← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 91

Sashe 43

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jallabiya ya saka ya sakko yana mamakin Ina Binta ta shiga ake irin wannan dukan qofar bataji ba ko itace ta fita qofar ta kulle ta waje.

Takaici ya qumeshi ganin Lantana me aiki, ya tsani matar saboda kana ganinta kalar munafukai ne da ita.

Ta durqushe a qasa kamar zata kwanta tana gaishe shi ya amsa a dake yana cewa
"Wane irin abu ne haka zakizo kina dukan qofar mutane"
"Kayi haquri yallabai kasan dokar Hajiya qarfe bakwai nake zuwa gidan nan to Nazo tun bakwan na buga ba'a bude ba na tafi shine na dawo na sake bayi bugun da qarfi ne ko bacci take kar nayi laifi tace banzo da wuri ba"
Tsaki yayi ya juya ciki, harya fara hawa sama ya dawo jin tanata qwanqwasa qofar Bintan shiru ba'a bude ba, ta matsa ya isa jikin qofar ya kwankwasa kana ya murda handle din qofar.

Fahimta da yayi a kulle take yasa ya zagaya ta window ta da yake a tsakar gidan ya zuge ya leqa ciki, kayana da ya gani barbaje suka fahimtar dashi bata nan, se abin ma ya bashi dariya a fili yace
"Yaji tayi kenan"
"Ki tafi na manta zataje zata fita yau ta fita da wuri ina bacci" ya fadawa Lantana, kamar zata fasa kuka haka ta ja qafa tana waiwayensa, kamar tace masa zata zauna ta jira tunda ko fita Bintan zata yi tana barinta tayi mata jiran gida gashi ta kwaso yunwar safe ta saka rai zatazo taci me kyau kuma ace bata nan.

"Alhaji Mairo tazo ne?

Kuma zuwa yaushe Hajiyar zata dawo?" Ta fada tana sunkuyar da kai,
"Idan ta dawo zata saka a kiraki ba yau ba ba gobe ba, kija qofar ki tabbatar kuma ta rufu idan kin fita" ya bata amsa yana juyawa tilas ta fita taja musu qofar gidan.

Audu kuwa kasa komawa bacci yayi, tunanin inda Binta ta tafi ya shigayi, qila ba zata wuce gidan Baturiya ba dan bata da yar uwa a Kano bare yace gurinsu zataje Baturiyar itace yanzu babbar Qawarta ko yace Aminiya indai ba gidanta taje ba to Kaduna ta tafi.

Zabura yayi ya miqe yana salati, idan Kaduna ta tafi ya Alhaji zero dauki maganar?

Ze goyi bayansa ko kuma ze goyi bayan yarsa ne?

Idan Alhaji ya goyi bayan Binta yace ya sakar masa yarsa ya makomarsa zata zama kenan dan dai Alhajin shine abin tunqahonsa, duk abinda yake ganin ya tasarma zama da bazar Alhajin yake rawa.

A gurguje yayi wanka ya shirya, kai tsaye gidan Ali ya fara zuwa suka hade a waje Alin na shirin fita ya kuma tabbatar masa Binta bataje gidan ba dan babu inda zata buya da ze kasa ganinta.

"Dan girman Allah kazo ka rakani Kaduna" ya roqi Alin
"Kai yanzu?

Ina babu wannan magana, ai yanda ka tirko rigimarka se ka san ta yanda zaka kasheta.

Amma fa ban taba dauka da gaske kaci kai ba Audu se yanzu, duk matan da suke garin nan yayan mutunchi ka rasa wadda ta burgeka se wannan yarinyar?

Kodai Asirinsu tayi amfani dashi ta zarge zuciyarka?" Ali ya fada yana tsareshi da ido.

Audu yaja tsaki kafin ya shige mota ya daga ba tare da ya bashi amsa ba
Yau dinma Musbahu yaje ya dauka suka tafi Kaduna, seda ya isa qofar gidan kuma ya fara tunanin me zece musu idan ya shiga?

Seda sukayi sallar La'asar da Magriba da suka riskesu a hanya kafin ya saka kai cikin gidan.

Ko ina tarwai da haske, Tun daga Get suka fara gaisawa da ma'aikatan gidan harya isa qofar falo.

Ta ciki Munira ta hangoshi, ta kwasa da gudu tayi daki ta fadawa Binta da tunda tayi wanka taci abinci take rama baccin da batayi jiya ba.

"Wlh ko me za'ayi karki koma ai raini nema kamar ke ace a miki kishiya bayan duk fafutukar da daukar hakkin da mukayi muka fitar da waccen shine za'a dakko miki alaqaqai to babu wannan maganar" Muniran ta qara zugata.

Tun daga yanda Alhaji ya amsa masa gaisuwarsa yaji guiwoyinsa sun qarayin sanyi dama Mama tana musu iso a tsayw suka gaisa ta shige ciki, yau ko Kayan Alatun da ake tarbarshi dasu be samu ba Ruwa da Lemo ma Alhajin ne yayi magana aka kawo musu.

"Bansan ta taho ba Alhaji, na dawo daga sallar Asuba kawai na tarar bata nan" Audu ya fada bayan dogon shirun da sukayi kowanne kamar ya rasa abin fada.

