Sashe 53
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallarta dai da kyau kiga dawa tayi miki kama?"
Ta zuba mata ido tana so ta gano wacece din kamar yanda ya ce, tai fici fici da ido se ko ta zabura sanda ta gama ganota ta nunata tana cewa
"Ke..meye wannan?
Me zan gani haka?"
Yanda tayin ba Zubaida ba hatta Audu seda ya bushe da dariya yanda kasan wadda taga wata fatalwa haka rikice tana jera mata tambaya yace mata
"Kinga abin mamaki ko?
Yanda kika san cikin nan na jira ki tafi ya fara girma qila da baki dawo yanzu bama sedai kizo ki tarar ta haifeshi"
"Au Namiji ma zata haifa?" Maganar ta subucewa Bintan, Zubaida ta kalleta Audu da be gane inda maganarta ma ta dosa ba yace
"Yan tagwaye ma kuwa muke tsammata dan wannan cikin daga ke har Bara'atun ban taba ganin wadda tayi me girmansa ba" ya furta sunan Bara'atu a fili karo na farko tun bayan rabuwarsu da ita.
"Zancen banza ma kenan, ita zata haifi yan tagwayen a gidan nan?
Wlh baze yuwu ba" ta idasa kwancw qullin haukarta.
Zubaida ta gyara zama ganin cin kan Bintan gaba yakeyi tace
"Yaya ina wuni?
Ya aka baro yan gida?
Ya me jiki kuma?
Ubangiji ya qara afuwa yasa kaffara ne" daga nan ta shiga yunqurin miqewa tsaye tana jin Bintan dake kallon Audu tace
"Lallai ma wannan rainin wayo ne qarara kuma wlh bazan dauka ba, ni za'a mayar mahaukaciya cikin da be ko cika qata hudu bane zeyi wannan girman sannan saboda jaka ce ta raineni na yarda ai kuwa ba'a isa ba"
Zubaida bata tsaya sauraronta ba ta wuce dan dai kamar maganar bata shafeta ba haukanta da bata gajiya dashi ne ya motsa ga Mijinta nan seta sauke shi a kansa amma ba ita ba ciki kuma dai ba mutum ke bayarwa ba balle tace zatayi fito na fito da wanda ya bata dan haka tana zuwa daki taci abinci tasha saiwoyin data jiqa jiya dataje gida Baba Zayya Amaryar da Malam Hassan Babanta yayi watanni biyu kenan ta hado mata saiwoyi wai na taimakon sauqin naquda ne da rage zaqi a yanda Baba Zayyan tace wai cikinta ya nuna alamun ta kusa haihuwa ta ringa dariya tana cewa Baba Zayyan kace a kanta za'a fara haihuwar hudunni kenan ita kuma tace mata to su daura tsakanin su za'a me gaskiya dan bata yarda da lissafin Asibiti ba ko makaho yaga cikin Zubaida yasan ya haura zuwa watanni bakwai ko takwas.
"Idan kika lissafa watanninki a daki ai cikinki ya kusa isa haihu ina watan Sallar Tsofaffi akayi Bikin wata na takwas fa kike ciki yanzu ai dab kike da ki haihu" Baba Zayya ta nanata mata.
Ita dai bata dauki batun da muhimmanci ba, wata hudun nan shi take lissafawa kanta dukda girman cikin da motsin da takeji abin dubawane, ba wannan ne cikinta na farko ba ciki biyu tayi a rayuwarta ta baya sedai dukkansu baau kai matakin da aka busa musu rai ba ta ciresu dan haka ba zata dorar da komai game da yanayin girma ko sanda yake fara motsi ba.
Ta dafe cikin da hannu biyu tana jin wani yanayin nadama mara misaltuwa yana shigarta.
Yanzu fa Al'umma zasu iya ringa jifan abinda zata haifa da rayuwarta ta baya ko?
Washe gari Audu na fita Binta ta fice itama, daren jiyan basu kwashe shi qalau ba, Bintan da tayar da bala'i babu rufa rufa tace Audu ya raina mata wayau, watau ciki yayiwa Zubaida a waje can gurin tambadarsu shine ya aurota dan su rufawa kansu Asiri kenan ko to billahillazi ba zata yarda ba seta bankada kowa yaji wannan aika aikar da sukayi baze gurbata musu zuri'a ya hada yayansu da yan uba Shegu ba ta ringa masifa tana bala'i seda ya zabga mata mari ya korata dakinta kafin ya samu sa'ida hayagagar da take masa akai da safe kuwa ko leqata beyi ba dan tayi bala'in bata masa rai akan maganar tata Zubaidan kanta daga bakin qofa suka gaisa ya fita shine Bintan najin fitarsa daman ta shirya itama ta tafi gidan Turai.
"Yanzu ke meye abin daga hankali a nan yanzu?
Wannan ai abinda zaki koma gefe kiyi dariya kisha kallo ne idan ma da cikin ta shigo ke ai gaba ta kaiki dan magana na fita dayan biyu ne dole ya sawwaqe mata ta tafi ta nemi uban cikinta idan ma nasa ne dai ta saku tunda dai ba'a Aure da ciki to ai gaba ta kaiki gobarar Titi a Jos Qawata" Turai ta fada bayan da taji bayanin Binta.
Ta numfasa tace
"Zancenki gaskiya ne amma ta yaya kike tsammanin haka zata faru?
