← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 91

Sashe 65

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan Inna karki manta har yanzu fa Binta tana cikin gidansa, kina dai ji har ta kori Amaryar da yayi kin kuma ji rade radin da akeyi a gari kan itan ma wata qullalliyar ta qulla mata kenan bata canza zani ba tana nan da halinta babu abinda ya sauya" Bara'atun ta fada a sanyaye cikin karayar zuciya.

Inna Hajara ta galla mata harara tace
"Ai bari kiji, wlh wannan karon kika kuskura kika tsaya tsoron kishiya yayi tasiri a ranki se kinci ubanki.

Ai maciji baya saran mumini a guri daya sau biyu, kin zauna da ita kinsan duk wani salon tuggu da munafuncinta dan haka kema seki shirya irin naki da zaki goga da bata hanyar cuta ko Ha'inci ba.

Sannan da kike cewa saboda yayansa ne koma saboda menene dai abu daya ake fata kuma ya tabbata idan baki koma gidansa ba zaki cigaba da zama hakane babu Aure tunda dai kina kallo cikin Garin nan da kewaye labarinki babu inda be ratsa ba wanene ze Aureki?

Gidan san dai da kika gogo baqin fentin acan zaki koma ki wankeshi karma ki kuskura naji kin tado da wannan maganar balle har dalilin haka yasa ya janye muradinsa idan ma besan gaskiyar ba.

Ko iya komawar da zakiyi ta isa ta karya Alqadarinta saboda ta dauki haqqinki ne saboda tayi silar ki fita daga gidan yanzu kuma Allah ya nufa zaki koma dan haka ma shiri zamu fara, yace da zarar kin amince yana zuwa za'a maida Auranko?

To ki aika a kira Hayatun yau ki sanar masa kin Amince, in sha Allahu bazaki rufa qarshen watan nan cikin gidan nan ba zaki koma dakin Mijinki yan hassada da baqin ciki da masuyi mana dariya sedai su mutu Allah yayi abinda basu isa su hana ba".

Duk yanda taso fahimtar da Inna Hajara buqatar taja lokaci Audu yazo da kansa su tattauna kafin qulluwar kowacce magana qi tayi, daga qarshe ma takans taje ta samu Qanin Babansu ta sanar masa da cewar Mijin Bara'atu yazo biko bata ko tunanin maganar ta rushe tunda dama ba wani ginuwa tayi ba.

Malam Sadi wanda yake cike da wulaqancin da Audu ya musu ya ginawa su Bara'atun sabon gida sannan ya siye gidan da sukaso tozartasu akanshi sedai kuma tsoron Tijarar Audun daya tuna furucinsa na cewar duk seya siye gidajen da suke ciki in suka bata masa rai sanda suka goranta masa cewar meye hadinsa da Bara'atun da har ze siya musu gida? banda Rashin zuciya matar data kashe masa Da ze dawo yana bibiya take ya kora musu gargadi sun kuma san ze aikata domin cefane Bechi yake tayi yana siyan gidaje da filaye tamkar wasu yan tsaki tuna wannan tasa yace babu komai duk sanda suka shirya suzo.

Dataga Bara'atu ba zata nemo Hayatu ba dakanta ta tura aka kira mata shi suka qulla magana ba'aja lokaci ba yayi takakkiya yaje ya sanar da Audu abinda ake ciki.

"Ashe har yanzu Bara'atu tana sona tana kuma muradin zama dani?" Audun ya fada kamar wani soko sanda Hayatu ya gaya masa yanda ake ciki.

Hayatu ya karkace yace
"Bana tsammanin haka, domin munyi magana da ita kuma ban fahimci wata alama taso ko muradi a tattare da ita ba se Damuwar data nuna mun ta son sanin ka yarda da ita ko kuwa har yanzu kana mata kallon Mara Imani Azzaluma?"
"Bana son maido da wannan maganar tunda har wadda ta zalunta ta yafe mata magana ta qare a gurina" ya bawa Hayatu amsa yana wani dauke kai kamar bashi ya gama shauqi yanzun nan ba, Hayatun ya sake cewa
"Kenan har yanzu kana kan bakanka?

Dagaske Zuciyarka ta aminta da cewar Bara'atu ta aikata abinda Binta ta zargeka dashi?" Hayatu ya tambayeshi yana tsareshi da ido, seya miqe tsaye yace
"Ya za'ayi kazo ka tsitsiyeni kamar wani yaronka kana tambayata?

Wannan fa abu ne daya shafeni nida Iyalaina kuma ni nake zaune dasu duk wani wanda ze bayar da shaidar Halin Bara'atu bafa ze kai kamar ni da nayi zaman shekaru sama da biyar da ita ba, ku sanin zahiri kukayi mata ni kuwa na santa har badini dan haka ba ku zaku ringa gayamun abinda zatayi da wanda zatayi ba.

