← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 91

Sashe 62

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Binta ta hura hanci tace
"Ai ba se kin fada ba, haihuwa dai an haifesu amma naci alwashin muddin ina raye yaya nane zasu zama kan gaba a komai na dukiyar Audu, baze tuna yana da wasu yaya ba bayan nawa, duk wanda yaci Arziqin Audu to ni naso"
"Ina yinki qawata fada da cikawa wannan aikinki ne" Turai ta fada tana bata hannu suka tafa.

Haka suka yita qulle qulle da shiri na yanda za'ayi yanzu da nan gaba.

A haka har lokacin haihuwar tata yazo bayan anyi suna da kwanaki Turai taje ta sameta da zancen rashin zuwan yan Bechi.

"Ni se nake gani ko dai babu dadi yaci ace kina sabga dasu, saboda dangin Miji ba qananan Munafukai bane, kinga idan suka kafawa mutum qahon zuqa Allah ne kadai ze kubutar dasu.

Kina kallo dai yanda nake zaune da nawa duk sharrin mutum be isa yace na masa mugun abu a fili ba kuma na sani sun sani basa qaunata nima bana qaunarsu amma tunda ban bada qofar da zasu wulaqantani ba kinga qalau muke zaune dan haka kema dole ki gyarota dasu, ki jasu a jiki musamman ma naki da suke Fuqara'u Ahalin tsiya.

Kamar kajine kina watsa musu tsaba na tabbata zasu biki ko wannan ma ze qara miki fada idan kika kame yan uwansa kinga koda ace kin samu tangarda dashi ba fata ba yan uwansa zasu zame miki makamin da zaki gyara komai" cewar Turai.

Binta ta numfasa tace
"Turai baki san yan uwan Audu ba musamman yan dakinsu.

Yanda yake da wannan kafaffiyar zuciyarfa iwa ta mutanen farko haka suke.

Bana tsammatar kudi ze saka su soni kina kallo ko shi din da yake musu shine jigon komai nasu akan Wannan shegiyar Bara'atun duk suka masa tawaye, yanzu an kuma na biyu sun nuna sunfi qaunar Karuwa akaina shiyasa duk suka qi zuwar mun Barka amma ai na samu labarin su sukazo suka kaikayan suna suna gidansu Zubaidan.

Tsinanniyar Bilkin nan tun ranar sunan Dady na farko bata qara tako qafarta gidan nan ba gara Aishar tazo jinya kwanaki can Mazan kuwa tunda suka zo fadar Baqin labarin Auran Karuwa basu dawo ba hatta Baballiya tunda aka Auro ni sau daya ya tako qafarsa gidan nan sedai fa idan naje can Kaduna na ganshi ya samu guri ya baje kamar gidan ubansa yanzu nan Yakubu ne kadai yake zuwa idan cin mutuncibsa ya tashi kuma daman duk ciki Audun ma shi yake shakka shi kadai ne yake tsayawa ya gaya masa magana son ransa kuma ya shanye baze iya mayar masa ba a yanda ya tsaneni kuwa ko duniya da abin cikinta zan bashi baze qaunaceni ba haka Annamimiyar matarsa ni ko kamanninta bazan iya tunawa bama yanzu.

Kai na tsani Yakubun nan iyajar raina wlh" ta qarasa tana cizon yatsa tsanar da tace tanawa Yakubu ta nuna qarara akan fuskarta.

"Dukda haka dai ance se an tsaga ake ganin jini, daurewa zakiyi ki cusa kanki cikinsu ko basa qaunarki ta hakane fa zaki ringa sanin wasu abubuwa da suka shafi shi kansa Audun, hatta da dukiyar tasa kince duk abinda ya samu acan yake narkata, filaye gonaki duk ya tattara acan to idan kika qwafe a nan kin bar musu komai can ta yaya zaki san me kuke dashi?

Irin hakane kina zaune kina lissafin dokin Rano se anzo ranar kasafi kiji abinda ba haka ba ita Bara'atun da take cikinsu tsaya mata zasuyi taja rabo me tsoka ga wannan itama tunda sun nuna tafi musu ke duk mara musu baya zasuyi a barki da lissafi.

Amma idan kika shige su ta yanda ba za'a layance miki komai ba kin sani shima kuma ki matseshi ta yanda duk abinda yayi ko zeyi seya gaya miki"
"Yana ma gayamun in dai ya siyi abu ze fada mun tunda wannan matsiyaciyar ta fita ne dai kinga yanda abubuwan suka koma"
"Se haquri ki kuma cigaba da lallabawa daman ai ba kullum ake kwana a gado ba dole wata rana a samu yanda ake so wata rana kuma aka sin haka sannan ba yanzu muke dubawa ba gaba zamu gina lokacin Jin dadib ai be ma zoba tukunna qawata kedai Allah yayi mana tsahon rai musha shagali" Inji Turai.

Binta ta murmusa tace
"Ai ni dole ma nayi tsahon rai dan munyi Gadonsa"
"Ke karkiyiwa Allah gatsali wlh yanzun kijiki a rami" Turai ta fada tana zare ido, Binta ta rufe baki tace
"Uffararan Allah na tuba ba haka zance ba, dangin mu dai sunyi Gadon tsahon rai kinga nima zanyi" ta sake sakin wani shirmen Turai ta miqe tana cewa
"Bari kiga nayi nan iskancina be kai shiga hurumin Allah ba, to mutuwa dai ba ruwanta da gadon tsayi
n rai ko gajartarsa in lokaci yayi dole a tafi" da haka hirar ta watse saboda Binta tace kan me kuma ana hirar arziqi zata sako musu zacen mutuwa.

