← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 91

Sashe 76

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Allah ya jiqan Bara'atu kawai ni daman tun tuni ai nace na yafe mata idanma wannan kake tunani" ta bashi amsa ba tareda ta kalli idonsa ba babu tsammani kuwa taji saukar yatsunsa a kuncinta irin marin nan na bazata seda ta wantsala gefe tana zare ido kafin ta taqarqare ta fasa qara tana kiran
"Ka mareni"
"Na marekin, kuma dukan tsiya zanyi miki yanzu muddin baki bani amsar abinda na tambayeki ba sa'innan na koraki gidanku" ya fada yana miqewa tsaye PPP ll ya razana Bintar bata taba ganin ya birkice haka ba, Bay's play llp ta fara ja ganin yana neme neme da alama abinda ze doketa dashi din yake nema hakan yasa tace
"Zan fada maka wlh, nidai na shiga bandaki ina fitowa kawai na tarar da ita ta zauna akan Jaririn"
"Har yanzu kina da bakin yimun qarya ko?" Ya fada yana nufota da wayar Radion daya zare, ta yunqura zata gudu Hijabin jikinta ya tadeta ji kake timm ta fadi a qasa be ko bata damar biqin radadin faduwar ba ya shiga zabga mata Bulaliya ta ko ina a jikinta.

Dukanta yake kamar ya samu qato dan uwansa yana fadin "ba zaki fadamun gaskiya bako?"
Dadai ta tabbatar da gaskiyarta ce zata kwaceta a hannunsa dole ta fada,
"Wlh sune, basu fadamun daman ya mutu tuntuni ba se bayan da aka gama mana shari'a wlh ba laifi na bane kayi haquri ka kyaleni".

Be barta ba seda hannayensa suka gaji zuwa sannan ko motsin kirki bata iyayi ya mata lilis fatar jikinta duk ta fashe nan ya watsar da bulalar ya shige daki ya barta tana jan numfashin wahala dan kukan ma ta kasa cigaba da yinsa.

Wanka yayi ya fito ya tsallajeta yayi waje abinsa, Munira na bakin qofar, tunda ta jiyo ihun yar uwar tata ta taho sedai tsoron karta shiga ya hada da ita yasa taci burki a gurin.

"Kar na dawo na tarar daku cikin gidana daga ke har itan" ya fada mata.

Ta sauke ajiyar zuciya da be taba lafiyarta ba, seda ya sauka daga qasan kafin ta shiga, yanda taga Bintan ta tsorata ta kamata Binta ta fashe da kuka saboda Azaba ta ko ina jikinta radadi yakeyi mata.

Hudu ta gota sanda Munira ta hada musu yan abinda zasu buqata Binta ta coccogala suka fita daga gidan Audu saboda tsoron abinda ze iya biyo bayan zamansu Alhalin yace su tafi.

Gidan Turai suka nufa dan babu halin Tafiya Kaduna a wannan lokacin, suka hadu suka ringa jimamin al'amarin.

"An auna arziqi dabe furta ya sake ki ba ai, lokaci kawai zaki bashi ya danyi fushinsa ya sakko komai ze daidaita" Turai ta fada.

Binta dake kwance magashiyyan Zazzabi na nuqurqusarta a haka ma wai taje Chemis an bata maganin rage radadi dana zazzabin shine taji dama dama.

"Yanzu ta mutuma amma tsinanniyar matar nan ba zata barni na zauna lafiya da Mijina ba Allah ya isa tsakanina da Bara'atu" ta fada tana sakin kuka.

Munirah tace
"Yanzu ashe ba zaki saduda ba Yaya Binta?

Wannan abun be isa ya zame miki ishara ba?"
"Zanci uwarki idan kika sake saka mun baki a magana" ta fadawa Muniran daga nan tayi shiru tana jinsu da Turai suna maganganu akan matakin daya kamata su dauka, ita dai Allah ya gani tayi nadama kuma tana fatan itama Bintan ta ganr gaskiya tun lokaci be qure mata ba sannan da sun je gida dole ta warwarewa Iyayensu komai daya faru saboda ayiwa tufkar hanci, muddin Binta bata rabu da wannan matar da alamu suka nuna ita take sake dorata a hanyar banza ba ba zata taba komawa ga Allah ba.

Washr gari suka tattara suka wuce Kaduna, Binta bata tsammaci abinda ta gani bayan da Munirah ta fasa kwai ba, gigicewar da Salima da Sakina sukayi ba kadan bace Ummu ko fadi take
"Kun gani ko?

Kunga abinda nake jiye muku ko?

Yanzu wa gari ya waya?

Gashi nan ta mutu ta bar muku duniyar kuji da dakon haqqinta".

Alhaji Zakariyya wanda yake fama da ciwon bugawar zuciya kusan shekara hudu kenan da ciwon ya ta'azzara masa abu kadan yake tayar masa dashi wannan tashin hankali daya riskeshi na abinda Yaran nasa suka aikata ya sake motsa masa ciwon sosai, ita kanta Maman Seda Hawan jininta ya tashi, Allah ya sani daga ita har Mijinta babu me muguwar zuciya da baqin rai irin wanda Yaransu suka gwada.

