← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 91

Sashe 72

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Audu ya gyara zama yana kallonsu duka yace
"Na gayawa Binta saqonki sedai bataji dadin abinda kika fada ba kuma kamar yanda ta fada abinda kika bullo dashi so kikeyi ki ruguza mana zaman lafiyar da muka fara samu a gidan nan dan haka ni a matsayina na wanda ya ajiye ku duka zan yanke hukunci, kamar yanda muka tattauna jiya magana tana nan zaku ringa ayyukanku kan yanda muka tsara babu wani ja inja ba kuma nason na sakejin wata magana daga kowanne bangare".

Abin be wani bawa Bara'atu mamaki ba domin tasan za'a rina wai an saci zanin Mahaukaciya wannan ba sabon abu bane a gurinta kuma yanzu ta tabbatar da zarginta na cewar Binta na nan kan halinta babu abinda ya canza kuma nemanta takeyi da sharri shiyasa ta kawo wannan tsari to amma ba zata zauna ta zama sakarya ba a wannan karon ma, dole ta fadi ra'ayinta koda kuwa Audun zeyi masifa bazata yarda taci gaba da zama yar amshin shata a gidan ba.

Ta kalli Binta dake murmushi tana lada qafa kafin ta fara magana ba tareda ta kalle shi ba tace
"A gaskiya kayi haquri nidai na yafe sharar dakina zan ringayin abata da kaina kuma ina roqar Alfarmar itama ka daukemun ta dakinta, na yarda ta canza mun da wani abun daban da zan ringayi mata amma banda sharar daki"
"Yanzu Bara'atu har kinyi kaurin wuyan da zan fadi magana ki musamun ni zan zartar da hukunci a gidana kice ba haka za'ayi ba?" Audu ya fada a fusace cikin tsawa yana kallonta, bata son fada sannan ya za'ayi a tauyeta kuma tayi magana ya nuna ta masa rashin kunya dan ta nemi haqqinta wannan ya karya mata zuciya Kwalla ta taran mata a ido amma ta kasa magana dan tana bufe baki tasan kuka zata saki, Binta da taji kamar ta taka rawar murna ce ta katseshi da cewa
"Haba Yallabai, haba ranka ya dade Allah ya huci zuciyarka ungo karbi ruwa kasha" ta miqa masa ruwa be karba se huci yake yana hura hanci ta sake marairaicewa tana cewa
"Haba mana Sadauki ni banga abin bacin rai a maganar nan ba kowaccen mu fa tana da damar da zata fadi ra'ayinta shiyasa tun jiya naso ta bude baki ta fadi abinda yake ranta take yanke da bamu zo yanzu ana bacin rai ba amma dukda haka daman maganar nan nina kawota tunda kuma a maimakon samun daidaito tana nema ta haddasa fitina na janye, zan saka a nemo mun wata me aikin kawai taci gaba da taimaka mun itama idan tana so a samo mata in kuma bata so taci gaba da aikinta yanda ta saba shi kenan magana ta wuce kowa yayi haquri".

"Bata isa ba wlh ita tayi kadan ta kawo mun tsarin da zanbi a cikin gidana yanda na tsara haka za'ayi" ya sake fada a zabure, Bara'atu ta kalleshi, yanda yake magana tamkar shiya kawo dokar tun Asali kamar ba Shirin Bintan bane ita ta kawo nata tsarin ya hau ya zauna ita kuma da bada sadaki ya aurota ba saboda ana so ayi mata rashin Adalci taqi shine yake wannan kumfar bakin.

"To bari na nemi alfarma, tunda tace abar mata sharar dakinta zatayi ni kuma nawa na canza mata da wani aikin ka barmu mu sasanta a tsakaninmu mana" Binta ta sake fada kamar da gaske sasancin take so ayi.

Yayi shiru kamar baze tanka mata ba kafin kuma murya a dake kamar ta Boss yace
"Ina jinki".

"Yauwa Nawan, yau akwai tukuici na daban ladan wannan Alfarmar daka mun" seta juya kan Bara'atu tace
Bara'atu da taja Hijabi ta rufe fuska dan ta kasa riqe kukan daya zo mata qasa qasa takeyinsa tana share hawaye wato dai ranakun baqin cikinta basu qare a gidan Audu ba, maidota yayi ya qara sauke mata buhun hunan rashin mutunchin da be ida sauke mata a baya ba, da sauri ta dago kai jin abinda Bintan take cewa
"Kin ga ya dage dole mubi tsarin da aka kawo da farko amma tunda kin nemi a canza, idan kin yarda ni a bangarena a maimakon sharar dakina zaki ringa yimun Wankin kayan Yara ke ma seki fadi abinda zan ringayi miki a madadin taki sharar" ta qarasa tana doka murmushi kamar wawiya.

Kasa cewa komai tayi, ta kalli Bintan kafin ta kalli Audu tana jiran taji abinda zece se ji tayi yana cewa
"Babu maganan ta zabi abinda zaki mata, sharar dakinta ita tace ta yafe kar kiyi na dakinki kuma wannan da ba zatayi ba kika musanya mata" ya juya kan Bara'atu da tayi fakare tana sauraronsu yace
"Zaki ringayi mata wankin kayan yaran duk ranar da baki da girki, My decision is final" aka jefo turanci daga nan ya shige daki ya barsu zaune.

