Sashe 70
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A kwanaki biyu ba qaramin Ilimi Balarana ta zazzagawa Bara'atu ba da kuma wanda ta gani da idonta ta koyo, sun dawo ta qudiri niyyar tabuka abin kirki a wannan karon itama, zatayi amfani da duk dabarun data koya mata na riqe Miji, zatayi iyakar yinta yanda ba fata takeyi ba koda ace wani abu ya sake faruwa badai a zargeta da sakarci ko rashin sanin ciwon kai ne ya janyo mata ba.
Tafiyarsu Legas ta qara rura wutar bala'i a zuciyar Binta, dukda ya gaya mata kafin su tafi abin ya zafeta matuqa harta kasa jurewa ranar da suka dawo a dakinta ya sauka bata iya shanyewa bata amayar masa da abin da yake cikinta tas akaci sa'a be kulata ba domin shima ya qaro karatun zama da mata, ya san da akwai abubuwan da mace zatayi wanda Kishine yake tunzurasu babu yanda kuma zakayi da ita dole kayi haquri.
Watanni uku da dawowar Bara'atu, a hankali kyakykyawan zaman daya fara ginuwa tsakanin Ma'auratan ya fara samun tazgado, salon da Binta tayi amfani dashi a zamansu na farko da Bara'atu shita sake maidowa na cusguna mata ta hanyar bautar da ita da kuma zaginta tareda muzantata sedai a wannan karon ta canza salo ta kuma biyo ta hanyar da a qaramin wayo da Dabarar Bara'atu ba zata iya kaucewa Kaidinta ba.
Da farko ta dakatar da Lantana da Mairo daga zuwa aikinsu wanda tayiwa Audu qaryar Lantana sata takeyi mata shiyasa ta koreta ita kuma Mairo ta dakatar da ita ne kawai su ringayin girkinsu da kansu be kyautu ace abincin me aiki ze ringa ci ba bayan yana da mata har biyu sauran Ayyukan gidan ma duk bazasu gagaresu,
"Da ze yuwu mu zauna da Maman su Baba mu tsara yanda zamu ringa ayyukanmu kawai ba se wani ya taimaka mana ba.
A gidan Yaya Aminu naga irin tsarin ya burgeni kuma hakan ya qara shaquwa da fahimta a tsakanin matansa kana gani duk gidanku babu Kishiyoyi masu fahimtar Juna kamar matansa haka yayansa kansu a hade baka ma iya banbance wannan na waye to nima irin zaman da nake so mu gina a gidan nan kenan duk abubuwan da suka faru a baya su zama tarihi mu tun kari gaban mu" abinda Bintan ta tsarawa Audu kenan cikin salo na zallar kissa da iya hada tuggu.
Audun yayi na'am da shawararta kuma yaji dadi, tabbas Matan Aminun abin kwatance ne yanda suke zaune tamkar Dadansu da Goggo Fadi kafin rasuwar Malam Tijjani, haka suka tashi gidansu aiki da komai tare su Dadan su keyi kwana a Turakar megida ne kadai ze nuna maka wadda take da Girki a cikinsu shiyasa shawarar tayi masa dadi yasan kuma Bara'atu ma zatayi Na'am da hakan itama.
Sanda ya sanarda Bara'atu hukuncin da Bintan ta yanke na sallamar su Lanatana batace komai ba saboda daman ba ita suke yiwa aiki ba, sharar tsakar gida kadai abinda take mora a aikin nasu tunda ba Girki daya sukeyi ba kamar dai farkon zamansu ne me Miji tayi abinci dashi har gara Mairon tana kama mata wasu abubuwan idan tana girki a Kitchen din tsakar gidan Lantana kuwa kallon Arziqi ma baya hadasu balle aje a ga batun tayata aiki shiyasa sallamar masu aikin bata dameta ba.
Anyi kwana biyu da maganar ya tarasu falonsa domin tsara yanda zasu raba aikin gidan, Binta ce da girki ranar tana ta kai kawon hada musu abinci su duka gaba daya harda yaran dan sun dawo Abdullahi ma anyi hutun makaranta yana komawa gida ya samu labarin Innarsa ta koma Kano kwanansa biyu shima ya hado kayansa ya taho Audu da Binta suka ringa masa tsiya.
Seda aka qare cin abincin suka sallami yaran suka sauka qasa kafin suka nutsu cikin kujera dan yin maganar data tarasu din.
"Dan Allah ya kukaji abincin yau?
Har wani dadi ya qara na daban saboda mun hadu Ahali gaba daya munci tare, gaskiya haka zamu ringayi daga yanzu saboda ni daman a gidanmu mun saba tare muke cin abinci gaba daya kaima ai ka sani" ta yi maganar tana kallon Audu se shima ya murmusa ya mayar mata da cewa
"Kwarai kuwa, ina fatan kuma wannan hadin kan ya dore"
"Nikam daga gurina babu wata matsala ai kamar yanda na gaya maka komai daya faru a baya ya wuce itama ina fatan ya zama haka a gurinta dukda har yanzu dai naga ta kasa sakewa se ta ringa darare jikinta kana kallo fa tunda muka zauna yanzu bayan gaisuwa babu abinda ta qara cewa ta barmu muna ta zuba kamar lalatattun Radiyo" Bintan ta soko Bara'atu wadda kanta ke qasa tana kallon lallen da tayi kwanaki biyu da suka wuce sanda ta karbi girki maganar Bintan kuma bata saka ta dago kota amsata ba saboda ita har yanzun ranta yaqi Aminta da wannan takun na Binta ba kuma taso ta saki jiki da ita ta sake shammatarta irin na wancan karon.
