Sashe 69
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har akayi sallar Magriba babu Binta babu Audu, bayan tayi sallah ta gyara kwalliyarta, babu laifi ta qara jiki akan shekarun baya da take gidan dukda ba qiba tayi ta azo a gani ba amma ta murje, yanayin ta dai na Shiru shiru da sanyin jiki yana nan wanda halittace canzashi da kamar wuya, a bangaren wayo ko ace wayewar kai ma babu wani cigaban Azo a gani data samu domin shekaru kusan hudun a Bechi tayi su ta sake komawa duhun kan data baro, mutanen da taci gaba da mu'amala dasu sune dai wanda ta sani tun yarintarta babu wani sabon Ilimi ko wayo data qaro ita ba Makarantar Boko ta shiga ba balle Islamiyya kullum tana zaune a gida kwalliya kanta ba yi takeyi ba Hadiza ce tayi qoqarin ganin ta saitata tayi gyara ciki da waje a dan taqin kwanakin da aka saka na tariyar tata, ita da yake yanzu a cikin Kumbotso take aure babu laifi kanta ya waye fiye da Bara'atun dukda daman tun Asali ba zubinsu daya ba dan da ace Hadiza ce ta samu damarda Bara'atu ta samu ta auran Audu tabbas ba Binta ba kowacce Macece zata iya karawa da ita.
Seda aka fara kiraye kirayen sallar Isha'i taji motsin an shigo gidan, ta taga taga wucewar Bintan,gabanta ya yanke ya fadi har seda ta dafe ta shiga karanto Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, fargaba da razanin da ta ke shiga duk sanda ta ganta a baya irinsa takeji a yanzu ta rigada ta tsorata da Bintan Allahya sani.
Tana cikin wannan halin aka sake shigowa wannan karon Audu ne shida Musbahu.
Faduwar gabanta ta ninku tana jiyoshi suna magana dan bata iya leqawa ma ta ganshi ba harya sallami Musbahun taji alamun tafiyarsa yayi can gurin Binta kafin ta iya sauke numfashi.
Tana cikin sallar isha ya shiga dakin, ganin tana sallar yasa ya fita bayan ya fada mata sallahun ta sameshi a falon Bi ta idan ta idar haka ta ringa taraddadin taje ko kar taje bayandata idar da dallar daga qarshe dole ta miqe, babu wani sauran magana ta rigada ta dawo cikin gidan nan abu biyu ne kodai ta tashi ta kwatarwa kanta yanci ko kuma rayuwarta ta qare cikin tsoro da firgicin Miji da kishiya.
Tana tafe sallaf salaf a ranta tana kewar Balaraba, qila basu san ma an mayar da Auran nasu ba tasan da tana nan data qara mata qarfin guiwa dan duk sanda sukaje Bechi idan taje gurinta maganar kenan take mata ta tashi ta kwatarwa kanta yanci wannan sanyin Jikin babu inda ze kaita.
Da sallama ta shiga falon kanta a qasa bata zauna ba har seda ya bata umarni ta dan dofana kan kujerar data fi kusa da ita.
Maganganu yayi musu dan ba za'ace Nasiha ba wanda kusan duka jan kunne ne ga ita Bara'atun akan abubuwan da suka faru a baya da baya so a sake maimaita irinsu ya kuma tabbatar mata da cewar Binta da kanta ta nemi daya maido da ita har yana fada mata a wannan karon itace qasa da Binta dan haka ta bata girmanta na kasancewarta Gaba da ita a aure da kuma shekaru.
Yanda ya ringa maganar gaba daya se taji ta muzanta ta kuma gasgata tunaninta na cewarba ra'ayin kansa bane wani ne ya sakashi ya maido da ita amma me yasa duk cikin mutanen se Binta?
Meta shirya?
Wace kitimurmurar take so ta sake hada mata data nemi a maido da ita iyakar Taskun data sakata a baya be isheta ba kenan?
Ya gama maganarsa ya basu damar me magana tayi, Binta da kanta ya gama fasuwa da yanda ya nunawa Bara'atun ita ba komai bace yanzu a gurinsa, taji ina ma haka ta kwantar da kai lokacin daya auro Zubaida tabbas da martaba da qimarta a gurinsa ta zarce ta yanzu amma hakan ma babu laifi zatayi duk iyawarta ta sake kafa kanta.
"Nidai babu wani abu daga gurina, Bara'atu daman tun asali yar uwa na dauketa ba kishiya ba ina fatan kuma itama wannan karon zata saki ranta ta zauna dani zuciya daya, sannan kafin a kai ga maganar rabon kwanaki akankwana uku da zakayi mata na qara muku sati kunga kwana Goma kenan saboda kuji dadin Amarci sosai a tuna baya" Bintan ta fada cikin kissa.
Wata dariyar Bosawa Audun yayi, Ita dai Bara'atu kanta yana qasa, to me zata ce musu kuma?
Tana jinsu suna ta soki burutsunsu shida matarsa kafin aka rufe taro yace taje yana zuwa.
Bata tsammaci zuwansa da wuri ba se gashi ko minti goma bata rufa da komawa ba ya shiga da ledar kayan Marmari da kaza.
Washe gari haka ta tashi mamaki na neman kasheta, wato Namiji ko, Namiji duk wadda taci laya akansa ta shigenge.
