← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 91

Sashe 75

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata mata ce take fadin
"Dazu take cemun tun da muka hau jirgi tayi addu'a idan har ta kammala aikin Hajjinta lafiya kuma ibadarta ta karbu tana fatan ubangiji ya karbi ranta a binneta a qasar Ma'aiki tace tsoro takeji anya kuwa tayi Hajjinta daidai ashe lokaci yana tafe ubangiji ya karbi shahadarki Bara'atu Yarinyar kirki yarinyavme haquri Annabi yasan da zuwanki" haka akayi jana'izar Bara'atu da Asuba a masallacin Harami aka binneta a maqabartar da ba kowa yake samun wannan Alfarma ba se me tsananin rabo shikenan rayuwar ta qare ta tafi ta bar Binta a duniyar da take ganin ba zata qare ba.

Dawoqar Mahajjata a maimakon murna se Al'amari ya juye na koke koke da Jimami, duk wanda yaji mutuwar Bara'atu seya girgiza hatta da Binta da da take ganin idan aka bata wuqa zata iya dabawa Bara'atun se gashi sanda labarin mutuwarta ya rsketa zuciyarta seda ta tsinke ta kuma girgiza.

Munira qanwar Binta da tazo Kano tun Bayan qaramar sallah dalilin takurar da Mama take mata akan ta fitarda Miji bayan kamar wadda aka sakawa hannu Sauro be taba tsaida ita ba bare yaje gidansu da sunan zance shiyasa ta tattaro ta taho gurin Bintan saboda ta samu sauqi kuma qila ta samu Mijin a nan sanda taji zancen mutuwar Bara'atun kuka ta fasa ta dora hannu tana tumami
"Mun shiga uku Yaya Binta matar nan ta mutu bamu nemi yafiyarta ba wlh inaga haqqintane ya kamamu gashi naqi Auruwa Anty Sakina haka siddan aka koreta daga gurin aiki duk irin hanyar Dady da mutanen daya sani ta kasa samun wani aikin ga Mijinta ibtila'in daya fada masa daman da aikin nata suke lallabawa da tallafin da Dady yake bata to ta rasa aikin ita kanta Yaya Salima cikin garari take masifar yau daban ta gobe daban gashi yanzu ta mutu balle mu roqeta ta yafe mana qazafin da muka mata shikenan haka rayuwarmu zata qare a balbalce ni kenan bazan taba yin aure na na shiga uku na lalace wayyo ni Munira kaicona dana biyewa shedan muka laqabawa Baiwar Allah sharrin kisan rai bata ji ba bata gani ba" magana take cikin ihu da kururuwa wanda mutanen da suke tsakar gida Yan Bechi da sukazo tarar su Bilki duk sun Jita, Audu na kan Baranda dan jiri ne yake neman kadashi tun sanda labarin mutuwar ya riskeshi shiyasa ya zauna a gurin ana masa fifita se ga wata sabuwa yana jiyowa daga dakin Binta.
*PROMO PROMO PROMO*
*Nace kina da Labarin MOMMY MOROCCO ME KAYAN MATA KUWA?* *Ko kuwa dai kina nan zaune baki wangale kina fama da masu niqa Kuka da Citta ko su qulla miki Garin Masara da sunan Magani*? *To ki karkade kunnenki Yar uwa ki kuma maza ki dauraye qafarkin nan da tayi furu furu domin MOMMY MOROCCO Ta diro Nigeria kuma tafe take da Abin Arziqi Niqi Niqi*
*Ina mai farin cikin shaida muku Moommy Morocco zatayi BONANZAr kayanta na kwana biyu*.
*Tazo muku da zafafan magungun wanda ya taba amfani dasu ne kadai ze baki labari Ingantattun magunguna na gani na fada ajin farko wanda aka hadasu cikin tsari da kula daga Ganyayyaki da kayan abincinmu masu qara lafiyar jiki da saukarwa Mace Ni'imar da take buqata kayanta babu Algus babu abinda ze cutar dake da yardar Allah*
*1-Da akwai hadin First ladies exclusive VIP package*
*2-Qafarka qafata package*
*3-Kankat package*
*4-Da kuma Mini package*
*Tazo muku da gangariyar maganin SANYI sadidan na Jiki dana Mara wanda In sha Allaahu ba ke ba sanyi kuma za a iya ba wa Yara, Maza ma suna sha*
*Bata tsaya iya nan ba tazo da Turarukan ta na ban mamaki se wanda ya gwada ze bada labari, Kedai kada ki bari de wannan damar ta wuceki domin ta zabtare Farashin kayanta har zuwa kaso 50% discount!

Kyaso wannan gara basa ta wuce ki kuwa Indai ba Bintan Audu kike ba*
*A tuntubeta a WhatsApp:09086233009*
*Ko kiran waya a 08029988065*
*Siyan Nagari Maida kudi gida*
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 29*
"Ke Munirah meye haka?

Baki da hankaline kike daga murya baki san bamu kadai bane a gidan nan?" Binta ta fada a rikice tana qoqarin toshe mata baki Muniran ta fizge tana cigaba da cewa
"Ki barni Yaya Binta abin kukane ya sameni dole nayi, daman Yaya Ummu seda ta fada, tace akwai ranar da zamuyu kuka muyi Nadama, seda tace tun muna da sauran lokaci mu kwance qullin da muka daura a lokacin ban dauki maganarta da muhimmaci ba, haka kawai muna zaman zamanmu muka jazawa kanmu masifa ta hanyar shiga haqqin baiwar Allah da bataji ba bata gani ba muka bata mata suna kuma mukayi silar mutuwar Auranta gashi yanzu ta mututu ta bar mu a duniyarda nauyin haqqinta a kanmu nidai Allah ya isa tsakanina daku kun cuceni wlh" ta sake fada muryarta a sama tana rusa kuka.

