← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 91

Sashe 49

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi qoqarin shiga dakin ta dakatar dasu daga abinda sujeyi amma qofar a kulle dole ta wuce dakinta tana kuka wiwi qarin takaici da baqin cikin yanda Audun ya bude baki yana ihu tamkar farin shigan Hauka yanda kasan yau ya fara sanin Mace, washe gari kuwa taga qarshen bariki dan bata tsammatar Audu ya fita sallar Asuba kuma bataga kyallin idonsa ba se yamma lis shima tareda Amarya suka fito suna raha da dariya hannayensu sarqafe da juna yanayin shigarsu ya nuna mata cewar fita zasuyi.

"Idan na yarda Allah ya tsine mun albarka" ta fada yana miqewa tsaye harda cire dan kwali tayi damara.
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 19*
"Idan na yarda Allah ya tsine mun albarka" ta fada yana miqewa tsaye harda cire dan kwali tayi damara.

Duk su biyu suka dakata suka kalleta, fuskar Zubaidan dauke da murmushi harda rausayar da kai tace
"Ina wuni Yaya Binta?"
"A gidan ubanwa na zama yayarki?

Ni zako gwadawa Karuwanci?

Koda yake na manta sana'arki ce ai ba a qasa kika tsinta ba" Bintan ta fada murya a sama,
"Meye haka ne Binta?

Ke baki iya magana a hankali bane dole se kin daga murya kamar meyi da mutanen sama sannan wannan damarar da kikayi ta mecece haka?" Audu ya fada yana kallonta se kuwa ta shiga qara tamke damararta tana cewa
"Ba shakka dole ka tambayeni me nakeyi haka wato kaima an dora maka darasi irin nasu na tsofaffin kilaki ko?

Saboda tsabagen rashin Adalci tun daren jiya rabona dana sakaka a ido, haka ka kwana kana kurma ihu a gidannan kamar wanda ya samu abinda baze qare ba sannan yau ko kyallin qeyarka ban gani ba se yanzu zaku fito cikin shiri da alama ma waje zakuyi wato ga banza jaka ka ajiye wlh ba zan yarda ba" ta qarasa maganar tana qoqarin fashewa da kukan takaici saboda tuno daren jiya da tayi.

Wani murmushi me tafe da qaramar dariya Audun yayi ya kalli Zubaida data sunkuyar dakai, Karuwa da Binta ta kirata ya soki ranta amma tayi shiru tana qoqarin danne damuwarta tareda hana kanta karaya a gaban Bintan,
"Ashe dagaske kike da kika ce duk maqota suna jina yanzu yaya zan kalli mutanen waje idan na fita bayan na tafka abin kunya qato dani ace yar yarinyar kamar ke ta sakani ihu a daki?

Gaskiya mu koma an fasa fitar nan gara na hada kunyar jiya data yau gaba daya gobe na fita dan bazan fasa ihu ba"
Da Binta ta rasa abin fadi se kawai ta fasa kuka me kama da ihu ta juya ta shige daki, Zubaida kuwa dariya ta fashe da ita tana kare fuska saboda kunyar maganar tasa,
"Mu koma ciki" ya sake fada yana kama hannunta ta zame tace
"Babu ruwana kaje ka rarrashi Yaya Binta kar kasa ta qullaceni"
"Ki barta zan lallasheta gobe dan bazanso abinda ze sosa mun rai ba bare harya hanani ware murya dakyau nayi ihun dadi"
"Allah ya isa tsakani na dake yar iskar Karuwa, idan ma kuma Asiri kikayi kika shigo gidan nan na rantse da Allah sena karyashi zaki gane dani kike zanje" Binta data fito da Hijabi a jirkice ta fada cikin kuka kafin ta fice daga gidan ko ina zata se Allah,
"Ka bita mana kana kallo ta fita" Zubaida ta fada cikin yanayin damuwa, ko a jikin Audu ya juya ciki yana cewa
"Duk inda taje ma zata dawo" daga haka ya jata suka koma ciki fitar da suka niyyata aka fasa.

Binta kuwa bayan fitarta rasa inda zata nufa tayi, Turai bata nan ta tafi Gumel suna Yayarta ta haihu kaf Kano kuma ita kadai ce qawar da take kaiwa kukanta.

Haka nan tasha kwana ta tasamma gidan Lantana wanda tunda ta fara mata aiki shekara uku kenan sau daya ta taba zuwa sanda Salisu Babban dan Lantanar ya rasu se yau data rasa gurin zuwa kawai zuciyarta ta raya mata taje can.

Lantana da makwaftanta biyu na tsakar gida sun baza faifan Binta suna caccaka, haka nan kullum aikinsu kenan yanzu labarin kishiyar da aka mata dake neman zauta ta take basu
"Ai in gaya miki alqadarinta ya karye, badai ta kori ta Allah ba ai gashi nan an hadota da wadda zataci ubanta ta kowanne fanni, kilaki fa akace yo har a gaya mata iya kissa da kisisina" daya saga cikin matan ta fada, Lantana ta buga cinya ta bude baki zata bada sharhi Binta ta doko sallama suka zabura gaba daya daka kallesu kaga marasa gaskiya
"Hajiya, kece?" Lantana ta fada bayab data miqe tana sosa kai kamar me kwarkwata, Bintan ta kallesu irin kallon raini kafin ta nufi wata Farar Kujerar roba dake ajiye a tsakar gidan,
"Allah yasa lafiya dai Hajiya keda kanki kika zo gidan nan idan wani abu ne aida se ki aiko a kirani" Lantanar ta sake fada.

