Sashe 14
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yakubu be iya cewa komai ba tunda Dada ta goyi bayan Audu, qarshe bisa shawarar Audu da Bilki suka yanke cewar za'a tada gini Jikin katanga a fitar da qofar shago ta waje da kuma ta cikin gidan inda zasu zuba duk wasu abubuwan buqata da suke wahala a Qauyen, mutum daya ne yake shiga Kano yayo sarin kaya shima se yafi wata beje ba dan haka abubuwan buqatu da yawa sedai a haqura ayi amfani da wanda ya samu sannan Bilki tace tana so Audun ya ringa aiko mata da zannuwa da sauran kayan kwalliyar Mata daga Kano tana siyarwa dan shima Mace daya ke wannan sana'ar Asabe Dillaliya, sunyi na'am da shawarar, aka kasafta kudin kowa aka fidda masa rabonsa kafin suka sake hadesu Audu ya adanasu cikin kayan tafiyarsa.
Cikin abinda ya masa saura a hannu ya tafi Kumbotso dan yiwo musu siyayyar abubuwan amfani, dayace Yakubu yazo su tafi qi yayi dan har sannan a qule yake dashi, yasa an siyar da Gona kuma ba'a siyi wata ba an tattare kudi wai za'a juya su.
Se ya liqis ya dawo Bechi niqi niqi da siyayyar da yayiwo, a qofar gidan ya tarar da magina sun jiqa gefe ga bulo da alama gini ake a cikin gidan.
Ne damu dasu ba yayi musu sallama ya shige sedai abinda ya gani ya sakashi dakatawa tareda tsayar da yaran da suka tayashi daukar kaya.
Hashimu na tsaye da Malam Sha'aibu magino suna magana, ga katanga nan da aka fara dorawa daga bakin qofar soron har jikin katangar baya ta gidan da Alama an tasarma raba gidan ne.
Bawai Rabawar ne ya bashi mamaki ba Aa yanda aka tada katangar idan aka gine ze zaman su basu da hanyar shiga bangarensu kenan ko kuwa Katanga zasu ringa tsallakawa oho.
Aminu ya fito daga dakin Goggo Fadi kana ganinsa kasan a fusace yake beko lura da Audu ba ya kalli Hashimu yana cewa
"Tun wuri ka dakatar da wannan ginin wai me yasa duk abinda ze janyo tashin hankali a gidan nan shi kakeyi?
Yanzu ta ina kake so su ringa shiga barayinsu?"
Cikin ko in kula Hashimun yace masa
"Ko su fasa wata qofar ko su siyi fukafukai duk matsalarsu ce gida ne dole a raba kuma a sannu yanda na raba su da gonar shima gidan seya gagre su zama sun barshi".
Zuciyar Audu ta harzuqa amma ya daure bece komai ba ya wuce da qafa ya tunkude bulon da basu gama kamawa ba aiki Yar katangar da ta fara tsayi ta ruguje ya shige abinsa yaran da sukayo masa dako suka bishi, a fusace Hashimu yabi bayansa har qofar dakin Dada seda Audun ya dire kayan hannunsa kafin ya kalli Hashimu dake numfarfashi ze fara bala'i yace
"Idan ka manta bari na tuna maka soron a cikin rabon gadon mu yake, saboda idan muka ja katanga baku da ta inda zaku fasawa Mahaifiyarku qofar fita shiyasa muka barshi amma da tuni na dade da sakawa an toshe qofa mun canza mata fasali" yana gama fadar haka ya shige ciki ya bar Hashimu da yayi shiru yana tunani, tabbas gaskiya Audun ya fada Soron rabonsu ne tsabar shaidan da yake masa kururuwa yasa ya manta ganin yafi kusa da bangarensu idan kuma suka toshe din da gaske basu da kusurwar da zasu bullawa Goggo qofa dan ta bamgarensu sun fisu yawan dakuna haka zakila Kudun su da yamma jingine suke da gidaje babu damar su fasa qofa sabanin su Audu da suke ta gabashin gidan inda fili yafi yawa kuma babu gini jikin katangar ta bangaren.
Cike da borin kunya ya tafi yana cewa
"To se kuzo kuyiwa soron kudi a biyaku dan babu fashi gidan nan se an raba shi".
A cikin daki kuwa Dada ta girgiza kai mamakin lamarin Goggo Fadi da yaranta ya kasa sakinta a kullum sabon abu suke tsiro dashi to wai me yasa tun Malam na raye basu bayyana halinsu a fili ba se yanzu daya kau?
A daren Audu da Yakubu suka tara matansu nan dakin Dada suka qara jan kunnensu tare dukda basu da matsala, lafiya lau suke zaune Dada kuwa a yaya ta daukesu ba surukai ba idan kaga yanda suke gwanin sha'awa.
Kamar yanda suka fara girki daya sukeyi kuma a hakan zasu cigaba, Sadiya yar wajen Bilki zata ringa taya Balaraba kwana, da farko Innar Bara'atu tace zata turo mata qanwarta se daga baya kuma tace Babansu ya hana.
Daga qarshe Abdullahi mutumin Audu dan gurin Aminu aka bata dukda Goggo Fadi da Hashimu basu so ba, da yake shima Aminun tsayayye ne yayi musu fes yace dan sa ne kuma ya bawa Audu halak malak ko bayan ransa yayi Tijara kafin magana ta Mutu Abdullahi ya dawo dakin Bara'atu lokacin shekarunsa hudu a duniya.
Audu da Yakubu sun dawo Kano cike da kewar Matayensu kowanne yana jin jiki haka suka duqufa abinda ya maido su, sunyi register rubuta jarabawar kammala Sakandire da suka ci sa'a daidai lokacin an fara kwana kadan suka rubuta cikin yardar Allah sakamako ya fito dukkaninsu sun samu sakamako me kyau.
