← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 91

Sashe 20

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace masa ya shirya kayansa kala hudu zuwa biyar a jaka ya kuma hada takaddunsa, Bara'atu ta ringa musu dariya tana cewa
"Dukda dai bamyi karatu ba amma nasan ba haka taka ake kai mutum makaranta ba dole se anbi matakai ka nemi gurbi idan ka samu kafin ka tafi ko?"
"To ai nima ba cewa nayi zan kaishi kaitsaye ba, zuwa zamuyi can muji yanda tsarin komai yake saboda ban gsu da bayanan Labahani ba besan takan komai ba kawai shirme yake gayamun gara muje kinga idan abin babu wahala kinga ba se anyi jeka ka dawo bazan baro shi can kawai" Audu ya bata amsa.

A daren tana hada masa nasa kayan Babannan dake wasa ya zubo da wata jaka da Audu ya cukuikuye takaddar kammala sakandirensa ya jefa a ciki da takaddun gonakin da suka siya a Bechi, ta tattare ta mayar tana masa fadan ya fiya qiriniya, Babangida ne ya daga wani qaramin kati ta bata ankare dashi ta mayar ba ya fita dashi.

Audu na qofar dakin inda ta baza musu tabarma saboda zafi suna Hira dasu Baballiya da murna tasa ya kasa bacci.

Abdullahi Babangidan ya kaiwa katin hannunsa, ya haska da yar fitila yana karanta abinda aka rubuta a jiki kafinya miqawa Audu yana cewa
"Baba ga abinka Baba ne ya dauko"
Audu ya karbi katin ya haska shi tunaniya tafiyi na menene, duk sonya tuna kuma ya kasa, Kaduna daya gani a Address din dake jiki ya sakashi bawa Abdullahin yace ya miqawa Ummansu ta saka masa cikin jakar da ze tafi dashi, komana wanene yana da yaqinin zeyi masa amfani tunda zashi Kaduna.
* MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na *GHT wato good health treatments
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri *
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number
08129249549*
07011401314*
*Seda suka hau mota har sun wuce Zariya kafin katin ya fado masa take kuma ya tuna inda ya samo shi, wannan Alhajin daya taba taimaka ya basu Mai shekaru kusan uku kenan nasa ne.

Farin ciki ya kamashi, a ransa ya ringa Addu'a Allah yasa yana raye kuma yana Kadunan idan sunje ze neme shi su sada zumunchi.

Ikon Allah kenan, qila rabon su sake haduwa yasa Babangida binciko katin dan ko da kudi bazece ga a inda ya ajiyeshi ba, zaton sa ma ya fadi tun a ranar.

Haka suka sauka Kaduna, Baballiya nata dan banzan raki wai tafiyar Nisa ya gaji Audu ya balbaleshi da masifa yana cewa a haka zeje aikin sojan qato dashi amma se ragonci kamar Mace.

Ganin yana nema yayi masa kuka ya sakashi neman gurin me abinci a cikin tasha ya siya masa, suna zaune yana tunanin ta ina zasu fara, gashi la'asar harta kawo kai dan motar da suka hawo se a hankali kamar sun hau Jaki.

Wani akwatun waya ya hango wanda ake biya ayi kira ya miqe yana laluba Aljihunsa inda ya saka katin Alhaji Zakariyya ya tafi gurin.

Ya bada lambar aka kira masa, kiran farko ba'a daga ba seda akayi na biyu muryar mace cikin harshen turanci ta ratsa kunnensa.

Gyara nasa harshen yayi suka gaisa kafin ya shiga tambayar mamallakin lambar wanda a katin yaga an rubuta Zakariyya, "wa za'a ce masa?" Ta tambayeshi yace mata
"Kice masa Audu Bechi ne" Audu ya fada duda yasan babu tabbacin Alhajin ya gane tunda ba gaya masa sunansa yayi a wancan lokacin ba idanma ya tuna ya taba haduwa da shi kenan.

Matar tayi shiru kamar me tunani kafin tace ya riqe waya tana zuwa.

A can bangaren sakatariyar Alhaji Zakariyya ce ta dauki wayar wadda take a cikin ainihin office dinsa, ta sani lamba ce da yake magana da mutane masu muhimmanci dan haka duk wanda ya kira tabbas yana da muhimmanci gurin Ogan nata.

Kwankwa qofa tayi, Alhaji Zakariyya ya bata damar shiga.

A taqaice ta sanar masa da kiran daya shigo din, sunan Bechi data fada kawai ya sakashi zabura kamar wanda akace anga Dan uwansa daya bata.

Fuskarsa a washe har haqoransa sun bayyana cikin son tabbatarwa yake tambayarta
"Kikace BECHI"
"Yes sir, haka yace sunansa Audu Bechi" ta bashi amsa.