Cikin muryar qunquni ba tareda ta kalleta ba tace
"Lafiya lau, zaman gidan ne ya isheni shine na fito"
"Ai to barka, kuma ke kikace na taho da wuri yau ai da yanzu ina can na tayaki hirar to ina wuni?" Cewar Lantana sauran matan da se sannan suka iya magana duk suka gaisheta.

"Bari naje Lantana inaga su Shamsiyya sun taso daga Allo yanzu, mace daya ta fada se dayar ma ta miqe tana cewa
"Bari na biki ki lallabemun kan nan nawa, Lantana Allah bamu Alkhairi"
"Duk tafiya zakuyi?

To ku gaida gida nagode" Lantana ta fada ta na miqewa ta taka musu.

Binta na zaune tana qarewa tsakar gidan Lantanar kallo yanda kasan wani filin baje koli can kwanukan wanke wanke can kayan yara sun cire sun zubar a qasa harda zannuwanta ga abinci da akaci aka zubar ba'a kwashe ba banda tiqar rake da qutsirarrun Kara gurin murhunta kadai abin kallonne.

"Bari na kawo miki ruwa Hajiya" Lantana ta fada Binta ta kalli Randarta ta kalli Lantanar kafin ta zabga tsaki tace
"Kika ce mun Mijinki yana aikin Malanta ko?

Yana ina?

So nake a karyamun duk asirin da waccen tsinanniyar tayiwa Audu a yau nake so ba se gobe ba ta yanda ze mata korar kare ta tafi gidansu komai dare"
"Tirqashi" Lantana ta fada a zuciyarta a fili kuwa seta gyara zama tace
"To yanzu kin hau saiti kenan Hajiya"
"Da ba a saiti nake ba?

Karki gayamun magana Lantana saboda kinga nazo gidanki, ki kiramun shi ayimun aikin da yake gabana ba surutun banza nazo muyi ba"
"Allah ya baki haquri Hajiya nima ba surutu nake miki ba, amma yanzu dai Malam baya nan ya tafi qauye kuma kwana uku zeyi a can, da ace jiya kikazo da zaki tarar dashi amma da akwai Mijin qawar nan tawa da suka fita yanzu shi yana nan a gida Malam me makarantar Allon nan ta kan kwanar shigowa idan kina so yanzu sena rakaki gurinsa duk abinda Malam zeyi miki shima irinsa yakeyi" Lantana ta fada cikin ladabi.

Binta tayi shiru na wani lokaci, zata so ace a yau din nan an karya mata duk wani Asiri da Zubaida tayiwa Audu amma kuma bata son terere, shima Mijin Lantanar data zo gurinsa saboda tasan zatayi komai cikin sirri ne Lantanar ba zata fitar mata da sirri ba wannan da take fada kuwa bata da tabbas a kansa dan haka ta nisa tace
"Jibi kikace ze dawo ko?"
"In Allah ya yarda Hajiya"
"Shikenan, bari naje na dawo" ta fada tana miqewa tsaye, Lantana taso ta jata da wata maganar ta zauna ko Allah zesa taji yanda ake ciki dan daga ganin idanun Bintan da kuma kawo kanta da tayi gurin Mijinta da tayi mata Qaryar yana aikin Malanta tun farkon fara aikinta a gidan tasan banza bata kao zomo Kasuwa kuma duk abinda ya koro Kifi daga ruwa ya fada wuta toh tabbas yafi wutar zafi, zata so taji komenene dan ta samu na yamadidi a unguwa kamar yanda ta saba raba zancen Bintan lungu da saqo a unguwar amma yanzu babu fuska dole ta haqura ta rakata zaure tana jaddada cewar Jibi da Malam ya dawo zata sanar mata.

"Ko na biki na tayaki zaman ne Hajiya?" Bata dai sare na ta fada, Binta ta mata Banza tayi gaba.

A maimakon ta tafi gida kai tsaye seta bige dabi ta wancan lungun ta bulla wancan seda taji ana kiraye kirayen sallar Magriba kafin ta kama hanyar gidan ranta na quna da tunanin me zataje ta tarar, tana shiga Soro hawaye ya balle mata, wai yau ita Binta ce gidan Audu ya gagareta zama har ta fita tana garari a titi saboda qata Mace?

Wlh bata isa ba, taci alwashin seta tozarta Zubaida, yanda ta kori Bara'atu Salin Alin haka itama zata fita ta bar mata gida, Audu da duk abinda ya mallaka nata ne wata mace bata isa tazo ta mata katsalandan a sabgarta ba.

A tsakar gida sukaci karo ya fito da Alama masallaci zeje,
"Kin dawo?

Ga Alhaji can an maidoshi bakya nan yana gurin Yar Dagwas" Audun ya fada mata kafin ta bashi amsa ya rabeta ya fice daga gidan dan har an tayar da sallah.

Kamar kububuwa ta doshi dakin Zubaidan babu sallama.bare neman iso ta bankada labule ta fada ciki.

"Wane Dan abu ta kazan ne ya baki izinin taba mun yaro?

Dana tsarkakakke zaki shafa masa Dattin zina?

To bari kiji karki dauka kinga gurin zama a gidan nan, yanda kika shigo da qafa biyu idan bakiyi wasa ba sedai a kwasheki a wilbaro dan sena karairayaki na zubar.

Se kinyi nadamar auran mun Miji, sena illataki yanda ko kin koma yawon Karuwancin naki ba zaki samu masu tayawa ba, bani Dana, kuma ki fito ki doramun abincin dare yanzun ba se anjima ma".
Chapter 49 · 0% Book details