← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 91

Sashe 34

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nifa wlh Ji nake kamar na rufeki da duka Bara'atu" Balaraba ta fada kafin taci gaba da cewa
"Banda tsabagen abin haushi Bintar me?

Me akayi akayi wata Binta da zaki zauna ta shigo gidanki ta mayar dake yar kallo bayan ke kika ci wuyar Audun kika zauna dashi tun bashi da ko sisi har ya zama mutum ta ganshi ta aura na tabbata wlh a rayuwar da kikayi dashi Binta ko a me wanke mata kaya ba zata dauke shi ba.

Amma shine kika zauna kika barta take zuba miki mulki a gida kin zama yar kallo jibeki dan Allah yanda kika qwanjale kika fita hayyacinki tamkar me wani ciwo ita kuwa tana walwala da farin ciki Miji na hannunta wlh tun wuri idan zaki farka gara, ki amshi Mijinki da matsayinki, ke kika sha wuya dashi dan haka yanzu kamata yayi duk wadda zataji dadinsa to a bayanki take".

"Kema dai kya fada Yaya Balaraba" Aisha ta tsoma musu baki taci gaba da cewa
"Koni da nake zaune a qauye wlh bazanyi sokoncin da Yaya Bara'atu takeyi ba banga wata kishiya da zanji tsoro ba, ba daga Kaduna ba ko daga Ingila ya aurota qarewar Bariki sena gwada mata nawa wayon qauyen dukda shima Yaya Audu da laifinsa ko nace ma yafi kowa laifi.

Wancan zuwan da sukayi da Yaya Ummaru ya masa magana akan abinda tayi lokacin auran Saleh cewa yayi wai ayi haquri shi baya iya mata fada saboda idan ya duba yaga komai ya samu yanzu a rayuwa Ubanta ne sila kuma shi uban a duniya babu abinda yake so kamarta shi yasa yake mata lamuni kiji wani rainin hankali fa se kace wata diyar Qaruna ko kuma yanke Talauchi suka bashi".

Balaraba taja tsaki kamar zata tsinke harshenta kafin tace
"Saboda ubanta ya masa silar arziqi se akace tafi kowacce Mace ko yaya?

Rabonsa ne a jikinsu kuma ko zasu bashi su haukace se yaci kawai tsabar mugun hali ne irin na maza matar da aka sha wuya tare da ita bola wadda zata diro rana daya itace abokiyar cin arziqi kuma wlh Audu ya bani mamaki a irin yanda kowa yasan yana qaunar Bara'atu ban taba tsammanin ko Gimbiya Elizaabeth ya auro ze fifitata akan Bara'atu ba"
"Abin ne nake ga kamar harda Asiri" Aisha ta sake fada Balaraba ta harareta tace
"Aikin kenan kullun ace Asiri, shin maza basa isakanci dole se an musu Asiri da yawa da haka suke fakewa ayita daukar Alhakin matan da basu ji ba basu gani ba ace asirce su sukayi, shidai Audu daman halinsa ne be fito ba se yanzu daman kuma kinsan kudi shi yake nuna ainihin kalar mutum ita kuma Binta tayi amfani da wannan damar take zuba sharafinta tunda shi ya bata qofa.

Ni da Allah tashi kije ki karbo musu idan ba haka ba kuma naje da kaina" ta qarashe tana kallon Bara'atu data sunkuyar da kai idonta ya tara kwalla dalilin maganganun da sukeyi.

Tun jiya Balaraba take mitarzancen nan, babu wanda ze fuskanci halin da take ciki kowa sedai yace mata wawuya ko sakarya ta kasa kwatar yan cin kanta ta sakarwa Kishiya ragamar gidanta daga zuwa to dan Allah base ta samu kwarin guiwa da Adalci daga gurin wanda ya ajiye su ba?