Rashin lafiyar Alhajin tasa basu bi takan Binta ba qoqarin yanda zasu cetoshi kawai sukeyi a sannan.

AUDU
Tattara yaran yayi ya maidasu Bechi bayan da Binta ta bar gidan harda Zakariyya da bata tafi dashi ba, rayuwa ta masa quncin da be taba zaton ze tsince kansa a makamancinsa ba, komai ya sukurkuce masa, duk ya gigice ya fita a hayyacinsa shi kadai yake rayuwa a gidan abinci sedai ya siya ko yaje gidajen Abokanansa yaci.

Be bi takan Binta ba balle yasan me take ciki dukda har yanzun be yanke hukunce dangane da cigaban zama da ita ba ko akasin haka cikin wannan yanayi ya share watanni biyu, Yakubu yazo Kano ya tarar dashi gashi nan shi ba me hankali ba shi ba zararre ba, dukda cewar yana da fushinsa a zuciya amma akace Jini ba wasa ba ya tausayawa Audun.

Shi ya ringa tausarsa ya nuna masa cewar kuskure dai ya rigada ya aikata a rayuwarsa yanzu abinda ya rage masa shine ya gyara sannan rabuwa sa Binta ba shine mafita ba a yanzu tunda dai ya fahimci wacece ita ya kuma san tuggu da makircin da take shirya masa a gida seya hankalta ya kuma san me yakeyi, sannan ya bashi shawara da ya hade kan gidansa, yaje ya maido da Zubaida ta raini Yayanta a gidan ubansu yasan kuma ita zata iya riqe Marayun Bara'atu ta hada da nata saboda zancen yace ze maidasu Bechi ma be taso ba ya kuma jaddada masa ya tashi ya koma makaranta ya nemi ilili na boko dana Muhammadiyya saboda Ilimi shine gishirin rayuwaz daga shi har Bintan Jahilci shine jigon abinda yake qara ingizasu ga shirmen da suke aikatawa a rayuwarsu.

Karo na farko da Yakubun ya dangantashi da Jahilci kuma ya amsa beji Haushi ba ya kuma tabbatar masa da ze bazama neman Ilimi ze kuma gyara mu'amalarsa, zancen Zubaida kuwa daman ya dade yana saqa hakan a zuciyarsa tun ma kafin Bara'atu ta sake fita daga gidansa dan haka ya roqr Yakubun dayayi masa Jagora suje dan yana kunyar Idon Mahaifinta ya sani be kyautawa Tsohon ba.

Yakubu beqi ba suka shirya sukaje, ko a fuska Malam Hassan be nuna musu komai ba ya ringa Maraba dasu ga Yan Biyu sunyi girma sosai sunyi wayo idan ka gansu zaka dauka sun shekara uku ko sama kamanninsu daya sak sedai banbancin halayya inji Malam Hassan ya nuna Hussaini yana cewa
"Kaga wannan kaiya biyo sak, rigima a cikin Hussaini harda ta bayarwa sadaka shi kuwa takwarana yanda kasan wannan dan uwan naka salihin bawa babu ruwansa haka Tagwai din zeyita cin zalinsa yayi shiru na zakaji bakinsa ba".

Audu ya sunkuyar da kai dan ji yayi kamar zaginsa Malam Hassan yake a fakaice Yakubu kuma yayi murmushi yana cewa
"Dama hakane ai duk tagwaye se an samu wannan banbancin dabi'ar daya me sanyi daya me zafi"
"Wannan gaskiya ne dan nima nawa Hussainin Allah ya jaddada rahma a gareshi haka muka sha fama tun quruciya har zuwa girma shekarun mu Arba'in da biyar Allah yayi masa rasuwa sedai shi be bar baya ba yaya hudu ya haifa duk kuma sun rigashi mutuwa" Inji Malam Hassan.

"Allah ya jaddada rahma a gareshi" Audu da Yakubu suka hada baki gurin fadi.

Shiru sukayi nadan lokaci kafin Yakubu ya numfashi ya amayarwa da Malam Hassan abinda yake tafe dasu.

"Wai, ashe baka sani ba?

Ai yau kwana Ashirin da tara kenan da Zubaida ta daura aure kwana goma sha biyu kuma da tarewarta, nan qasan mu babu nisa take Yaron Aminina Malam Bala ta Aura wannan da kuka taba gaisawa a nan har nake ce maka Daga qasar waje ya dawo yayo karatun Likitanci" Malam Hassan ya fada yana duban Audu Audun kuma ya kalli Yakubu kamar dashi ake maganar,
"Tooo ai babu labari Baba, da yake muma din an samu Rashi ne uwargidansa ce ta rasu a Makka sunje aikin Hajji ba'a dawo da ita ba wannan ya tayar masa da hankali har yasa ya dauki lokaci haka be leqo Yaran ba.
Chapter 76 · 0% Book details