← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 91

Sashe 2

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiya fara miqewa ya kalli Aminu dake harhada takaddun gabansa cikin izgili yace
"Dama anyi gadon farar qafa dole a tsammaci abinda yafi wannan, Allah dai ya sauwaqa ya kuma tsayar iya kanku kar a bata mana sauran iri da halin bera" yana gama fadar hakan ya juya ya fice daga gurin dukkan su kuma sunji abinda ya fada, Da daddaya suka ringa ficewa daga conference room din ya rage Alhaji Audu, Alhaji Abdullahi wanda yake heading bangaren Siminti kuma dane a gurin Alhajin Audun ma'ana dan Yayansa ne da suka hada uba se Mustapha Manzo, shugaban Legal department na rukunin kamfanunuwan Bechi.

Alhaji Abdullahi ya kalli Alhaji Audu dayayi shiru da alama yayi nisa a tunani, cikin ladabin da yake masa tun usulan yace
"Gaskiya Baba a iya fahimtata da kuma binciken da nayi bana zargin cewar Aminu yana da saka hannu a cikin batan kudaden nan"
"Nima dai abinda zan fada kenan, nayi amfani da duk wasu measures da muke using gurin gano me laifi banga wasu alamu na rashin gaskiya a tattare dashi ba.

Amma abinda yake bani mamaki shine tabbas kudi sun bata amma babu wata alama da za'a iya tracing a ga inda kudin suka tafi tunda ba transfer akayi ba and we don't deal with huge cash here ballantana ace cash aka debe su.

Ni dai what I'm thinking is that kudin nan dama babu su, lissafin bogi aka bashi kawai kuma ina ganin matsalar badaga ko ina aka samota ba se daga Oil Sector.

Tunda Naziru ya fara heading gurin nan ake samun runton lissafi Mr Obasaki yana yawan kawo mun qorafin idanna sanar maka Alhaji baka daukan wani mataki na sosai and i don't know your reasons for that.

Ire iren wadannan abubuwan ya saka mutane da yawa basa mixing Family with business saboda abinda bare zeyi maka ka dauki mataki idan Jininka ne dole ka daga amsa qafa, amma maganar gaskiya idan ana so a ga daidai se an gyara saboda kowa yasan can ne bangaren dayafi kowanne kawo profit idan aka cigaba da irin wannan tafiyar ina tsoron kar wata rana a wayi gari babu uwar kudi ma balle riba" Mustapha Manzo ya fada, yanda yake maganar duk wanda ya saurareshi dakyau ze fahimci jirwaye yakeyiwa Alhajin me kamar wanka.

Kai tsaye baya so ya dora alhakin batan kudin akan Naziru tunda bashi da hujja amma yana so Alhajin ya bincika da kansa ya tabbatar.

Alhaji dake sauraronsu a zahiri yana gyada kai amma a badini kanzil bazece yaji daga abinda suke ta babatu akai ba maganar farar qafa da Zakariyya yayi ce take masa yawo a zuciya wasu shudaddun Al'amura da suka faru a baya suka shiga dawo masa kamar auransa da Mahaifiyar Aminun, abubuwan da suka gidana a tsakani har zuwa rabuwarsu.

"Nidai Baba idan ze yuwu a janye maganar korar Aminu daga company nan, za'a iya suspending nasa na wani lokaci amma Yaron yana da matuqar qoqari kuma ya dace da gurbin da aka sakashi akai" Alhaji Abdullahi ya sakeyin magana se sannan Alhaji Audu ya dubeshi, kallon dansa na cikinsa yakeyiwa Abdullahin saboda shi ya fara riqewa kafin ya samu nasa yayan, haka kuma yana yi masa biyayyar da qalilan daga cikin wadanda ya haifa a cikinsa ne sukeyi masa irinta.