La shakka idan cikin ba nasa bane wannan kuwa na san ze iya sakinta amma muddin na sane kema kinsa babu inda zataje kuma zama sunyi auran ne daman saboda kauda idon mutane da kuma zargi"
"Banyi muku katsalandan ba Hajiya amma watan auran nan da kuke magana akai nawane tukunna?" Barira me Aikin Turai dake ta goge goge hankalinta na kan hirar su Bintan ta fada.
Turai ta harareta tace
"Wai sau nawa zan hanaki tsoma mun baki idan ina magana da mutane?
Aiki kikeyi dama ko kuwa zaman gulma shiyasa kika maqalw gaban Tv tun dazu kin kasa gama gogewa kenan?"
"Kiyi haquri hajiya ba gulma bace ba maganar gaskiya ce wanda a ganina duk abinda zaku shirya dole ya zamani kunyi akan saitin da ba za'a ruguzaku ba.
Akwai hanya me sauqi da zakubi ku heganta cikin nan kona Alhajin ne tunda dai an samu tangardar lissafi girman ciki ya zarta watanninsa" Barira ta sake fada bayan ta saki duster da take goge goge da ita ta juya ga abinda tafi iaywa wato hada tuggu da munafunci, abinda ya kaso mata aure kenan kuma ya korota daga qauyensu saboda an mata tambari duk wata Masifa data taso tsakanin kishiya da kishiya a garin In sha Allahu se kaji sunan Barira a ciki ita ta qullota kuma lafiya lau take zaune da nata Mijin tsabar yanda kawa qara da zuwa shari'a gaban me gari akanta yaqi qarewa yasa ya sallameta shine wata qawarta da ta fito Aikatau Birni ta janyota itama suka taho a gidansu Turai waccen take aiki dan haka da sukazo ita kuma tata me aikin sannan ta tafi gida se Mamarsu tace ta dauki Bariran dukda bata so ba dan bata son me aiki babba kodan irin Mazansu ido a mata amma ganin ta iya aiki kuma dai ta ganta kalar gidadawa kamar ba zata yarda da irin wannan abin ba yasa ta karbeta kuma se take jin dadin zama da ita dan Barira badai ladabi da duk cikin iya takunta.
Bi ta da Turai suka shiru sunasauraronta ita kuma ganin sun bata hankali yasa taci gaba da cewa
"Ina itace naji kunce tsohuwar kilaki?" Turai ta gyada kai alamar haka ne, Barira ta gyara zama tana buga cinya tace
"Yo Allah na tuba kwace goruba a hannun kuturu ai shiyafi komai sauqi, ai kamar yanda Hajiya tace miki ki koma gefe kihya kallo to haka zakiyi amma kafin nan se kin basa bam din da ze tayar da kowa, abu daya zafi fada da ze maida Alhaji hayyacinsa in ma cikinsa ne in ma ba nasa bane kawai kice masa kin gano da cikin ta shigo, zuwa sukayi aka kwantar dashi se yanzu da suke ganin ta dan kwana biyu aka tashe shi kina fada masa hala kija gefe kiyi zamanki kawai ki saka ido, in cikinsa nema zaki gane idan ma na wani ne kin haska masa hanya duk ma yanda akayi ze binciko"
"Amma Barira kanki yana kawo haske, to tsaya dagaske ana kwantar da cikin kar kuma mu fadi abinda ba haka ba" Turai ta fada tana jinjina tunani irin na Barira.
Barirar ta sake washe baki tace
"Kai Hajiya yo wannan har wani abun mamakine ko a nan cikin Binni ai anayi.
Mu a karkarar mu kihiya tanawa kihiyarta asiri a kwantar mata da ciki se kiga Mace ta hekara goma da ciki ayita cewa Aljanune nan ba asan Asiri aka mata ya kwanta ba in ta dage da neman magani se kiga ya tahi an haife dan to haka idan Yara suka dakko abin kunya hima zuwa ake a kwantar hi se an kwana biyu a daki lissafi yayi daidai se tayar dahi kiga yarinya ta haihu qalau babu me cewa komai"
"To amma ai ita watanta takwas yanzu fa" Binta ta fada bayan data gama hada lissafi akanta.
Barira ta sake sheqewa da dariya irinta shegun qauye tace
"Kai Hajiya yane muke ta maimaita magana amma kamar baku ganewa.
Dama ai kintatar lokaci akeyi se a daga cikin kinga in ta haihu nan da sati ko biyu ne ai babu me cewa komai tunda ta shiga wata na tara a daki to amma idan kika bullo da wannan maganar ko shekara tayi kanta haihu kin saka kokwanto a zukatan jama'a musamman da daman tana da tambari sannan shi kansa me gidan kinga lissafin da yakeyi na cikin ai be kai asalin watannin qiyasin girmansa ba ko?"
https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 21*
Rai fes Binta ta koma gidase da tayiwa Barira kautar Naira Dari biyu tukuici.
Ita kadai ta ringa sakin murmushi a hanya harta koma gida nan ta tarar da Lantana rabe qofar daki tana jiranta.
"Ai nazo tuntuni ashe kin fita, Mairo ma tazo ta tafi kin santa ita ba zata iya jira ba" Lantanar ta fada bayan data karni muqullin daki ta bude mata.