← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 91

Sashe 10

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tunda ka tafi makarantar kwana shikenab bamu sake haduwa ba shekaru kusan takwas kenan amma banji dadi da Audu yace mun ka bar Boko ba, kaga ni yanzu haka ina shekarar qarshe a Jami'ar ABU zaria ina karantar Engineering da ace ka cigaba kaima yanzun ko baka gama ba kana kan hanya" Hayatun ya fada.

Yakubu yayi murmushi kawai amma bece komai ba, duk wanda ze so masa da yayi Boko a bayan kansa ne dan mafarkinsa ne ya zama Alqali tun besan me hakan yake nufi ba.

Ganin bazeyi magana ba yasa Hayatu cewa ya tashi suje ya kaishi inda Audun yake dan shi suna haduwa sosai har inda ya kama hayar shago yake zaune a can Goron dutsen ya sani.

A kasuwa suka samu Audu yamma tayi anata hada hadar kasuwa dan a sannan ma ake cin kasuwar sosai, kayan yaji yake siyarwa a sannan da sauran kayan qamshi zuwan Yakubu tasa dole ya tattara komai suka tafi masauki.

Seda sukayi sallar Magriba da isha, ya rasa ma me ze ajiyewa Yakubun, ya kwaso Wasu yadika dinkakku kala biyu kowanne saiti uku a ajiye masa sannan ya sake dakko Shadda dinkin babbar riga shima guda biyu ya ajiye yana cewa
"Na Baballiya ne ba'a gama ba, daman Juma'ar nan nake cewa idan Malam Mudan ya shigo zan hada masa yayo mun gaba dasu kar kaya suyi mun yawa idan na tashi tahowa"
"Yanzu dai duk ka ajiye wadannan ka saurari maganar da nazo maka da ita" Yakubu ya fada yaba tattare kayan gefe, Audu ya zauna yana kallonsa se a sannan ma ya lura da cewar Yakubun bashida walwala dukda dai shi daman bame hayaniya bane sosai.

A taqaice Yakubu ya bashi Labarin daya gigitashi jin cewar an sakawa Bara'atu rana da wani dan uwanta ya shiga share zuba dukda qofar Shagon a bude take ga iska na busowa amma Audu zufa yakeyi kansa ya shiga sarawa jin ze rasa Bara'atunsa macen daya gama kwallafa duk wani buri na duniya akanta.

Shikadai yasan irin tanadin da yakeyi akan auransu shine yanzu Babanta zece ya bawa wani ita.

"Shiyasa kullum Dada take maka magana akan kasan me kake ciki saboda gudun haka, ban dama Inna Hajara tana tataka ai kasan tuni Bara'atu ta dade a daki Bilki da suke sa'anni kana gani da ciki yana tsaya mata ai tayi yaya biyu ko uku yanzu tunda dai ga Aisha nan da ciki Auran bana se ita kake so tayita zama har se sanda ka gama shirinka duk sa'annin ta sunyi Aure har an fara zundenta a gari " Yakubu ya fada.

Audu dai bece masa komai ba haka suka kwanta amma fa be iya bacci ba, cikin daren ya hada yar jakarshi, Asubar fari suka dauki hanya dan yace baze tsaya ganganci ba dole yaje a san me ake ciki amma da ransa baze bari wani ya auri Bara'atu ba.

Bayan dogon tirka tirka da yayyensu daga qarshe suka yarda zasuje tambaya masa Auran Bara'atun, sunje da fari Babanta yaso yayi gardama akan shi ya rigada ya amshi maganar wani ya basu haquri suka taho gida Hashimu har yana Allashi qara ai gara haka, seya koma can Birnin da ya liqe yagani idan ze samu macen da zata aure shi babu wanda yasan saga inda yake kujifa.

Kwana biyu tsakani Audu na kwance yana jinya tunda yaji cewar baza'a bashi Bara'atu ba sega dan aike daga gidansu akan Babanta yace ya turo yau a daura musu Aure ashe wai Rijiya ta durfafa dagaske zata fada idan ba'a fasa auranta da wancan ba, harta tsoma qafa daya babanta yaga dai dagaske bata hayyacinta shine yace ya janye amma fa sedai Audu ya turo yau a daura Aure dan muddin aka kai ranar daya saka da wancan tofa sedai ta mutu shine Innarya ta tashi Yayanta ta aikoshi, Audu najin batun ya miqe beyi wata wata ba ya kama hanyar Gona inda su Yakubu suke can suna gyaran kunya kamar wani yaro ya zube yana basu labarin abinda akace.

Daga qarshe dai Yaya Baba da wasu Abokanan wasansu biyu ne suka sake zuwa dan Hashimu yace ba inda zeje, an samu Baban Bara'atu ya haqurq da zancen daura aure ranar aka tsaida magana akan rana daya dana Yakubu.

Da wannan farin ciki Audu ya koma Kano, dukda ba haka yaso ba.

So yayi ace se yayi gida a Kano sannan zeyi aure dan biki yake so yayi irin wanda akeyi A Kano yayiwa Bara'atu lefw na yargata wanda ze zama abin tarihi a garinsu harda kewaye, amma yanzun ma bata baci ba, zeci gaba da qoqari kuma ko ba yanzu ba seya biya bashin duk abinda ya qudurci yi mata.

A haka kwanakin Biki sukazo, a zatonsa za'a daura aurene kawai tunda kowa yasan bashida Mahalli yayi qoqari ya siyowa Bara'atu kayayyakin fitar Biki daga Kano aka dinko harda takalma da mayafai kala hudu yayi mata na yan birni.