"Nikam matsalata dake kenan Bara'atu kin fiya qauyanci kiyi abu wani salo salo kamar mara jini a jiki tsakanin nida Bintan waye baqonki da ba zaki sake a cikinmu kiyi sabgoginki ba?" Audu ya fada yana gyara zama.
Seta daga kai ta kalle shi, kalmansa sun mata zafi dan har kwalla ce ta tarun mata a ido, bata da dauriyar zuciyar da zata jure cin mutunchi ko tozarci yanzu zata karaya ta fara kuka banda tsabar wukaqanci ita ze kalla yacewa Baqauya to ya suke shida itan? ai babu me gorantawa wani Asali dan tushensu daya koda yake shi daman be iya maganaba.
"Haba kai kuwa ya daga magana kuma zaka fara ce mata yar qauye?
Koda yake kunfi kusa ai, Qauyawa biyu, yan Qauyen Bechi" Bintan ta zage su duk su biyun a wasance garan kuwa se ya hau dariya yana cewa shi ba baqauye bane ai baqauye wanda bashida wayewa kenan shi kuwa da yake fes ko haihuwar Birnin ba zasu gwada masa wayewa ba ai ita kuwa Bara'atu abun ya sake qular da ita amma ta hadiye bata ce komai ba sedai ta quduri niyyar yi masa maganar muddin suka kebe, zata gaya masa bata so, karya sake wulaqantata a gaban Kishiya (as if zata iya).
"Yanzu dai muyi abinda ya taramu dare yanayi" Audun ya dakatar da wasan ganin Bintan na nema ta wuce gona da iri a wasan nata ta fara tabosu tana cewa wai kaf garinsu banda Yakubu waye yayi Karatun zamani dan shi kansa bata yarda yayi sakandiran ba
"Ke kuwa nasan dakyar ma idan kin taba shiga Aji" ta sake takalo Bara'atu wanna yasa ya dakatar da ita danshi basa shiri da raini.
Bintan ce dai tayi magana akan tsarin da take ganin zasuyi, Me girki ita zata dafa abinci wa gida gaba daya, zasu hade girkin kenan sabanin da da kowa takeyin nata sauran Ayyukan gida kuma shara da wanke wanke wadda bata da girki tayi harda sharar dakunan junansu sedai idan da wani uzuri ko lalura to dayar na iya daukewa dayar aikinta tsarin Binta kenan.
Maganar sharar dakunan Junan tayiwa Bara'atu banbarakwai dukda take Baqauyiya mara Ilimin amma tasan ko a karkarar da suka fito Kishiya bata sharewa kishiya daki sedai idan da lalura ina laifin iya tsakar gida?
Tana jira taji Audun yace wani abu akai amma shiru sema jaddada hakan yayi da yace sannan ya juya kanta wai yana tambayarta ya mata ko tana da magana?
Taga to me zata ce musu?
Ta ce be mata ba su samun abun magana daga shi har matar tasa kenan se kawai tayi shiru suka gama abinda zasuyi ta musu sallama ta wuce se bayan data koma dakinta kuma abin yayi ta damunta, Balaraba ta gaya mata karta ringa barin magana a ranta muddin akan abinda ze cutar da itane, koda za'a ce bata kyauta ba gara ta fada a gyara akan ta bar abin a cikinta ta cuci kanta da kanta to amma tana gudun tayi magana kuma su canza mata ma'ana saboda muddin bada zuciya daya Binta tayi wannan abin ba to tarko ta hada mata so take tace wani abu ta ruftata ciki, haka ta kwana tana saqe saqen me zatayi?
Ta yarda da wannnan tsarin ko kuwa dai ta gwada sa'arta gurinnusar dashi rashin dacewar hakan?
Bata son fitina ba kuma tason abinda ze sake janyo mata matsala da Binta ko Audu, a baya shiga dakinta na qasa da Minti biyar ya janyo har aka laqa mata sharrin kisan kai inaga yanzu taje shara?
A bangaren su Audu kuwa Bara'atun Binta ta gyara zama tana tsiyaya masa Zobo a kofi tace
"Se naga kamar Bara'atu bataji dadin maganar da akayi ba"
"Kinsan ta ai ita ba'a fiya gane ina ta dosa ba tunda kikaji bata ce komai ba hakan ya mata itama kenan" ya bata amsa bayan daya kurbi zobo.
Ba haka taso ji ba dan haka ta sake kalailayewa tana cewa
"Uhm haka dai kace amma ni yanayin fuskarta na karanci kwata kwata maganar man bata zauna mata ba, idan lura kuma ai tunda kuka dawo daga Legas din nan tsumewarta tafi tada, kafin ku tafi ai tana dan sakin fuska idan mun zauna irin haka amma yanzu fa sedai tayita sunkuyar da kai tana irga yatsunta kodai har yanzu ta riqe abinda ya faru a baya ne a ranta?"
"To idan maganar abinda ya faru a baya ne ai ke ya kamata ki qullaceta ba ita ba tunda ke akayiwa laifi ko?" Cewar Audu, se tayi narai narai da fuska tace
"Nima dai hala na gani, nida aka cuta na dubi Allahmace na yafe amma kuma tazo tana so tayi zaman gaba dani idan fa ba a gabanka ba ko gaisawa bama yi bana so ina kawo maka maganarta ne kaga kamar wani abun nake so na hada shiyasa amma wlh sam duk yanda nake so na jata mu zauna lafiya taqi sakin jiki kayi mata magana in dai akan abinda ya faru take tunani dataqi sakewa dani wlh na yafe kuma na manta komai ta saki ranta mu zauna lafiya abinmu mu kama ka ram yanda ba zaka sake hango wata ba balle wannan karon ma ka sake kwaso mana Kara da kiyashi".