Alhaji Zakariyya ya daga kan wayar dake ajiye kan teburinsa wadda take a hade da ta teburin sakatariyar, Audu nacan saqale da waya a kunne cikin jiran tsammani yaji sallamar Alhajin kamar daga sama har wata Ajiyar zuciya ya sauke ya shiga gaishe shi.

"Har na fitar da rai da zaka kirani, kullum da tunaninka nake kwana nake tashi, na kasa manta Alkhairin dakayi mun" Alhajin ya fada cikin tsananin murna.

Audu yayi murmushi yace
"Haba dai Alhaji dan wannan abin ka kasa mantawa tsayin shekaru?"
"Kai kake kallonsa a qanqanin abu, badan Allah ya kawo ka ka taimakemu ba a wannan rana bansan ya zamuyi ba.

Ya bayan saduwa ya Kano?

Kasan tun wannan ranar ban sake zuwa Kano ba amma duk idan naji wani zece sena bada sallahun a dubamun kai a wannan hanyar gashi bansan sunanka ba ballantana ko yan karkararku a tambaya" Alhaji ya sake fada.

Audu ya jinjina kai cike da mamaki kafin yace
"Ikon Allah, nima yau Allah ya kawoni Kaduna shiyasa na taho da katin nan nace idan baka mantani ba na kiraka muyi zumunchi"
"Kace kana Kaduna?" Alhaji ya fada har yana miqewa, Audu ya nanata masa kafin ya fada masa yana Tashar Kawo tareda qaninsa, Alhaji be bashi damar sanar masa da abinda ya kawo su ba yace ya tambayi me wayar Adireshin gurin da suke ya kuma jira a nan ze tiro direba yanzu a kaisu masauki ai baqonsa ne shi.

Haka ya zauna a gurin, ba'ayi ci mintina ashirin ba sega Direban Alhaji da sukaje Kano tare Audu na ganinsa ya gane shi ya qarasa gurin fuskarsa dauke da fara'a.

"My brother" ya fada yana buga kafadar Audu ko ba'a fada ba cike yake da farin cikin ganinsa.

Shi ya daukar musu jakar kayansu suka tafi inda ya faka wata luntsumemiyar mota yayin waccen shekarar suka shiga Baballiya se zare ido yake.

Suka ringa ratsa titunan Kaduna da gine gine masu kyau da burgewa a nan kuma Audu ya tabbatar da cigaban da Kaduna tafi Kano ta bangaren tsarin birni wanda ake fada su zauna kasuwa suyita tafka musu yau gashi ya gani kuma ya yarda.

Gine ginensu a tsare ga Titi ko ina Malam Baballiya ko kasa rufe baki yayi dan wasu ginin ma be taba ganin kalarsu ba saboda ko a Kanon daga makaranta se gida se ranakun hutu da Audu kan tafi Kasuwa tare dasu babu inda ya sani shiyasa Aljannar duniyar da yake gani yanzu ta mugun tafiya da tunaninsa.

A unguwar Sarki inda katafaren gidan Alhaji Zakariyya yake kutsa cikin wani gida.

Gini ne na Alfarma wanda ko a yanzu kwaskwarima kadan za'ayi masa ya tafi daidai da zamani.

Gurin da aka tanada dan ajiye motoci Direbam da yanzu Audu yasan sunansa Tunde ya faka motar.

Seda ya dallewa Baballiya qeya kafin ya dauke idonsa daga kallon taswirar gidan tamkar kwayoyin idonsa zasu zazzago.

Tunde ne yayi musu jagora har zuwa can gefen gidan inda sukaga qofofi guda hudu jere ya bude ta farko ya shiga suka take masa Baya Baballiya ne kan gaba Audu na daga baya saboda ya tsammaci bangaren matan gidan aka kawo su dukda sunbaro wancan qaton ginin me Bene qila na megida ne can amma ga mamakinsa cikin madaidaicin Falo yaga sun shiga.

Tunde na murmushi ya nuna masa qofa dake cikin falon yace
"Ga daki nan, ku shiga kuyi uzurin da zakuyi bari a kawo Abinci" daga haka ya juya ya fita.

Audu ya ringa kallon Falon dake malale da Kafet irin wanda daka taka qafarka zata lume a ciki ga wasu shimfida shimfidan kujeru na Alfarma, ya taba ganinsu sau daya a gidan wani Hamshaqi a Kano daya kaiwa Takalma wanda suma yana siyar dasu yanzu.

Wani qamshi da sanyi ya ringa ratsasu, ya kalli Baballiya dake nan kamar gaula har digar da yawu yake tsabar kallo kafin ya zauna akan kujera kamar me tsoron ace ya tashi.

Babu dadewa Tunde ya dawo da wani mutum a bayansa ya saka Apron da hular girki hannunsa dauke da wani qaton Try har mamaki ya kama Audu na tunanin yanda ya iya daukar wannan Try da hannayensa biyu ba taredaya nemi taimako ba.
Chapter 20 · 0% Book details