"Bari kiga na tashi" Balaraba ta sake fada tana yunqurawa dakyar saboda tsohon cikin dake jikinta nan Bara'atu ta zabura ta miqe tana cewa
"Bari naje, ni magana ce ban so wlh da kun barni yanzu se a dora musu wani tunda dai ta bamu iya rabon mu" da haka ta fice daga dakin tana jin Balaraban na zaginta.

Yan Bechi na ganinta sukayi mata caa suna cewa
"Yawwa Hajiya Bara'atu, tun dazu muke jira a qaro abincin kinga yara se kukan yunwa suke wasu ko karin safe ba suyi ba muka fito".

Da wani yanayi tace musu
"Kuyi haquri yanzu za'a kawo" ta fice daga falon zuciyarta na bugawa cike da taraddadin abinda ze biyo baya idan taje tace a qara musu abincin, dukda cewar su sukayi wahalar dafashi ita da wasu daga cikin yan uwan Audu da suka fara yowa gaba tun ana jibi suna.

Seda suka dafe shinkafa kwano goma sha biyar, dambu kwano bakwai ga tuwon safe na kwano bakwai amma banda su Waina, Funkaso Alale da sauran tarkacensu irin na yan gayu da suka kai akayo musu daga waje amma a ciki tuwo Malmala goma suka basu se shinkafar da bata fi rabin kula madaidaiciya ba tun hantsi be gama dagawa ba kuma suka kusa cinye shi saboda ba'a karya ba duk suna jiran a kammala abinci sannan ga ma'aikatan da suka tayasu duk a ciki ta debar musu suka tafi dashi gidajensu gaba daya yan uwan Bintan suka lode abincin a Kuloli suka kai daki.

A hankali take gifta matan dake zaune tsakar gidan yan suna, wasu maqwaftansu ne wasu kuma qawayen Binta da matana Abokanan Audu wanda suke hulda da ita kadai duk kuma rukunin data wuce zata musu sannu wasu su amsa wasu suyi mata banza harta dangana da qofar falon Binta,
"Maman Baba" taji an kirata ta waiwaya fuskarta ta fadada da murmushi ganin Maman Kabir ce maqociyarta guda daya da suke sabgar Arziqi gaba daya sauran Binta ta kwace su ko tace sun koma gurin Bintan.

"Se yanzu zaki shigo mana" ta fada tana jan kumatun Kabir dake hannunta ya kuwa janye ya lafewa mamansa tayi dariya tace
"Maquyacin kawai"
"Tun safe naso na leqo baqi nayi wlh se yanzu suka tafi" Maman Kabir din ta fada.

Bara'atu tayi murmushi tace
"Na sani tsokanarki nakeyi dazu Shamsiyya ta shigo ai tace Yayan Baban Kabir ne yazo, qarasa ciki to yanzu zanzo abu zan karbo gurin Binta".

"Ai gara na biki nima naga Jinjiri kafin na zauna" Maman Kabir ta fada hakan yasa suka shiga falon Bintan tare.

Yayyenta na tsaitsaye a falon sun hada kai suna magana sallamar su Bara'atu ta sakasu zabura tamkar marasa gaskiya, Yaya Salima ta qaqalo fara'a ta yabawa fuskarta tana kallon Bara'atu tace
"Aa uwargida an leqo?

Sannunku fa da aiki"
"Uhm" Bara'atun tace kafin kanta a qasa cike da taraddadi tace mata
"Daman yan Bechi da suka zo yanzu ne Abinci be isa ba shine nace ko za'a dan qaro musu"
"Aikin kenan abinci Abinci koda yake ba a saba ci ba, banda jaraba ma suna amma anyo gayya kamar wani Bikin fari wato za'azo aci banza to babu kowa ya nade yunwarsa ya koma da ita" Munira wadda take autarsu Bintan amma ta rigata aure ta fada cikin Fitsara se Yaya Saliman tayi saurin tareta tana cewa
"Haba ke kuwa Munira Abinci dai Allah na tuba abin aci ayi kashi kuma fa mutanen nan dangin me gidan ne idan ba'a basu ba to su za'a bawa?