"Yanzu wasan ya fara yarinya" Binta ta fito mata a sak ta fada kafin ta miqe tana juya Mazaune tabi bayan Audu tana wata shaidaniyar dariya irin ta wanda ya nisa cikin lamarin duniya.
https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 28*
Kwana tayi tana juyi duk motsi abinda ya faru daren jiyan seya fadomata zuciyarta tayi mata nauyi, idanunta banda radadi babu abinda sukeyi dalilin kukan data sha, Ta rasa a wanne matsayi zata ajiye Audu dan bata ta Binta kwata kwata ta gama sallama mata amma shi Audu fa?

Son zuciya ko kuwa qin gaskiya ne yake saka shi aikata abubuwan da yakeyi ko yaya?

Me yasa duk hukuncinsa yake kasancewa na son zuciya kuma bisa goyon bayan rashin gaskiya?.

Rashin baccin da batayi ba cikin dare yasa ta makara, dakyar ta iya tashi tayi sallah kanta na bala'in sara mata ta koma ta sake kwanciya tana jin yaran na qu qunin Yunwa dan Zakariyya harya fara kuka gashi bata jiyo motsin Bintan ba alamarbata sakko ba balle ta dora abin kari, Audun m yau be leqa su da Asuba yaga ko sun tashi ba kamar yanda ya saba haka daya dawo wucewarsa daki yayi tunda fushi yake da ita kuma yau din Lahadi ce baya fita da wuri daman se qarfe sha biyun rana shiyasa Bintan ta qara samun damar tsula tsiyarta.

Abdullahi ta kira tace ya share tsakar gida ya wanke saboda hadari ya taso daren jiya ruwa be sauka ba se Iska ta taho da qura ita kuma ta daure ta hada ruwan wanka ta yiwa yaran kafin Hajiyar gidan ta gama qailularta ta basu abin kari.

Tana cikin shiryasu ta jiyo hayagagar Binta ta san baze wuce da Abdullahi take ba.

Cikin kayan Babannan ta samarwa Zakariyya wanda suka masa tace su zauna nan bari ta kawo musu abin karyawa ta zura Hijabinta tana qoqarinfita ta jiyo sallamar Bintan a qofar dakinta, tayi A'uziyya a zuciyarta domin Binta ta zarce shaidan kaidi, sanin Audu na gida kuma zata yuwu wani bala'in ta sake zuwa ta hada mata dan haka tayi saurin fita kafin ita ta shigo mata cikin dakin.

Faran faran tamkar babu wani mugun abu a ranta ta gaida Bara'atun ita dai daga lafiya ta gagara qara ce mata komai saboda zuciyarta gaba daya ma tsinkewa takeyi, ita dai kaf a karkararsu bata taba ji ko ganin Mace irin Binta ba, to ko daman wannan abin shine wayewar da ake fada?

Idan kuwa hakane ta godewa Allah da ta kasance bagidajiya akan ta zamo daga cikin munafukai.

"Kuyi haquri na barku da yunwa ko?

Bacci ne ya kwace mun yau, Bari in maza ko ruwan shayi ne a tafasa se a soya wainar qwai tunda muna da burodi" Binta ta fada tana murmushi.

Cikin sanyi Bara'atu tace
"Babu komai ai" ta bata amsa a sanyaye daga nan Bintan ta juya tana murmushin da Allah kadai yasan ma'anarsa.

Kusan Minti goma tsakani Binta ta sake dawowa da qaton Fulas din ruwan zafi tun wanda Dada ta bata ne lokacin Amarcin da ake zuba musu ruwan zafi a ciki.

Yana da girma ga riqe zafi shiyasa take jin dadinsa sosai.

"Sannu da aiki" ta fada sanda ta kabi Fulas din, Binta tayi murmushi ta koma kitchen ta sake kawo mata Farantin data Zubo faya fayen wainar qwai.

A babban Jug din da take hada musu shayi gaba daya ta zuba Madara da Milo da Sukari kadan kafinta tsiyaya Ruwan zafinta motsa, ta zubanata a kofi ta zubawa Abdullahi se ta qara ruwan sanyi akan sauran ta dan qara musu Madara da Milo sannan ta zubawa sauran Yaran.

Yanda suka rarumi Kofunan duk sunbata tausayi musamman Zakariyya da yake qaraminsu a ranta tace
"Wato muguntar harda dan cikinta takeyiwa" tana kallo ya kafa kai yana kurbar shayin a yunwace Babannan yace
"Umma Burodi da kwai"
"Yanzu zan baka ai uban gajen haquri" ta fada tana tura masa farantin data saka masa Burodinsa da kwan akai sauran ma duk ta miqa musu nasu.

Abdullahi yakai kofi bakinsa ya kurbi shayi ba zato Bara'atu taji ya fesoshi da qarfi harya batata, a zafafe ta buga masa tsawa tana cewa
"Wane irin wulaqanci ne haka ai kasan shayin da zafi zaka kurba ya qonaka ji yanda ka batani duk ka tsalla mana yawu acikin abinci"
Abdullahim dake karkada harshe yawu na dilala dakyar yace mata
"Umma ba zafi bane, gishirine a ciki kamar ze tsinke mun harshe"
"Gishiri?" Ta fada cikin mamaki, Babangida daya matse fuska yace
"Nima da akwai a cikin nawa Umma".

Robar da sukari yake ciki ta janyo dan ta tantance ko kuskure tayi gurin daukowa sedau sukari ne a ciki, se kuma ta saka cokali ta dibi shayin gabanta dan kadan ta kai baki ai da sauri itama ta fesoshi jin wani azababben gishiri tamkar an jiqe kwano gida ciki ruwan fulas din to meya kawo gishiri ciki?

Kofunan hannun Babannan da Zakariyya wanda qiris ya rage ya shanye nasa ta kwace da alama shi be gane banbancin dandanon gishirin bama.
Chapter 72 · 0% Book details