Alhaji ya nisa yana kallonsa yace
"Me ya hadaku da har yasa ta baro gidan ba tareda saninka ba?".

Be boye masa komai ba ya bashi labarin Auran da yayi wanda yake ganin shiya tunzurata ta baro gidan, ya rufe da qaryar cewa
"Bansan cewa zasu daura Auran ba saboda tambaya kawai akaje".

Shiru Alhaji ya sakeyi yana kallonsa kafin yace
"Menene gaskiyar maganara data fada na cewar Yarinyar Karuwa ce?" Seda ya daga kai ya kalli Alhajin saboda kalmar daya fada din se yaga kamar tayi girma musamman ana maganar matarsa ne ina laifin yace tsohuwa, wannan ya tunzuro zuciyarsa ta raya masa ci masa mutunchi Alhajin ya tashi yi amma ya danne dan ko ya masa qarya bashida amfani tunda har magana ta fito amma a ina Binta taji wannan batun?

"Kayi shiru" Alhaji ya katseshi, kansa na qasa yace
"Gaskiya ne, amma ban aureta ba seda na maidata gaban iyayenta tayi Istibra'i kamar yanda shari'a ta tanadar"
"To akan me ka daki Mamana har kaji mata ciwuka a jiki?" Alhajin ya fadi ainihin abinda yafi damunsa a duk cikin maganar, se Audu ya daga kai da sauri ya kalleshi jin abinda ya fada.

"Wlh Mari daya nayi mata, shima kuma cin kwalata tayi a gaban yan uwana da sukazo fadamun an daura aure ta labe harta tsinci maganar shine ta shaqemun wuya nace ta sakeni taqi ni kuma zuciya tasa na mareta bayan nan ko yatsa ban nuna mata ba wlh" ya fada cikin kare kai.

Alhaji bece komai ba yaja Intercom ya kira cikin gida kan Binta tazo, ba'a dauki lokaci ba ta fito tana jan qafa fuskar nan kamar dafaffen Kunu ta zauna kusada qafar Alhajin tana hararar Audu wanda ke kallonta yana mamakin abinda ya karceta a fuska kamar sunyi dambe da Mage.

Ce mata yayi ta maimaita duk abinda ta fada cewar Audu ya mata, tana kuka ta shiga shiryosu harma da abinda dazun bata fada ba na cewar daman Audun ya dade yana yawon ta zubar dinsa har kwanaki yake tafiya yayi acan in ya dawo kuma tayi magana ya zageta koya hada mata da duka qarshema tace idan ta fita har gidan yake kawo mata shidai kasa cewa komai yayi saboda mamaki, maganganunta kuma babu yanda za'ayi ace qarya takeyi tunda tabbas yana yawace yawaceb har yaje ya kwanan amma ai ba abinda take fada yakeyi ba sedai kuma waye ze bada shaidar hakan?

Shidai Alhaji na jinta yana kuma kallon Audu daya kasa rufe bakinsa seda tayi shiru kafin ya kalleta yace
"Kinaji ko Mamana, duk wani Aure da kika gani tattare yake da qalubale muddin kuma ba ma'aurata sun bude cikinsu ba bazaka taba sani ba dan haka kowa haquri yakeyi kamar yanda kika faro haqurin kici gaba dayi kuma tunda ya auro yarinyar da take dauke masa hankali a wajen ai magana ta qare se ayi fatan kuma Allah ya hada kanku ya bada zaman lafiya.

Kaikuma abinda nake so na gaya maka shine ka tabbatar kayi na farko kuma kayi na qarshe da zaka dora hannu da sunan duka a jikin Mamana, zan manta da duk wata alaqa dake tsakaninmu na maka ka a Kotu domin bana hada kowa da yayana, ban daki yar kowa ba dan haka babu hujjar da zata saka wani ya dakar mun yata.

Idan tayi maka laifin da ba zau iya sasantawa a tsakaninku ba ka kawo mun qararta nizan hukuntata amma bazan lamunchi duka ba ina fatan ka gane?"
Kunya, nauyi da takaici suka rufe Audu gaba daya ya rasa ma abinda zeyi, Alhaji yaci gaba da cewa
"Idan Allah ya kaimu gobe yanda kikazo da sassafen nan ki tattara ku koma aje aci gaba da haquri kuma na kashe maganar nan, Aure kuma dakayi Allah ya sanya Alkhairi ya baka ladan Jihadi"
"Wlh bazan koma ba, babu yanda za'ayi nayi zamab kishi da Karuwa Dady kawai kace masa ya saketa idan ba haka ba bazan koma gidan ba" ta fada cikin kuka tana bubbuga qafa.https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE17*
Badan Audu yaso ba sedan Yaya Baba dayace muddin ba sanarwa da Yakubu ba bazasuje masa neman Aure ba tilas ya kirashi ta wayar Landilayin wadda ya hada a gidansa shima kuma Yakubun suna da ita a Ofishin da yake aiki dan haka ya kirashi.

"Allah ya sanya Alkhairi yasa ayi a sa'a" abinda Yakubun ya fada masa kenan bayan daya shaida masa zancen Auran se kuma yaji babu dadi dan haka yace masa
"Amma zaka zo ko?
Chapter 43 · 0% Book details