Saqo na baka ka isarmun na gode kwarai kuma zan sallameka yanzu In Allah ya yarda cikin zatin da ze kama nima zan shigo garin" ya qarasa yana laluba Aljihunsa ya zaro Rafar Yan goma na Takadda sababbi qal ya irgi dari biyar ya miqawa Hayatun.

Girgiza kai yayi cikin tsananin takaicin Audu ya miqe shima yace
"Banzo gurinka dan ka bani kudi ba kuma banyi maka abinda nayi shima saboda ka biyani ba nayi ne saboda Allah saboda kuma na daidaita rayuwarka tunda na fuskanci kai baka da alqibla ba kuma kasan ina kakw dosa ba.

Abu daya da zance maka shine in har Allah yasa auranka da Bara'atu ya maidu kayi qoqari ka riqeta da kyau dan wlh muddin ka sake yarda Tuggu da makirci yacika ka rabu da ita se kayi nadamar hakan" yana gama fada masa ya fice daga Ofishinsa ya barshi nantsaye da kudi a hannu dan daman a sabon Kamfanin daya bude ya sameshi.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number
08129249549*
07011401314*
Karo na farko da jikinsa yayi sanyi akan bacin ran daya gani qarara kan fuskar Abokinsa koma yace Amininsa.

Ya mayar da kudin Aljihu yabi bayan Hayatun da har ya fita farfajiyar gurin ya kwala maaa kira.

Dalilin ma'aikata dake kai kawo a gurin ya tsaya, da yawansu duk Yan uwane da qannen Abokanan nasa ya kwaso daga Bechi ya basu aiki se kuma manyan ma'aikata wanda masu kwalayen makaranta ne ya dauka aikin su suke riqe da manyan muqamai a gurin.

"Mu koma ciki muyi magana" ya fada sanda ya cimmasa.

"Tsayuwar da kaga nayi anan ma Albarkacin wadan nan yaran kaci bazanso su gane cewar kowa kana da Baraka dashi ba" Hayatu ya bashi amsa.

Audu ya bata fuska yace
"Wai wane irin abu ne wannan?

Ni wai a wane kalar mutum kuka daukeni da duk abinda nayi kuskurene kowa ganin baikena yakeyi?"
"Ni kuma tsanina da kai ai magana ta qare Alhaji Audu, kayi haquri ma da katsalandan din da na maka bakina da bashida linzami ne ya kasa yin shiru, bari naje kaga Rana da daga zan iya rasa motar komawa gida" Hayatu ya fada daga nan yasa kai ya tafi ya bar Audu a tsaye a gurin.

Jiki babu kwari ya koma Ofis ya zauna ya shiga Auna zamansa da Bara'atu da halayenta tareda na Bintan kamar yanda Hayatun ya shawarceshi.

Magana ta gaskiya ba tun yanzu ba yayi tunanin abubuwa da yawa da suka faru lokacin zaman Bintan da Bara'atu wanda ya fahimce su dalilin Auran Zubaida.

Ya gasgata cewar A bayan idonsa Binta tana cusgunawa Bara'atu tayi amfani da yarintarta da wautarsa tayi wasa da hankalinsa abinda yasa ya fahimci hakan kuwa yanda ta kasa danne Kishinta akan Zubaida kuma har a gabansa bayyanawa takeyi shi kansa dalilin Auran Zubaidan ya fahimci halayenta da yawa da bata bayyana masa su ba a baya se yanzun kuma yaji rashin jin dadin yiwa Bara'atu uzuri a wancan lokacin har ya tsaya ya fahimci gaskiyar abinda yake faruwa ko ya bincika amma maganar mutuwar Zakariyya itace abinda ya gagara tsayar da matsaya akanta.

Magana ta Allah shida kansa ya zargi kansa daga baya da yanke danyan hukunci.

Ya tuhumi kansa akan kasa bawa Bara'atun kariya koya shaideta saboda ai rainonsa ce, shine mutum na farko daya kamata ya gasgata duk abinda akace tayi ya san kuma tabbas bata da muguwar zuciyar da zata aikata kisan kai amma yanda Al'amura suka kasance a lokacin da yanayin zamansu hade da tasirin maganganun Binta ne suka juyar masa da hankali be kuma tashin gano hakan ba se bayan faruwar al'amarin daya wakana tsakaninsa da Zubaida inda qiri qiri Bintan tayi amfani da Duhun kansa ta ingizashi ruwa wannan ce tasa harya fara tunanin anya kuwa Lamarin Bara'atu ma babu lauje cikin Nadi kuwa?

To amma kuma seya tuna Idan sharri Binta tayi mata Ya Za'ayi yan uwanta harda Yaya Sakina su goya mata baya?

Gaskiya baya tsammatar ace gaba dayansu sun hada baki akan al'amari irin wannan tilas da akwai qamshin gaskiya a cikin maganar koda ba duka ba.
Chapter 65 · 0% Book details