Cike da Izzar data zame masa jiki yace
"My decision is final, idan shi Barrister Manzo be sani ba, kai kasan Hadiza ka kuma san dalilin rabuwata da ita dan haka bazan yi ganganci a matsayin kuskure ba" daga haka ya miqe tsaye yana gyara zaman babbar rigarsa datasha wani aiki irin na sarakai.

A baya suka biyo shi duk rayukansu babu dadi har suka shiga Elevator Barrister Manzo yana so ya sake magana amma Alhaji Abdullahi ya hanashi.

Tun kafin qofar Elevator ta gama budewa gaba daya suke jin hayaniya, Reception din cike da ma'aikata da sukayi cirko cirko se muryar Naziru dake tashi kamar ana yaqi.

Cikin karadi da kwaroroto irin na Mahaifiyarsa yake cewa
"Wlh Babu inda zaka je se ka bude jakar nan mun cajeta, hauka ma akeyi kenan.

A kamaka dumu dumu da laifin sata a koreka daga aiki sannan ka lullubo jaka zaka fita bamu duba munga meye a ciki ba salon ka kwashi sirrikan mu ka fitar ka saidawa Yan hamayya ko to baka isa ba" ya fada yana kiciniyar fincikar Bag pack din Aminu daya saka duk wani abu nasa me muhimmaci da yake a tsohon office dinsa tunda an sallameshi daga gurin.

Alh Abdullahi da Barr Manzo suka nufesu da sauri jin abinda yake faruwa, Alhaji Audu kuwa ko a jikinsa ya nufi qofar da zata fitar dashi daga building din.

Daf da ze fita kunnuwansa suka jiyo masa wasu mata biyu ma'aikata dake saga gefe suna kallo daya tana cewa
"Nidai Safna da arziqi irin na wadannan mutanen gara talauchi da kwanciyar hankali, su fa basu san abin kunya ba, wlh Chairman dai bewa kansa tanadi na kwarai ba Allah ya baka arziqin zuria amma ka tarwatsasu babu soyayya bare shaquwa a tsakaninsu kowa so yake yaga kasawar dan uwansa yanzu idan baka sani ba wlh ba zaka taba yarda MD Oil and Gas da AG ubansu daya ba dan ko barene beci yayi masa irin wannan tozarcin ba ballantana jininsa."
Dayar tace
"Uhm kedai bari Halisa kinsan su CMD yayan Mowa ne shiyasa suke sharafinsu, bandama AG da MD Agric wa kika gani a yayan nasa yana aiki a nan se yayan yan uwa dana abokanai ragowar kina kallo duk wanda yazo baya zama yake neman hanyar da zata bulle dashi to ko nice wlh ba zan zauna ba Arziqin ubana amma a fifita wasu su zasu amfana ai dai idan Chairman ya sheqa be gyara kan gidansa ba to kuwa kwanciyarsa qalilan ce a kabari dan kullum se an tashe shi yaga tsiyar daya bari a duniya da ransa ma ji yanda suke akan dukiyar inaga an raba gado wani be samu yanda yake tsammani ba" suka tafa hannu suna cewa
"Allah dai ya kyauta.

Alhaji Audu ya daga qafa dakyar ya qarasa ficewa daga gurin bayan ya gama sauraron hirar tasu.

Tunanin maganganunsu yakeyi a ransa, ba yau aka fara fada ba ko ya faraji wasu su fada masa akan idonsa wasu a boye suti gulma kamar dai wadannan kuma tun abin baya damunsa yana daukar sa ba a komai ba har ta kawo matsayin da shida kansa ya hangi illar da yayiwa kansa da rayuwar Ahalinsa gaba daya.

A lokacin daya dora tubalin ginin sam be hango rashin ingancinsa ba, be hasaso ranar da ze iya ruftawa dashi ba seda lokaci ya qure masa akazo matakin da ko yana so ya gyara mawuyaci ne hakan ta yuwu.