"Alhamdulillahi!

Dadina da gobe saurin zuwa, Allah nagode maka daka matsi bakin Azzaluman bayinka suka tonawa kansu Asuri, kaiconku wlh, kaicon Zuciya me cike da Mugunta da Zalunci irin taku.

Yanzu ai ga duniyar nan gaba daya bama gidan Audu ba ta tafi ta bar muku se ku shinfida tabarma ku cigaba da zama kuna kasa abinda kukaga dama a cikin duniyar, amma ku sani wlh cutar da kukayiwa Bara'atu bazata barku ku zauna lafiya ba, yanda kuka saka rayuwarta cikin qunci da takura harta koma ga mahaliccinta da yardar ubangiji haka zaku qare taku" Bilki ta fada idanunta na tsiyayar da hawaye, ta waiwaya ta kalli Audu daya runtse ido kamar yayi bacci a inda yake zaunen tace
"Baka da banbanci kaidasu, yanda zasu qare rayuwarsu suna girbar sharrin da suka shuka kaima haka zaka qare taka kana Nadamar zamanka da Bara'atu"
"Ke Bilki menene haka?

Da wanne kike so yaji dan Allah?" Aminu ya katseta.

Bata kulashi ba taci gaba da kukanta.

A cikin daki kuwa Munirah na gamsheqar kuka Binta na tsaye akanta ta harde hannye gaba daya kanta ya qulle ta rasa abin da zatayi a lokacin, ji take kamar ta rufeta da duka shegiyar yarinya ta kwance mata zani a Kasuwa yanzu da wace kalma take so ta gyara kwabar da tayi mata?

Tana jiyo sanda su Aminu suke fadawa Audu zasu wuce saboda kar suyi dare a hanya.

"Ka daure ka shiga daki ka kwanta, rayuwar kenan daman farkonta da qarshenta dan taqin kadan ita dai Bara'atu tata ta qare kuma In sha Allahu munayi mata kyakykyawan zaton tana Babban masauki addu'a kadai zamu cigaba da bibiyarta da ita kafin tamu tafiyar ta riskemu Allah yasa kuma abinda ya faru a baya ya zame mana darasi a rayuwarmu gaba daya" Aminu ya sake fada masa daga nan suka fara haramar wucewa Bechi.

Cikin yanayi me ban tausayi Audun ya miqe, dakyar ya iya ce musu Allah ya tsarw hanya ya daddafa ya haye samansa a falo yayi zango ya kwanta rigingine a qasa wani zafi da radadi yake ji daga can cikin zuciyarsa, numfashinsa ya ringa fita da sauri da sauri tamkar wanda yayi gudu a, a sannu ya baiwa Idanunsa damar fitarda abinda suke muradi, hawaye ya gangaro ta gefen idanunsa zuwa cikin kunnuwansa, tamkar me tsoron wani ya jishi ya saki kuka kamar mace, kuka me tafe da abubuwa da yawa a cikinsa.

Cikin muryar da bata fita yake cewa
"Dana san mutuwa zakiyi Bara'atu da ban rabu dake ba, inama ina da damar maido da baya, dana canza zaman da mukayi zuwa mafarkinki, dana san rayuwarki ba zatayi tsaho ba da...da...." Ya kakare yama rasa abinda ze fada se kawai yaci gaba da kukansa a hankali kewar Bara'atun me nauyi tana dirar masa.

Kalamanta na sallamar da tayi masa suka ringa dawo masa kamar sannan take maganar, tace ta yafe masa amma bashida tabbacin Allah baze kamashi da laifin cutar da ita ba wai meya shiga kansa shi?

Meyasa ya kasa tantance gaskiya da qarya a zamansa da Bara'atu?

Me yasa ya gagara yi mata uzuri ya ringa Muzguna mata yana tozartata?

Yanzu gashi ta tafi ta bar masa duniyar dai, tayi masa nisan da baze taba taddota ba.

Seda yayi kuka me isarsa kafin ya tashi dalilin kiran sallar Azahar da ake tayi yana layi kamar wanda ya shawu ya dauro Alwala, baze iya sauka ba dan haka a nan yayi sallarsa addu'arsa gaba daya ta nemarwa Bara'atu Rahmar ubangiji ce, yana nan zaune yayi zuru zuru kamar wanda ya kwana zawo, motsin hawowa saman ya jiyo, ya waiwaya ya kalli qofa daidai nan Binta ta shigo da Try a hannunta ta doro kulolin abinci jikinta sanye da Zurmemen Hijabi har qasa fuskarta tayi jaa ta kumbura kamar wadda tasha kuka ta qoshi.

A gabansa ta ajiye Try din ta zauna se ji yayi ta fashe da kuka tana hailala da salati, yayi zukudi yana kallonta kawai.

"Mun shiga uku mun lalace Ashe Bara'atu mutuwa zatayi daman?

Me yasa yarinyar nan bata haqura munyi zaman lafiya anyi rabuwar arziqi ba?" Yeeee ta sake rushewa da wani kukan.

"Binta" ya kirata cikin kaushin murya, tayi dif daga kukan munafurcin da takeyi ta kalleshi, cikin sautin daya fi na farko ya sake ce mata
"Zan sake tambayarki menene gaskiyar abinda ya faru ranar sunan Zakariyyah?"
"Wace gaskiya kuma wai kake buqatar sani bayan abinda nida yan uwana muka shaida maka tun a waccen ranar?
Chapter 75 · 0% Book details