qare ko Kara be cire a gonar zancen da akeyi yanzu gonar ta zama tamkar kufai, aciki ne ma ake zaton Gwamnati zatayi ginin firamaren da za'a bude wadda me gari ya bashi shawarar ya bayar dan abinda za'a biyashi ya nemi wata ko qarama ce ya siya.
A labarin daya ringa kewaya gari ance anga Hashimu yana zagaya gonar da dare bayan sunyi zancen cinikin Baffaye yaqi wanda ba'a kwana biyu ba wannan ibtila'i ya fadawa Baffaye, bawai ya yarda da abinda aka fada ba amma kalaman Hashimun na dazu sun saka qara masa hujja nacewar ze iya yi musu mugunta a kan Gonar.
Ransa fal da baqin cikin hanyar da yan uwan nasu suka dauka bayan gushewar Malam da bashida burin daya wuce ganin sun hada kansu amma abu ya gagara, haka ya kwana da takaicin abin a zuciyarsa washe gari kuwa qarfe goma na safe gaba dayansu suka hallara yan dakin Goggo Fadi dana dakinsu.
An kirawo Dillai a gaban kowa sukayi wa gonar kudi da daraja abinda ya qara qonawa Hashimu rai dan kafin zuwansu seda ya samu daya daga ciki har cin hanci ya bashi akan su kassara farashin gonar, haka ya tishe kudin cas ya basu abinda ya qara bawa kowa mamaki su kam sun rasa a ina Hashimu yake samun kudi haka.
Audu da yan uwansa suka qule a dakin Dada, Yakubu nata fada akan abinda ya faru, Bilki da Aisha ma dai sunbi sahun Audu nayin amanna da siyar da gonar dan har Bilki na cewa daman taji a bakin Mijinta Hashimun na fadar koda tsiya se ya mallakin barin gonarsu ya zama nasa to gara da kayi ta arziqi shikenan.
Audu ya kalli Dada yace
"Yanzu ya za'ayi da kudin nan?"
"Ni a ganina a nemi wata gonar a siya idan yaso ko haya ce a bayar ko kuma a nemi ma'aikata su ringa nomawa ana biyan su lada" Dada ta bada shawararta, Audu yayi shiru kafin ya kalli Yakubu yace
"Kai kuma ya kake gani?"
"Daka zarce hukuncin a siyar da baka shirya abinda za'ayi da kudin ba?" Yakubu ya fada a cikin fada Dada ta daga masa hannu tana cewa
"Bana son haka, karka kuskura ka saka wannan abin a ranka balle har sabano ya shiga tsakaninka da dan uwanka.
Kaifa ka gaya mun abinda kukaji ya fada jiya, kasan hatsabibancin Hashimu, ladan hayar da suke bamu kana kallo lalataccen da kwari suka taba ake tattarowa a bamu duk dan a zauna lafiya yasa ban taba magana ba yanzun daya nuna yana so gara a bashi dan qarshe zamu iya rasata baki daya".