← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 91

Sashe 6

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bari ma kaji wannan rabon da kaga an baku dan dai Goggo ta saka baki ne amma da mu bamuyi niyyar baku kamar hakan ba saboda babu guminku ciki mu muka sha wahala muka noma abinci dan haka daga yanzu in har kuna son kuci abinda aka noma cikin gonar nan to sedai ku shiga ayi daku" Hashimu ya fada, Audu ya kalle shi kafin ya miqe yana cewa
"Amma dai muna da gado a cikin gonar ko?"
"Su kuma ai ba bayin ubanka bane da zasu sha wahala su noma kuna zaune su baku kuci" Goggo Fadi da se yanzun ta saka musu baki ta fada wannan ya tabbatar masa da cewar shawararsu daya dan haka ya fice yana cewa
"Ai kuwa in har haka kuka zaba sedai a raba gonar idan yaso se na gani in abinda kuka samu ze isheku ku noma abincin shekarar".

Goggo Fadi ta hau tafa hannu tana salallami wai yazo har daki ya qare musu tanadi.

Audu kuwa yana fita dakin da suke kwana ya shige zuciyarsa na tafarfasa dan yasan idan ya koma dakin Dada ma fada zatayi masa ta bashi rashin gaskiya amma ya qudure a ransa kome za'ayi sedai ayi tunda ta haka suka zaba to su zuba su gani su waye zasu sha wahala.

Kenan ita Goggo Fadi luf luf tayi musu sanda Malam na raye suke zaune lafiya da Dada shine yanzu daga mutuwarsa ko kwana sittin be cika ba fitina zata fara bullowa daga barayinta.

Idan taqamarsu su suke noma gona ai su kuma suna da kaso a cikin qasar ya zama tamkar sun basu aro ne suna biyansu shikenan tunda dai basu hango wannan maslahar ba to za'ayita yanda suke so dan idan rigima ce kowa ya sani kaf karkarar bashida mahadi.

Tun yana dan mitsitsi fada ne dashi kamar dage babu randa baz fita wasa ba tareda an kawowa Dada ko Baffa qarar ya daki wani ba shiyasa ma ya dena wasa da sa'anninsa ya shiga cikin su Yakubu amma ko su din idan kaga yanda yake a cikinsu seka dauka ya girme su kura ce tayi lafiya kuma tunda aka tabota kowa ze dandani kudarsa.

Yana kwance yana saqa da warwarar ta inda ze bullowa al'amarin, yanzu idan ya koma Birni Yakubu ya koma makaranta kenan zaman gidan in ba'ayi wasa ba gagarar Dada zeyi to kuwa baze taba barin haka ta faru ba.

Yakubu ya shiga dakin rai a hade yace ya tashi su kwashe kayancan amma ko gezau Audu beyi ba, daya isheshi da magana yace
"Ka qyaleni baza'a kwashe ba se gobe tayi an sake Rabo sannan su kwashe nasu daga Rumbu tunda ai ba rabonsu bane ba"
"Audu kasan me kake so ka taso kuwa?" Yakubu ya fada yana zama a gefen qafafunsa Audu ya wuntsila ya tashi zaune yace
"Na sani, naje na same su sunce tunda bamu noma ba dan haka iyakar abinda zasu bamu kenan kuna daga yanzun ma muddin muna son Abinci sedai mu shiga ayi Noma damu"
"To ai gaskiya suka fada, shiyasa nace maka bazan koma makaranta ba na haqura da karatun zan zauna na kula da Dada dasu Aisha kai kuma ka shirya ka koma Birni kaci gaba da Buga bugar ka" Yakubu ya fada cikin sanyinsa, Audu ya galla masa harara tsabar takaici daya rasa me zece masa kawai yayi tsaki ya koma ya kwanta.

Haka Yakubu ya gaji da masa maganar ya tashi su kwashe kayan qarshe se Aminu daya shigo gidan ne ya taimaka masa suka kwashe, shima seda ya tambayi Yakubun kayan menene wannan yayi shiru bece masa komai ba.

Daya shiga gurin Goggo Fadi lokacin su Hashimu sun tafi gidajensu ya sake tambayarta nan ta wassafa masa qarya da gaskiya akan Audu, Aminu yayi shiru kafin ya kalli Mahaifiyar tasa yace
"Amma zancen gaskiya wannan ba Adalci bane Goggo, wannan hatsin da ake magana fa Malam ne ya noma shi a gonar sa mu duk mun tayashi aiki ne a matsayinmu na yayansa, kinga kenan duk wani Magajinsa yana da rabo daidai da kowa a ciki koda kuwa Jinjirine yau aka haife shi.

Sannan maganar kuce idan basuyi Noma ba baza'a basu abinci ba bata taso ba saboda yau idan sukace a raba gonar nan kun sani Kason da zamu samu baze isa mu ringa noma abinda ze riqe mu ba, kuma ko cewa sukayi mu ringa haya muna biyansu bamu da abinda zamu basu.

Nidai a ganina ayi maslaha koda kuna ganin ba za'a ringa raba daidai ba tunda mun fisu yawan Ahali a ringa fitar musu da abinda ze ishe su har su saida suyi sauran buqatu hakan duk taimakon kaine".

Goggo Fadi tayi kasaqe tana kallonsa kafin tace
"Babu shakka Aminu wato Hafsatu da Yayanta sun fimu a gurinka kenan ko?"
"Ba abinda nake nufi kenan ba Goggo, ni wlh kece ma kike bani mamaki gaba daya kin biyewa Yaya Hashimu yana doraku akan wata hanya ta daban dan Yaya Baba ma babu ruwansa sedai idan yanzu shima ya dauki hudubar tasa, har Malam yaja numfashin qarshe yana mana nasiha da mu hada kanmu kar mu bari baraka ta shiga tsakaninmu me yasa kuka zauna tsayin shekaru lafiya dasu se yanzu daya mutu sanda yafi buqatar mu hada kai mu cigaba da yi masa addu'a sanann ne kuma fitina da rabuwar kai zata bullo?

