Sashe 54
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Binta ta shiga tana cewa
"Eh ai ita da yake ta fiki tunani tana kuma da abinyi a gida shiyasa ba zata zauna ba tunda babu aikin da zatayi"
"Kai Hajiya" Lantanar ta fada tana yaqe dan taji zafin maganar Bintan kullum haka take yaba mata su da tana da zuciya yaci ace yanzu ta haqura da aiki a gidan gaba daya.
Binta ta shimfide Zakariyya tana miqa tareda wash
"Ai yaci ki dena goyashi haka Hajiya kar ku ringa danne na cikin, in fita ta kama ki ringa cewa na turo miki Aisha ta mana tana tayaki da daukarsa" Lantana da bata daddara ba ta sake fada, se kuma akaci sa'a Bintan ta yarda da shawarar tace zata ringa yin hakan.
Tana zaune a Falo tana ayyana yanda maganar nan zata tashi Lantana na share share sega Audu kamar an jefoshi ya fado falon, ta miqe da sauri tana tambayarsa lafiya kuwa yace
"Babu lafiya, yanzu Suleiman ya dawo daga Bechi yake shaidamun Allah yayiwa Babansu Bara'atu Rasuwa, ki shirya yanzu zamu tafi can dukda dai nasan ba zamu samu jana'iza ba amma gara muje din in yaso ma dawo gobe".
Binta taja tsaki bayan data koma ta zauna tana cewa
"Shine ka shigo a gigice har kana fadar mun da gaba na zata ma qata asarar ce ta fadawa Dukiyarmu?
To Allah ya jiqan musulmi amma babu inda zani da ranar nan fatsar fatsar".
Zubaida na bacci bacci ya shiga itama ya shaida mata rasuwar, iyakar abinda ta sani kan Bara'atu tsohuwar matarsa ce ba'a fi watanni biyu bama data san itace uwargidansa ba Binta ba a bakin Mairo mewa Binta Girki ranar ta roqeta ta koya mata yanda akeyin Gero da wake shine tace ai Maman Baba ma tana son Abincin a sannan ta tambayeta wacece ita tace mata Bara'atu uwargidan Audun tayi mamaki kwarai jin har yara biyu ne tsakaninsu dan be taba gaya mata ba data yi masa zancen kuma har yajin kwanaki ya mata saboda tace be kyauta ba dakyar suka shirya bayan yaja mata kashedin babu ruwanta da sabgarsa wadda bata shafeta ba, bata san meya rabashi da Bara'atu ba dan haka karta kuskura ta tsoma kanta a ciki shiyasa kidimewar da yayi yanzun da ya gaya mata rasuwar Baban Bara'atun ta bata mamaki, matar daya cire daga rayuwarsa ita da Yayan da suka haifa tare na menene ze dawo dan ta rasa mahaifi?
Haka ta cicciba ta hada abinda zata buqata a yar jaka tana hasaso yanda yan Bechin zasu karbe ta wannan karon, bata sake zuwa ba tun bayan da aka kaita wancan Al'amarin ya faru haka suma A matan Aisha ce kadai tazo babu dadewa tana ciwon Nono Audu yace tazo Kano taga Likita ta kwana hudu a dakin Zubaidan kuma dai lafiya lau babu abinda ya hadasu har suka rabu ta koma.
Bata san banda Binta za'ajwe ba seda yaceta fito su tafi, ta kulle qofarta tana tsaye jikin dakin Tsakar gida wanda Abdullahi yake kwana ciki kafin a kaishi makarantar kwana tun daga nan kuma idan anyi hutu Bechi yake tafiya da Audu ya tambayi ba'asi yace babu komai be matsa ba ya qyale shi kuma dai be fasa yi masa komai ba tamkar yana gidansa ze aikawa da Aminu kudin komai nasa ayi masa.
"Ba tare da Maman Zakariyya zamuje ba?" Ta tambayeshi jin yace suje,
"Badani za'aba uwar azagwai" Binta dake tsaye kan Baranderta ta turo dauri gaba irin wanda Zubaidan takeyi ta fada kome ta tuna kuma se tayi saurin sakin fuska ta matso kusada ita tana cewa
"Yauwa kar in manta, idan kun dawo daga Qauyen nan akwai taimakon da zakimun.
Wlh in gaya miki qanwar qawatace Ibtila'i ya hauta wani shege ya dirka mata ciki, to kuma ta samu Miji Aure nan da wata biyu wannan abu ya faru shine nace ko zaki taimaka ki kaimu inda kuke zuwa a kwantar muku da ciki a samu asiri ya rufu ayi Auran nan idan yaso intayi wata kamar biyar a tayar dashi ko kinga sahu a likafa babu me cewa wani abu".
Sak Zubaidan tayi tana kallonta har ta kai qarshe yanda take doka murmushi kadai ya isa yasa ka gane babu Allah a ranta makirci ne zallah ta hado, waiwayawa tayi ta kalli inda Audu yake tana fatan ace ya rigada ya fita beji wannan maganar da Bintan takeyi ba amma se taga yana tsaye ya zuba mata ido tamkar yanda Bintan take kallonta tana murmushi.
"Kinyi shiru baki ce komai ba" Bi ta ta sake fada har tana dafata fuska dauke da murmushin makirci se ta saka hannu ta tureta tana cewa
"Bani da lokacin Amsa shirmenki"
Binta tayi shewa harda rangada guda tace
"Allah nawa Annabi na uwata, yarinya ba kecw bakida lokacin amsani ba nice bani da lokacinki, kuma shirme da kikace a tsakaninmu za'a tantance wadda take shirme kwanannan, kiyiwa Bara'atu gaisuwa injini kinji Allah ya jiqan Babanta" daga haka ta juya tana kada Mazaune tana waqa abinta.
