← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 91

Sashe 38

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bashir ya ringa dariyar iskanci yana cewa
"A sannu dai duk zasu hau saiti, wato ina gaya muku dadin duniya a sha ruwa ga mata, kai Allah ka yafe mana kurakurenmu".

Haka har suka iso Kano.

Ba'a rufa sati ba ya kama hanyar Zariya ba tareda ya sanarwa da Abokanansa ba saboda yanda tunanin Zuby ya addabeshi, yaje gidan da suka ajiyeta wanda se sannan ya gane nan ma gidanmata masu zaman kansu ne, ya rasa ta inda ze fara nemanta.

Har gurin Magajiyar gidan aka kaishi tace babu Zubaida a gidan haka ya haqura ya dawo Kano da qunar zuciya sedai duk yanda yayi akan ya yakiceta ya haqura da tunaninta abin yaci tura.

Gaba daya ya shiga damuwa ya zaman har walwalarsa ta ragu.

Da Binta ta matsa masa da tambaya se ya ce mata Asara yayi, aiko ta si ta fishi shiga tashin hankali ma dan Binta na son kudi, dukiyar Audu kuwa jinta take kamar tsokar jikinta a kullum zancenta Duk abinda yake dashi nata ne tunda itace sila shiyasa take baqin ciki idan yayi Alkhairi wa wasu, ta bangarenta kuwa duk abinda take dashi ko take samu babu me ci, hatta a karan kanta mugunta takeyiwa kanta dan da wani ya mori abu tareda ita gara ta haqura da abun itama.

Wata biyu Audu ya kwashe yana dakon soyayyar Zuby, dayaga abin baze fita daga ransa ba tilas ya samu Bashir ya roqeshi akan ya nemo masa ita.

"Wlh sonta nake Bashir kuma da Aure" ya fadawa Bashir din.

"Amma dai Audu baka da hankali, to ai koni da nake cikakken dan Bariki iyakata da Karuwa na biya buqata ta mu rabu a gurin duk matan da suke yawo a garin nan ka rasa wa zuciyarka zata so se Karuwa?

Hauka kake ko shaye shaye ka fara?" Bashir ya fada cikin madaukakin mamaki.

"Nidai idan zaka nemo mun ita kawai ka nemota Malam babu ruwanka ko Magajiya ce a hakan naji na gani kuma ina sonta in har ta amince kuma auranta zanyi" Audu ya bashi amsa cikin tsare gida.

Bashir ya kunna sigarinsa yana zuga yace
"Babu shakka Haqqin Bara'atu ya fara dabaibayeka tun ba aje ko ina ba, ka saki yar gidan mutunchi me Cikakken Asali zaka maye gurbinta da Karuwa to Allah ya kyauta ka shirya gobe muje Zariyan, da kace musu Yar Dagwas da tuni an nemo maka ita sedai kuma idan suna ta canza a can dan halin matan Bariki ne basa amfani da sunansu na Ainihi.
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 16*
Kamar yanda Bashir ya fada suna isa suka tambayi yar dagwas se gasu a dakinta aka rakasu.

Zubaidan na kwance kamar mara lafiya suka shiga, ta ringa kallonsu da mamaki dan bata gane Audu bama Bashir dai data fi waya shi ta gane.

"Lafiya?

Tara ko bashi?" Ta fada cikin tsiwarsu irin ta yan Bariki bayan data miqe tsaye.

Audu dai se binta yake da kallo Bashir yace
"Ai kya bamu gurin zama musha ruwa tukunna yar dagwas", tayi gatsine kafin ta dauki wani siririn mayafi ta yafa a kanta da babu dankwali ta fita tana tafiya a hankali.

"Duk yanda akayi dan Hau ta hadu dashi ya lakada mata na jaki shiyasa ka ganta haka" Bashir ya radawa Audu.

Wani duumm yaji a zuciyarsa, shikam So be kyauta masa ba ya rasa macen da ze zargo masa se yar bariki wadda jikinta bashida shamaki da Maza.

Zuby ta dawo da kwalabe uku a hannunta, biyu na Giya is Coca cola daya ta ajiye a gabansu.

"Ga naka nan wadannan nawa ne" Bashir ya fada yana tura masa Coke din.

Seda ya zuqe kwalba guda kafin ya kalli Zubaida dake zaune daga gefe ta jingina tana kada qafa yace
"Tafiyar ta Aboki na ce, kwanaki ma yazo yayi ta bulayi ni ban ma san ya akayi yasan sunanki Zubaida ba yazo haka ya koma ba tareda ya sameki ba, bari na baku guri na dan nemi inda zan rage lokaci" ya fada yana miqewa da dayar kwalbar a hannunsa.

"Kaga jashi ku tafi ni ba lafiya ta isheni ba kuma ko qalau nake kasan tsadata ba haka nan ake fado mun ba kamar wata mara Aji" ta dakatar da Bashir din, se yayi murmushi yace
"Al'amarin da yake tafe dashi yafi wannan kedai ki saurareshi kawai" daga haka ya fita ya barsu.

Audu ya muskuta yana kallonta soyayyarta na qara huda zuciyarsa yace
"Bakida lafiya ne"
"Matsala aka samu nayi ciki, uban yace ze karba kuma naga kar daga baya yazo ya mun Akuya na zubar" ta fada masa kai tsaye kamar wadda ta aikata abin kirki, is ya kasa cewa komai ya zuba mata ido kawai zuciyarsa na bugawa.