A yanzu da yake cikin Shekara ta Saba'in da uku a duniya yaci ace yana kwance a gida yana hutawa da kuma shirye shiryen tarar da ubangijinsa ta hanyar yawaita tuba da ayyukan Alkhairi amma a maimakon haka tashin hankulan da be san suna wanzuwa ba a baya yanzu suke riskarshi.

Bashida kwanciyar hankali a gidansa, tsakanin Matansa koda ace ba dukka kullum ta Allah idan ba safiya ba rana idan ba rana ba Dare se Binta ta tayar da tashin hankalin da ze kwana ya wuni cikin quncin zuciya.

Ubangiji yayi masa ni'ima ta Yaya Maza zarata wadanda ya dora buruka da yawa a kansu sedai be gino rayuwar ta sigar da baze cimma mafarkin sa ba ya shuka barna yanzun kuma yana girbinta ne, yayan daya kwallafa rai akan zasu taimake shi a lokacin da qarfinsa ya tashi qarewa sedai sam hakan ta gagara a maimakon nutsuwa a kullum tukuicin tashin hankali yake samu daga garesu wanda shine silar komai ya sani ba laifinsu bane laifukansa na bayane suke farautarsa a yanzun.

Yayi zurfi cikin tunani har besan sun isa gida ba seda Dtiver sa ya bude ma murfin qofar bangaren da yake.

Ya fita ya tsaya yana qarewa Tamfatsetsiyar harabar gidansa kallo ga motoci nan birjik kamar a gurin saida su.

Gida ne daya amsa sunan gida wanda ko baka shiga ciki ba zaka iya wassafa tsaruwarsa, Get din gidan me kama da qofar Gari kansa abin kallo ne ga wasu shuke shuke da akayi a harabar na dogaye da gajerun bishiyoyi da suka qara qawata gurin se manya manyan Street Light jere da Zanqaleliyar Katangar gidan kamar ta mutanen Niger kana gani base an fada maka ba kasan idan dare yayi haske har yawa yakeyiwa Harabar.

Gini ne Duplex a tsakiya yana kallo ka idan ka shigo nan ne kuma turakar Alhajin dakuna uku ne a sama da falo a qasan kuma kantamemen falo ne da aka zubawa kujeru saiti uku da bandakin baqi a gefe se kuma wani qarami Daga can gefen wanda fadar tsaruwarsa bata baki ne a nan Alhajin yake saukar baqinsa na Mutunchi Babban Falon kuma na Meeting ne tsaf yake dauke jama'ar gidan duk yawansu.

A cikin harar akwai qofofi biyu dama da Hagu, ta hagun ce zata kaika cikin gida inda bangaren Matansa yake ta Dama kuma ta kasu biyu, daya ta inda dakunan samarin gidan yake ne dayar kuma dakunan masu aiki maza. daidai qofar da zata shiga dakai sashin samarin gidan ya hango Faisal yana tahowa da wasu kwaftara kwaftaran takalma a hannu irin na taqadiran Black Americans din nan yana waigen bayansa, baya tsammanin ma ya lura da tsayuwarsa ya giftashi yana cewa
"Dan kutumar uba da ka biyo ni mana da wallahi sena farke ka a gidan nan" ya fice abunsa ya bar Alhaji da zuciyarsa take tsalle da lugude, dawa Faisal yake fada da har yake furta wadannan munanan kalamai wai ze farke shi kamar wani Dan Daba?

Salim daya fito daga qofar shima kamar an harboshi yana kwalawa Issa daya daga cikin Buzayen fa suke gadin gidan kira ya taho da gudu ya durqusa cikin maganarsa ta buzaye yace
"Gani Alhajji me kuke da buqata?"
"Ina Faisal?" Ya fada a fusace, Issa ya daga hannaye sama yana cewa
"Ya fita Alhajji yanzun ya fice ta qofa"
"Zonan Salim" Alhaji Audu ya fada ganin shima be lura da tsayuwarsa a gurin ba.
Chapter 2 · 0% Book details