Irin yanda Audun ya ringa mata rawar jiki yana fada mata kalamai jinsa kawai ta ringayi, haka da safe be fita ba, Binta da ta kusa hadiye zuciya cikin dare ta mutu saboda baqinciki da kishi amma tun farar Asuba ta tashi ta hau aikin da babu lada domin ba dan Allah tayi shi ba.
Lafiyayyen abin kari tayi musu ta kai qofar dakin Bara'atun ta kwankwasa kafin ta ajiye dan ba zata iya shiga ba zata iya manta shiri takeyi ta bazara komai gayyar ta watse.
Haka ta ringa musu wannan kabakin arziqi harna kwana uku kafin ta kasa cigaba, yanda Audun ke rawar jiki akan Bara'atun ya tassama haukatata.
Ita dashi yake ce mata daya san ze samu wannan kwanciyar hankalin da nutsuwa a gidansa da Bara'atu ya maido a maimakon ya Auri Zubaida har yana tambayarta me yasa bata kishi da Bara'atu amma lokacin Zubaida taqi kwantar da hankalinta?
Ta rasa amsar da zata bashi, ba abin ta daddana masa Ashar ba se kawai tace saboda ita Bara'atu a gidan ta tararda kuma Zubaida ba wai kishi da ita takeyi ba kawai Asalinta ne be mata ba da ace itama a gaban Iyayenta ya aurota tamkar Bara'atun da lafiya lau zasu zauna.
Ango Audu dai ya ci karensa babu babbaka ya murji soyayya yanda ya kamata shi da kansa ya tabbatar da akwai banbanci tsakanin Abinda zuciyarka ce take sonsa da kuma wanda wani dalili yasa kake tare dashi.
Bazeyi qarya ba yana son Bara'atu, haka Zubaida da kansa ya ganta yaji yana sonta har kuma yanzun da da dama ze maidata itama suci gaba da zama yanda yake jin su biyun a zuciyarsa Binta bata kama qafarsu ba amma kuma ya rasa yanda akayi ta fisu tasiri a ransa, yafi girmamawa da daukar maganarta fiye da tasu menene dalilin hakan?
Seda ya kwana uku cif yana hutun Angwanci kafinya koma fita aiki a ranar kuma Binta ta sauke hau din data dorawa kanta ta yi mush girki ta bar Mairo taci gaba.
Baqin cikin data qunsa a kwanakin Allah yayi yawa dashi tana nan kuma tana jiran ranar ramuwa kwanaki goman nan cif su ta bawa Bara'atun matsayin kwanakin farin cikinta a gidan daga nan kuma wasan ze canza salo.
Kamar yanda ta qudurta kuwa haka ce ta kasance kwana goma Audu yayi a dakin Bara'atu wadda zata iya cewa k
wanaki goman nan sun zarce shekaru goma na rayuwarta dadi dominbata taba sanin dadin Aure ba a zaman da tayi da Audu kamar na wannan kwanakin.
Ya shayar da ita madarar qauna tarairaya da soyayya ba'a magana gaba daya ya goge mata hadda ya kuma goge duk wani shakku da take dashi akansa na cewar ya dena sonta ko yana da wata manufa akan maidota da yayi, walwalarta ta qaru har wani kyau da sheqi ta qara kana ganinta kasan hankalinta a kwance yake Yanda kuma Bintan take sabgogin gabanta bata shige mata irin na wancan karon yasa ta fara tunanin da gaske ta aje makaman yaqinta zasuyi zamane na babu ruwan kowa da kowa wanda zata so hakan.
Randa Audun ze bar dakinta zuwa na Binta har kuka ta masa ya ringa rarrashinta akan kwana biyu ne kacal ze dawo sannan a qarshen satin zasuje su dakko su Babangida ma su dawo gida a saka su a makaranta dan Zakariyya ma za'a dawo dashi duka za'a hadasu a kaisu makaranta me kyau wannan yasa ta dan rage damuwa.
Lafiya lau yayi kwanaki biyunsa dakin Binta randa ya dawo matasuka tafi Legas wanda tafiyar tazo mata a bazata ce mata kawai yayi ta shirya zasuje wani guri ta dauki kaya kala biyu farko ma ta dauka Bechi zasuje seda ta ganta a filin jirgi ta shiga zare ido, yau gata zata hau jirgi itama bata sake tsinkewa ba seda suka sauka yace mata Legas sukazo ta ringa tsalle kamar yarinya kamar wasa se gasu a gidan su Yakubu.
https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 27*
Da murna tayi musu yawa ita da Balaraban se kawai suka fasa kuka, Yakubu ko bakinsa ya kasa rufuwa, Audun ya shammaceshi dan besan duk abinda ya faru ba wannan abun da yayi kuma ya saka ya wanke duk fushin sa da yake damfare a ransa yaji matuqar dadin ganinsu ko ba'a fada ba kuma yasan hankalin kowannensu a kwance yake.
Aka ringa hirar yaushe gamo, A gidan sukayi kwanaki biyunsu dukda Audu yaso su kama Hotel tunda gidan qarami ne dakuna biyu ne daga nasu Yakubun se na yaransu amma Yakubu yace dole su zauna haka baquntar kwana biyu dai haka suka dawo Kano cike da kewa dan kwanaki biyun ba qaramin dadi yayi musu ba sun fita yawo har bakin ruwa sukaje aka musu hotuna Audu be taho ba seda aka wanke musu hotunan suka taho da kwafi dinsu.