Bayan ta yada wanka ta cewa Audu zataje Bechi ta kwana biyu, wannan yasa ya sassauto daga daure dauren fuskar da yake fama dashi tun rabuwarsa da Zubaida.

Ya shirya mata tafiyar Ado sabon Direban daya dauka yake jigila dashi ne ya kaita Bechin niqi niqi da kayan tsarabar data loda dan Hajji Kam taje tayo tsince tsincen su Zam Zam, Dabino Bagaruwa su kallo kallo na yara da sauran tarkacen tsaraba ta tafi.

Kadaran kadahan suka karbeta musamman da basu san da zuwanta ba dan haka babu wani tanadi da akayi mata ta bude dakinta ta shiga a ranta tana tsine musu babu wanda ya bita ko suce zasu tayata kimtsa guri sun dai karbi Naziru yana can hannun Sauda Amaryar Aminu.

Ta gama kakkabe dakin ta kimtsa abinda zata kimtsa kafin ta bude jakar tsaraba ta shiga kasawa gida gida.

Yara ne sukayita shelar zuwanta garin, Aisha ta biya gidan Bilki akan tazo suje yiwa matar Yayan nasu Barka da zuwa amma tace babu inda zataje.

Haka ta tafi ita kadai ta tarar da Yaya Mairo da Yaya Amina da matan Yayyensu duk sunzo Goggo Fadi ta aika an gayo musu.

Kamar yanda Turai ta fada kuwa duk wadda ta shigo fuska a murtuke dan ba a son ransu suka zo din ba dan dai bazasu tsallake kiran Sirikarsu bane amma data miqa musu qullin tsaraba se kaga sun hau washe baki suna godiya daga nan se a shantake a fara hira kuma wannan tasa Aisha ta tarar da dakin cike da Mata suka gaisa ta karbi yaron da daman shine maqasudin zuwanta bawai ganin Bintan ba tana tambayarta Yayansa tace mata Yana Kaduna tunda suka zo suna suka tafi dashi.

Bata jima ba tayi musu sallama tace se gobe zata dawo.

Bayan Isha Jamila Uwargidan Hashimu ta sake dawowa da Langa tuwo da miya data sakowa Binta abincin dare.

Tana daki bayan ta lallaba Naziru yayi bacci, qullin uban Nama ne a gabanta da damammiyar fura take ci Baballiya ne ya kawo mata bada jimawa ba tayi mamakin ganinsa a Bechi wato ya zo Kano amma koya leqa can gidansu da tayi masa tsiya yace mata ai yaje Kanon amma a Kamfani suka hadu da Yaya Audu dake ba jimawa zeyi ba anyi posting nasa can qasar Kudu yazo yiwa yan gida sallama ne shiyasa be shiga can gidan sun gaisa ba ya ajiye mata saqon ya wuce ta bishi da kallo tana mamakin girman da yayi, idan ba'ayi wasa ba zefi Audu tsaho da qirar qarfi yanzun.

"Sangangan kenan sudai sunyo gadon girmaz wai yanzu haka nawa Yayan zasu tashi kenan kamar dakarun yaqi?

Allah yasa dai su kwaso hankalin wancan me baqar zuciyar Wan uban nasu dan ta nan ya banbanta da sauran" ita kadai take sambatu tana danna lomar Nama abinta Jamilan tayi sallama.

Tsaki taja qasa qasa kafin ta amsa, babu damar ta boye abinda take ci dan ta rigada ta shigo dan haka ta hade fuska dan ba zata sammata ba.

"Aa, Hajiya irin wannan rabasha haka kice gashin Haladu aka kawo miki" Jamila ta fada tana kallon ledar kamar ta dumbula hannu yawunta ya tsinke dan qamshin naman ua cika dakin duka.

Yaqe kawai Binta tayi ba tareda tace komai ba a ranta tana mamakin meya maido matar nan kuma?

Yan cikin gidan ma sun barta ta huta kuma se ita zata kwaso jiki tazo ta isheta a daren nan daga zangar ta dan basu fuska dazu.

"Daman Tuwo na kawo miki, yo ahe ke tuni kin makari da babban yanka" Ta sake fada tana bude Langar tuwo da miyar data jere a qasa.

Warin daddawa da kuka suka daki Binta a ranta ta danna Ashar tace
"Ni zanci wannan baqin tuwon da miya kamar yawun Kaza?"
"Zabuwa Babansu yace a yanka a zuba miki a miyar" Jamilar ta sake fada tana karkato mata da kwanon miyar dan taga Namomin da suke ciki wanda qarya takeyi ba Hashimu ne ya bada ba satar mata Zabo tayi tasa aka yanka tasan kuma da zarar labari ya isa kunnensa gobe akwai bala'i dan da tace masa Bintan tazo ma seda ya kora mata ashar yace ina ruwansa da wata Binta.

"Allah sarki aiko nagode, bari na ajiye da safe se a dumamamun nayi kari dashi"
"Aiko daman yafi dadin ci dumamen" Jamila ta sake fada tana gyara zama.

Hira ta shiga sokowa Binta kamo nan kamo can, da taga bata da niyyar tashi dole ta bude naman ta mata bismilla aiko ta dirar masa seka rantse bata ci a gida bayan iyakar qoqari Mazajensu sunayi da wuya ayi miya lami a gida.

Seda suka tada naman tas wanda Jamila ce ta cinye Rabi Binta ta janye Furarta gefe dan wannan kam ba zata bata ba.

"Uhm bari na tashi dare ya fara nisawa, nace da safe in Allah ya kaimu nazo na rakaki ki gano gidan ummarsu Babangida ko?" Jamila ta fada yana miqewa tsaye da shirin tafiya.
Chapter 62 · 0% Book details