Kowa ya sani Dada bata da matsala kuma kome zakuyi ba zata daga kai ta kalle ku ba amma ai mutum ya kamata yasan daidai ba se an tunatar dashi ba ina amfani cikin danne haqqin wani wannan abun fa magana ake ta dukiyar marayu da wanda ya cinye kudi da kadarori daku da kuke shirin cin kwayoyin hatsi a gurin Allah baku da banbanci Goggo, nidai shawarata tun wuri ku farga karku bari shaidan yayi tasiri a zukatanku.

Yanzu an fara rigima akan Gona gobe kuma se ace za'a raba gida shikenan zumunchin da Malam yake ta mana takarar mu riqeshi kinyi sanadin murqusheshi"
"Nice ma zan raba muku zumunchin?" Goggo Fadi da jikinta yayi sanyi da maganganun Aminun ta fada, ya miqe yana cewa
"Eh mana saboda duk fitinar da su Yaya Hashimu zasu zo da ita idan kika tsawatar musu dole su bari amma idan kika basu goyon baya kinga gaba zasu qarayi" daga nan ya fice ya wuce can dakinsu inda suke kwana dasu Audu.

Tun Asuba da suka fita masallaci Audu be dawo ba kaitsaye qofar gidan Liman ya tafi ya jirashi yana zuwa kuwa ya zayyane masa abinda ya faru dan ya rantse baze bar maganar ba, shirye shiryen komawa Birni yakeyi tayaya hankalinsa ze kwanta a can Alhalin an fara irin haka ga Yakubu yana maganar ze haqura da mafarkinsa saboda ya zauna ya kula da mahaifiyarsu shi kuma baze yarda ba shiyasa zeyi iyakar qoqarinsa yaga komai ya daidaita sannan su rankaya su koma Kano dan yayi rantsuwa muddin yana numfashi seya cikawa Yakubu burinsa na zama Alqali.

Liman ya gama jin bayaninsa yace yaje ze samu me gari daga nan za'a kira duka yan uwan nasa su zauna haka akayi kafin yamma duk an kai musu sammaci bayan sallar isha'i suka hallara gaban me gari Hashimu se muzurai yakeyi Baba dai fuskarsa kadaran kada han.

Liman yace Audu ya maimaita abinda ya faru tsaf ya sake rattabo musu Yakubu se faman harararsa yakeyi aka tambayi su Hashimu sukace haka ne daga nan Liman ya fara musu shari'a ya karanto musu abinda Shari'a ta tanada akan rabon gado, koda ace wani da Guda daya shine kan ragamar juya dukiyar Ahali gaba daya, muddin dai wannan dukiya mallakin mahaifinsu ce duk randa ya mutu hatta da Jinjiri idan ya bari yana da gado a ciki, babu zancen kai kasha wahala ka tara dukiya tunda dai ba taka bace to ta kowace gaba daya.

Liman yace gobe za'aje a fito da Hatsi gaba daya a rabawa kowa nasa idan yaso se su sake hadewa su ajiye duk inda suka ga dama.

Hashimu zeyi magana Baba ya hanashi, haka aka tashi rayuka babu dadi washe gari kuwa Liman da wakilan me gari sukaje aka sake rabon Hatsi dukda cewar a cikin daren Hashimu yasa an kwashe fiye da rabi an kai gidansa ya boye a hakan seda aka fiddo da huhunhuna hamsin da biyar, aka hada dana gurinsu Audu shida ya zama sittin da daya nan aka raba musu kowanne bangare suka tashi da Talatin, guda dayan kuma aka bawa masu rabo ladan aikinsu wanda ba shari'a ce tace a bayar ba tsabar son zuciya ya saka su karba.

Cikin zafin rai Hashimu yace
"Toh tunda anyi haka se a fadi yanda za'a cigaba da kasafin Abincin dan wlh babu yanda za'ayi musha wahala muyi noma suna zaune mu ringa raba komai daidai dasu.

Audu yayi tsugul yace a raba Gona kowa ya dauki kasonsa.

Yakubu ya zabga masa harara yana cewa
"Idan an raba kai zauna ka nomata?"
"Se mu bada haya, idan kuma su zasu karba ma bismilla ayi qiyasin abinda zasu ringa biyan mu duk shekara" Audu ya sake fada.

Dada dai ta rasa abin cewa dan duk bata san tsiyar da aka qullo ba seda aka zo rabon abincin kiran da aka musu jiya da suka dawo babu wanda ya fada mata inda sukaje.

Haka dai aka tashi a matsayar zasu bar musu barin gonarsu suci gaba da nomawa, ladansu duk shekara abinda aka samu za'a raba uku, su dauki biyu su basu kaso daya matsayin ladan hayar gona kowa yayi na'am da hakan dukda zuciyar Hashimu da Sama'ila Mijin Amina dan karere sunyi wani qullinsu na daban.

Audu be koma Kano ba seda suka tabbatar sun saita komai, sun siyarda wani kaso na abincin suka barwa Dada kudin a hannunta saboda laluran yau da kullum kafin ya tasa Yakubu a gaba kamar shine qanin suka koma lokacin tuni zangon karatu yayi nisa har ana shirin jarabawa dakyar aka karbeshi yaci gaba.
Chapter 6 · 0% Book details