Yakubu ne ya tirsasa masa kan cewar seya rubuta dukda yace shi ba karatu ze ci gaba ba amma idan ya ajiye takaddar wata rana zatayi masa Rana.
Kudin da suka zo dashi Audu ya zuba suka fadada kasuwancinsu, yayi sarin kaya masu yawa ya aika dasu Bechi an bude shago wanda dama sun bar alhakin aikin a hannun Mijin Bilki Baballiya ne yake zama kuma ba qaramin ciniki akeyi ba dan kusan komai na buqata an kai harda ma sababbin abubuwa a gurin mutanen qauyen ba'a rufa sati biyu is anyi sabon sari an aika idan suka aiko da cinikin da akayi ta hannun Qanin Hayatu Mijin Bilki da yake jan motar kaya yanzun.
Tareda Yakubu suke fita kasuwa, tuni kuma an tayar da ginin filin da Audu ya siya a nan Goron dutse inda yake zama, filin nada girma babu laifi dan haka aka rabashi biyu shida Yakubu kamar yanda daman ya tsara.
Gini aka tada daki ciki da falo kowanne se safaya guda daya da kuma kitchen da bandaki ginin bulo, idan ka shigo soron gidan daya ne sannan zaka tarar da qofofi guda biyu na shiga kowanne bangare.
Yakubu ya dage akan Audu ya maida hankali gurin gyara nasa bangaren dan shi fa bega abinda ze rabo shi da Bechi ba, koda ya fara Karatu ze ringa tafiya duk hutu irin yanda ya ringayi lokacin yana makarantar kwana dan baze yuwu su tattaro su dawo Kano su bar Dada ita kadai a can ba ko bayan haka sam shi bashida sha'aqar zaman Kano ma baki daya haka dai aka ci gaba da rarrafa rayuwa watansu uku a Kano kafin sukaje ganin Matansu niqi niqi da abin Arziqi dan a watannin ba qaramin Alkhairi aka samu da kudin da aka juya ba ga can Shago da Sana'ar Bilki ma se sambarka.
Sun tarar da matansu da Dadarsu lafiya sumul ga qarin abin farin ciki Balaraba nada shigar ciki, wannan abu yayi wa kowa dadi, satin Audu biyu ya koma ya bar Yakubu dayace seya qara hutawa shi kuwa daya baro dukiya be bar me juya masa ba dole ya koma, kwanansa biyu da komawar shima saqo ya riskeshi wanda yakeyiwa Yakubu cuku cukun samun gurbin karatu ya aiko masa da cewar an samu dan haka Yakubu ya shirya ya tafi Domin har Samista ta fara nisa acan makarantar dole Audu ya juya Bechi.
Dan qaramin yaqi sukayi da Yakubu sanda Audu ya gama wassafa masa abinda yake faruwa.
Ya rasa me zeyi, ashe wai Audu can Jami'ar Ikko ya nemawa Yakubu gurbin karatun Shari'a ta hannun Tsohon Abokinsu na Magashi wato Hayatu duk a tunanin Yakubu anan kwalejin Shari'a da aka bude a Kano ze nemar masa Gurbin ashe shine dalilin daya sa be gaya masa komai ba akan zancen makarantar.
Yakubu yace ba zeje ba, ya za'ayi ma ya tsallake ya tafi har Kudu da sunan karatu?
Idan jami'ar ce baga ta nan a Zari'a ba tunda ta kano basu fara karatun shari'a ba a sannan ko ba wannan bama shi karatun Jami'a ya masa girma a lokacin baze iya ba, seda Dada tayi masa wuji wuji sanna ya haqura.
"Me yasa Yakubu duk qoqarin da dan uwanka yake akanka baka gani ko da yaushe cikin gwasaleshi kakeyi?
So kakeyi kuma ku zama kamar su ace babi jituwa bazaku hada kai da baki shawararku ta zama daya ba?
Idan kuna haka suma qannenku abinda zasu dauka kenan ni kuwa fatana ko bayan raina ace duk abinda zaku zartar a tsakaninku se kun shawarci juna kuma babu babba ko yaro in har daya ya bada shaqara me kyau da zata amfane ku ku karba ku zartar amma gashi kai da kake babba kai ne duk abinda aka kawo se kayi Adawa da hakan bana so bana jin dadi ka dena hakan" Dada ta fada masa.
Yakubu yayi shiru, har ga Allah baya jin dadin yanda Dadan take goyon bayan duk wani hukunci da Audu yake zartarwa dukda dai ba abu mara kyau yakeyi ba amma yin hakan ze saka ya dauka cewar komai yayi daidai ne ba kuma ze ringa duba muraden waninsa ba in har abinda zuciyarsa ta raya masa kawai shine daidai.
A komai na rayuwa shawara nada kyau amma ya za'ayi ya ringa zartar musu da hukunci kamar wasu Yayansa ai ko Baballiya beci ace Audu ya turashi wani gari can karatu ba tareda son ransa ba balle shi da girmansa harda iyali ya ajiye ayi masa wannan abun yanzu haka ze tattara ya tafi ya bar yar mutane har tsayin wane lokaci ze dauka kafin yazo?
Nan da Kano ma suna daukar watanni inaga Ikko da tafiyar kwanaki ce kafin kaje, anan cikin qauyensu da akwai Abokanansu biyu da suka tafi neman Arziqi shekara uku kenan zuwansu daya gida kuma sun basu labarin yanda Kudu take tayaya ma ze iya zama a can fisabilillahi amma ya ya iya?
Yanda ran Dada ya baci yasan ko yayi mata bayani ba lallai ta fuskanta a fuskar salama ba.