Barta dan Allah Bara'atu shiga ciki ki gayawa yar uwartaki se muji kamar Adadin da za'a zuba musu" ta qarasa tana nuna mata qofar dakin Bara'atu.

Maman Kabir da takaici ya quleta, ba abin tayi magana ba ta jawa Bara'atun ta juya kawai ta fita tana ce mata
"Bari naje an jima kan na tafi ma gaisa da ita" Bara'atu kuwa a sanyaye ta tura qofar dakin Bintan da sallama wanda tun zuwanta gidan shekara guda sau daya ta taba takashi randa aka kawota, ko ranar da zata haihu a qofar falo suka hadu ta taimaka mata suka tafi Asibiti.

Zuciyarta duk babu dadi ta shiga, ita abincinma ko kalarsa bata dandana a harshenta ba da suka gama girkin shayi ta kada tasha saboda yanda ta gaji sannan duk taron Jama'ar da suke iqirarin sunzo cin banza Jininta biyu ne a ciki Hadiza wadda dama tare suke zama se Ubaida data biyo yan zuwa suna saboda taga Yan uwan nata ragowar dukfa Dangin Audu ne, qanne da yayyensa da Matan yan uwansa se Maman Kabir Qawarta tilo da ta shigo yanzu wadda tana da tabbacin harta fita be zama lalle ko ruwan fanfon gidan tasha ba.

Bata tarar da Binta a dakin ba motsin da taji a Bayi yasa ta ankare da tana ciki, Jinjirin daya ci sunan Babanta Binta Zakariyya na nade cikin showel ta matsa inda yake yanda aka kwantar dashi yayi kusa da bakin gado sosai, dukda cewar jinjirine amma ze iyayin motsi me qarfin da ze fado hakan yasa ta dagashi ta maidashi can tsakiyar gadon yana ta sharar bacci abinsa daidai nan taji muryar Binta akanta tana cewa
"Waye wannan?

Uban me kikeyiwa Dana?"
"Gyara masa kwanciya nayi, naga an barshi a bakin gado" Bara'atun ta fada kanta a qasa.

Binta ta galla mata harara ganin itace kafin tace
"Akan me zaki shigo mun har quryar daki me kike nema?"
"Daman maganar Abinci ce yan Bechi sun qaraso wanda aka bayar kuma ya qare shine nace ko zaki saka a qara musu"
"Babu, gayyar yunwa nace babu abincin ko kuwa ni na ce suzo balle na basu abinci?" Bintan ta fada cike da masifa.

Bara'atu ta kalleta tace
"Yan uwan Yaya Audu ne fa ba wasu daban ba"
"Yana sama ai seki hau ki gaya masa ya sakko ya girka musu suci tunda yan uwansa ne ko kuma ke ki je ki sake dora wani amma ni abinci na ban dafa saboda wasu yan qauye ba na baqin dana gayyato ne dan haka malama maza fitarmun daga daki tun ranki be baci ba"
Kafin Bara'atu ta sake cewa wani abu burum Yaya Salima ta fado dakin kamar wadda ta labe daman tana jiran lokaci yayi ta shiga.

Inda jinjirin yake ta nufa ta dauke shi tana cewa
"Bari a fita dashi mutane nata zuwa ganinsa se kuma ta zare ido ta kalli Binta data cire dankwalin kanta zata canza kaya tace
"Ke zo ki gani wane irin bacci yaron nan yakeyi haka qirjinsa baya dagawa alamar numfashi?"
tana rufe bakinta Babbar Yayarsu Anty Sakina ta shiga dakin ta kallesu sunyi cirko cirko tace
"Lafiya kuwa meya faru?"
Salima ta miqa mata Babyn tana cewa
"Yawwa dubashi kiga Anty se naga kamar baya numfashi" da yake ita malamar jinya ce, nan ta tattaba yaron tayi salati tace
"Wannan ai ya rasu".
Chapter 34 · 0% Book details