Ina jinka fadi abinda ya kawoka dan kwanciya nake so nayi" ta sake fada tana gyara zama, zaman shima ya gyara ya fuskanceta dakyau kafin ya shiga zayyano mata abinda yake cikin zuciyarsa dan ya gaza dannewa,
"Kuma ni da Aure nake sonki, ina so ki bar wannan rayuwar ki koma gida gaban iyayenki wannan rayuwar bata dace da Mace kamarki ba, ki je kiyi Istibra'i zan aureki".

A duk maganganunsa fadar ta koma gida gaban iyayenta ne ya jefata a wani hali ya tado mata da tsohon mikin dake zuciyarta nan da nana hawaye suka wanke mata fuska.

Kewar gidan da Mahaifanta ya taso mata se gani yayi ta hade kai da guiwa tana kuka wiwi.

Hankalinsa ya tashi da kukan da take ya kuma shiga mamakin me ya sakata kuka, shidai ba wa'azi yayi mata ba balle ace tsoron Allah ne ya ratsata kawai ya gaya mata yana sonta ne ze Aureta amma take wannan kukan kamar wadda zata mutu take.

"Ki dena kuka dan Allah" ya fada cikin rabewar murya.

"Ka tashi ka fita" ta bashi amsa cikin bada umarni.

Ya tsaya amma tsaqar data buga masa tasa dole ya fita cike da mamakinta ya zauna a qofar dakin.

Zubaida kuwa tana kuka ta koma tunanin Baya, gida take tunuwa da mahaifiyarta tareda sauran yan uwanta da kuma dalilin daya fito da ita.

Duk ranar da aka ambaci Iyaye ko Gida se tayi irin kukan nan, tana so ta sake ganin nata amma bata da hali.

Kalaman Mahaifinta suka dawo mata sanda yake korarta daga gida.

"Ki tafi, idan kika sake waiwayarmu Allah ya isa iyakar abin kunyar da kika jamun ya isa ki tafi duk inda zakije Zubaida na yafeki daga cikin Yayana".

Cikin dare ya koreta, ba tareda yayi tunanin ina zataje ba wane hannu zata fada kuma ya gaya mata karta kuskura taje gurin danginsa kona mahaifiyarsu.

Hatta da yan unguwa da suka tausaya mata suka so bata mafaka Tijara yayi musu yace ze hada duk wanda ya shigar masa hurumin gida da hukuma haka ya koreta se tasha taje ta samu mafaka duk akan dalilin Qaddarar data fada mata wadda shine sila.

A dalilin kasa sauke nauyinsu da Allah ya dora masa na ciyarwa da sauran buqatu ya tilasta mahaifiyarta fara dora mata tallan shinkafa da wake tana kaiwa Bakin Kasuwa kuma a nan ne qaddara ta hauta wani Azzalumi yayi mata wayo yayi mata fyade, shekararta goma a sannan, ya gana mata Azabar data fitar da ita daga hayyacinta qarshe ta farka ta ganta a gidansu Kwance ga Mahaifiyarta na Kuka Mahaifinta kuma na Sababi kamar zeyi Aman wuta.

Yana ganin kuma ta farka be duba komai ba yace ta tashi ta fitar masa daga gida, a fadar sa daman an sha gaya masa ana ganinta a shagunan Maza, ko a sannan din be yarda Fyade akayi mata ba, a yanda wanda suka tsinto ta suka gaya masa wai ciki ta zubar, wanda ya bata maganin ya gudu se ita suka tsinto cikin Jini a wani kango.

Babu dogon tunani babu komai Mahaifinta ya yanke wannan danyan hukunci na korarta a cikin dare.

Beyi tsinkayen cewa a sannan ko Al'ada bata fara ba ballantana ace ta dauki ciki, yayi mata korar kare cikin rashin Imani, Mahaifiyarta da qannenta naji suna gani tabar gidan shekaru goma kenan kuma kamar yanda ya fada bata sake koda taka qafarta a qasar Kano ba da Asuba tabi wata mata Mai siyar da Abinci a tasha daman ta santa idan ta kawo tallah tana gaisheta matar tasan abinda ya faru da Zubaidan dan haka data ganta cikin daren bata tambayi ba'asi ba kawai ta dauketa ta kaita dan dakinta na langa langa dake cikin Tashar.

A nan ta gyarata tayi mata wanka ta kuma bata Abinci washe gari da Asuba suka hau mota suka bar Kano dan dama taga matar ta hada kayanta tsaf da alama zatayi Balaguro, bata tsinci kanta a ko ina ba se a Kwantagora, da fari Abinci suke siyarwa da giya a nan gidan daga matar ta ingizata zuwa ga wannan rayuwar da take nadama da dana sanin shigarta.

Takanyi kuka tace me yasa bata tsaya ba Babanta ya halakata tunda yace idan bata fita ba seya kasheta?

Data sani ta zauna ya kashe ta ta mutu tun sannan qila da tana Aljanna abinta da wannan qazamar rayuwar data jefa kanta a ciki.

Audu na qofar dakin yana jiyo kukan ta daga ciki, kasa daurewa yayi ya koma ya tsaya akanta yana ganin yanda take kuka har jikinta na jijjiga.

"Dan girman Allah kiyi shiru, idanhar maganar so ko aure danayi miki ce ta sakaki wannan kukan na janye na haqura ke dena Kukan haka" ya fada cikin sigar lallashi.

Bata bari ba, haka ya kai tsugunne ya ringa lallashinta da kalamai masu kwantar da hankali.

Shida kansa yayi mamakin inda ya iyasu, be haqura ba har seda ta dena kukan tana ajiyar rai da jan majina.

"Kiyi tunani akan maganata" ya sake fada mata ba tareda ya sare ba.
Chapter 38 · 0% Book details