Ana saura kwana hudu daurin Aure ya tafi Bechi bayan yayi sallama da Abokanasa na kasuwa dana unguwa dukya shaida musu zeyi aure, amma biki ba yanzu ba suka hada masa gudummawa kuwa sosai har seda yayi mamaki, koda yake shidin ba daga baya ba gaskiya bashida rowa ko kadan, haka Biki, suna, ta'aziyya sedai idan beji ba suma duk sun masa Alqawarin idan biki ya tashi zasuje tunda yanzu abin yazo a qurarren lokaci basu shiryi tafiyar ba.

Ranar Juma'a aka daura Auran, na Yakubu aka fara daurowa da safe a can Rigarsu Balaraba suka dungumo da Amarya da yan uwanta, se bayan sallar Juma'a aka daura na Audu da Bara'atu.

Murna kam ba'a cewa komai a gurin Dada da tasha kwalliya cikin kayan da Audu ya dinka mata, haka qannensa Bilki da Aisha sun sha Anko Baballiya kuwa shaddarsa iri daya data angwaye wanda dama Audu ya dinka musu da niyyar suyi fitar bikin Yakubu se gashi abu yazo a daidai.

Qarfe tara suna can Majalisa da Abokanai ana ta shaqiyanci sega Baballiya da gudu yake fada musu wai an Kawo Amaryar Yaya Audu.

Kowa yayi mamaki dan ko jiya da yaje gurinta seda suka sakeyin maganar tace masa Innarta tace se daga baya zata tare tunda abin yazo babu shiri Babanta kuwa Magriba nayi ya tada ballin se an kaita, an ce masa babu daki yace ta rakuba a na Babarsa da ya san be shirya auran ba yayi haka yan uwa suka rakota ita kam ko a jikinta dan ko cikin Rumbub gidan aka ce ta zauna shiga zatayi tunda dai burinta ya cika ta Auri Audu.

A dakin sa aka sauketa da qawayenta da zasu kwana, daren ranar Audu tunanin yanda zeyi kawai yake, da yasan za'ayi haka da ya ququta ko babu dabe itama an tayar mata da daki ko ciki dayane, haka dai gari ya waye, da hantsi yan uwan Balaraba suka gama mata jere tsaf irin na yar gata harda Kumbo nan suka fara shirin tafiya bayan sun qara damqa Amarta a hannun yan uwan Yakubu.

Daga bangaren Bara'atu dai babu wanda yazo se qawayenta da suka kwana.

A can gidansu ana ta taqaddama tsakanin Babansu da Innarta akan yace ko tabarma baze kai mata ba tunda bata bi abinda yake so ba, ita kuma ta rantse se yayi, da yasan haka ne seya bata lokaci ita da take son auran zatayiwa yarta komai amma yanzu banda kwanuka babu abinda ta tanada dan haka dole ya fito da kayan gado danbaze barwa yarta abin gori ba bayan ba rasa abinda zeyi mata yayi ba gashi tun rana bata daga ba labarin jeran da akeyiwa Balaraba ya fara bazuwa a gari dan itama Babanta Attajirine a rugarsu kuma itace Auta a mata dan haka sun mata bajinta.

Hayaniyarsu har dakin Ilu Abokin Audu da suka kwana a gurinsa maqota suke dasu Bara'atun kuma dakinsa jingibe yake da dakin Soron su Bara'atu inda Innar tata da Baba suka shiga wai suna sirri saboda yan biki dake ciki se gashi Audu yaji komai, sulalewa yayi ya tafi cikin garin Kumbotso saboda yafi masa kusa akan yace ze tafi Kano, yasan gurin lokaci lokaci yana zuwa dan har Aboki yake dashi kai tsaye gurinsa ya tafi bayan sun gaisa be bata lokaci ba ya zayyane masa abinda yake tafe dashi na batun kayan daki saboda garinsu Babu Kafinta meyin kayan katako, gadon qarfe kuma a gurinsa shi da yake zaune a birni yake ganin kayan gado da akeyi na Alfarma ya fitar masa yayi.

Nura ya kaishi gurin wani Kafinta da ake ji dashi a Kumbotso dan a Kano ya koyo aiki wasu kayan ma daga can yake dakkowa ya kawo.

Ya numa masa wani Gado Lamba 1 da Kobud dinsa me biyu ta yan gayu dan harda mudubi a jikin murafenta ga kuma mudubi shima me durowa uku a jiki kayan sunyi kyau gasu Ruwan Hoda irin kalar da Bara'atu take so sedai kudin da aka saka musu a yanayin da yake ciki sun masa yawa ga Katifa da ze siya da pillo, aka tirza aka tisa dakyar dai kaya suka siyu, shima seda Nura yayi masa ciko daga baya zasu warware tunda suna haduwa A Kano, aka loda masa su a A kori kura da dundumemiyar katifa da pillow biyu harda Abin shimfida dana rufa ya kama hanyar gida.

Sanda ya dawo yamma tayi rana na gabda faduwa, a waje ya bar masu mota ya shiga ciki nan ya tarar da Dada da yan uwanta da basu wuce ba suna ta kiciniyar kwashe yan kayayyakinta ana shigar dasu dakinsa nasa kuma suna waje da alama dakinta za'a mayar dasu daman ba wani shirgi ne dashi ba Gadon qarfe ne da wata Katifa da yake ta saka ranar canzata tunda ba kullum yake kwana a kai ba se yayi ta mantawa se akwatinsa guda daya.

Kunya ta kamashi yanda aka faka kayan a gefe, kenan Dada dakinta zata basu kuma wannan Gadon za'a sakawa Bara'atu
"Yawwa ga Audu" Matar Yayan Dada da basu yada zumunchi ba ta fada dan tun safe ake nemansa an rasa shi ga babu waya bare aji inda ya tafi.
Chapter 10 · 0% Book details