Zubaida na tsaye inda take ta kasa motsi har seda Audu yayi mata magana kafin ta shiga daga qafa dakyar har suka fita.
Seda suka dauki hanya sosai motar shiru babu me cewa qala kafin ya yanke shirun ta hanyar yi mata maganar data saka qirjinta bugawa dam kamar ze fashe.
"Sanda kikace kin zubar da ciki dagaske kike ya fita ko kuwa qaryarku ta yan bariki kikayimun?"
A razane ta kalleshi, hankalinsa na kan titi fuskar nan a hade tam kamar ta shanu.
Shiru tayi zuciyarta na tsinkewa, takalarta yakeyi da masifa ita kuma bata shiryawa hakan ba bata da kalaman da zata kare kanta dasu a yanzu ta tabbatar matarsa ta rigada tayi masa famfo shiyasa ta tayar da wannan maganar a gabansa qila kuma ta rigada ta fada masa abinda take so ta fada wannan da tayi fami ne ta barbadawa ciwo gishiri.
"Ba magana nake miki ba kin mayar dani dan iska kinyi shiru" ya fada cikin masifa harda buga sitiyari, Zubaidan ta zabura saboda tsawar ta shigeta amma a maimakon tayi magana se kawai ta fashe da kuka.
To me zata ce masa dan Allah?
Kwafa yayi be sake ce mata komai ba har suka isa Bechi, sun tarar da Anyi Jana'izar Babansu Bara'atu, a qofar gidan suka tsaya daman ya fice ya barta a motar ya tafi gurin Maza masu karbar gaisuwa Tilas ta fita ta shige qofar dataga Mata na shige da fice.
Bata san kowa ba dan haka ta tsaya tana raba ido,
"Ashe tare kuke" taji an fada daga bayanta ta waiwaya ganin Aisha yasa ta saki ajiyar zuciya a qalla taga wanda ta sani.
"Muje ciki" ta sake fada mata se tabi bayanta suka ratsa matan dake zaune ta gaishe su tareda yi musu ta'aziyya kafin suka dangana da Rumfar Inna Hajara.
Anan taga Bara'atun tana rakube gefe ta sake zama fiyat da ita ga tashin hankalin mutuwar data riskesu ta farat daya idan ka ganta gwanin tausayi.
Aisha ce ta gabatarwa da Bara'atu da ita. a matsayin Amaryar Audu, suka sake gaisawa kafin Aishar tace su koma tsakar gida dan yafi iska.
Bayan su.
Zauna Bara'atu da kanta ta fito ta kai mata ruwa da Kunun Tsamiyar da aka kawo na sadaka tace
"Ki dan sha wannan kafin a sauke abinci"
"Nagode" Zubaidan ta fada a sanyaye badan zata iya sha ko cin wani abu ba dan jiki da zuciyarta gaba daya batajin dadin da zata iya saka wani abu a bakinta a halin yanzu.
Sunyi jugum jugum Aisha tace
"Itace matar Yaya Audu ta farko, Makircin Binta ne ya fitar da ita daga gidan ta qulla mata sharrin wai ta kashe mata Jariri ranar suna"
Qirji Zubaidan ta dafe tana zare idanu, tuna a inda suke yasa ta saisaita kanta cikin kaduwa tace
"Kashe jariri?"
"Wlh fa, kuma sharri tayi mata dan wlh ko kiyashi Bara'atu ba zata kashe da gangan ba balle mutum sahun barawo ta taka yaron dama ya rasu shikenan suka liqa mata sharri daga shiga dakin shi kuma Yaya Audu babu binciken komai ya yanke hukunci dalilin mutuwar Auranta kenan shekara Uku yanzu".
"Uhm" kawai Zubaida ta iya cewa, wato ashe nata tuggun da take shirin qulla mata me sauqi ne akan na Bara'atun kisan kai fa kuma na rashin Imani ace Jariri ka kashe wannan ai tayi mata tambarin da ba kowanne Namiji ne ze iya dauke kai ya aureta ba wadda ta iya kashe dan Jinjiri babu tausayi ai kisan babban mutum qaramin abu ze zama a gurinta.
Haka ta ringa jimanta maganar jikinta ya qarayin sanyi qalau da Al'amarin gida Audu, taga Babangida da Babannan sun girma Masha Allah musamman da suna da garin jiki irin na gidansu se suka tashi kamar yan biyu sedai duk su biyun suna nan a hargitse yaran qauye dai sak to uwarsu bata da nutsuwar zuciya balle ta iya samun damar kulawa dasu yanda ya kamata, Manema uku ta samu bayan rabuwarta da Audu biyu duk ba yan garin su bane amma da sunyi zuwa daya biyu za'a samu wani annamimin da zeje ya soke maganar sedai taji shiru ba zata sake jin duriyarsu ba wannan abin yasa ta shiga damuwa matuqa ga tunanin Audu da soyayyarsa data qi barin zuciyarta sedai ta sani ya mata nisa bama ta yiwa kanta fatan komawa gidansa Addu'arta daya ce a kullum ubangiji ya warware mugun qullin da Binta tayi mata ya wanketa a idon Audu da duk wanda ya yarda da sharrin da aka mata.
Se Yamma Aisha da Zubaida suka bar gidan rasuwarz babu motar Audu a waje hakan ya tabbatar musu ya wuce gida dan haka ta rakata can kafin ta wuce gidanta itama dan Magriba ta kawo kai.
"Kace badan wannan rasuwar ba qila da sedai kuzo kawo mana Jariri ko Jinjira" Goggo Fadi ta fada sanda Zubaidan ta shiga dakinta gaisheta ta tarar da Audu a ciki.
Bece komai ba itama bata amsa ba se kanta data qara yin qasa dashi.