Sashe 21
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ya naganku a nan ga jakarku ma baku kai ciki ba?" Tunde ya fada yana tsince jakar su Audu da Baballiya ya watsar a garin qauyanci.
Cikin dakin ya kai musu Kuku kuma ta aje kayan hannunsa ya fita ya sake kawo wani madaidaici dabe kai na farko ba daga nan ya fita ya barsu Tunde ma ya fita bayan ya jaddada musuga abinci nan suci su qoshi tamkar suna gida.
Kiran la'asar da akayi ya saka Audu miqewa ya shiga dakin.
Nan dinma lailaye yake da Kafet ga gado na Alfarma da sif irin ta cikin Bango se mudubi daga gefe.
Qofar da yake zaton itace ta bayin ya bude ya shiga.
A zuwansa Lagos sun taba zuwa gidansu wani Abokin Yakubu da suke karatu tare a can ya koyi kunna irin famfon daya gani anan idan ba haka ba da yau an sha kunya.
Ya kunna Famfo ya tara hannu da niyar Alwala yaji ruwan zafi sabanin na sanyi.
Wannan dalili ya sakashi canza shawara, sosaiya ya gaji jikinsa na ciwon wahalar mota dan haka ya dakko soso dan yaga sabon sabulu a kwalinsa ya koma bandakin ya tara ruwa me zafi a bokiti ya sheqa wanka a bandakin yan gayu yayi Alwala ya fita.
Tsaf ya shirya yana jinsa kamar yau ya fara wanka a rayuwarsa.
Idanbeyi qarya ba fatarsa har wani sulbi tayi taji sabon sabulu.
Anan yayi sallah seda ya idar ya tuna da Baballiya sukazo ya fito falon, nan ya ganshi Baje kan kafet yana bacci ga Abincin daya kacaccala nan ya barsu bude se zuba munshari yake kamar wanda yayi awanni da kwanciya baccin.
Tsabar takaici besan sanda ya kai masa hauri da qafa ba ya kuwa miqe a zabure ze kurma ihu Audu ya zare masa ido dole ya nutsu ya hau sosa inda ya haureshin yana tura baki girman Banza yake dashi amma ya ringa abu kamar qaramin Yaro.
A gaba Audu ya tasashi seda ya tara masa ruwan wanka ya kuma zuba masa wani a Buta yaja masa kunne akan karya kuskura ya kunna musu famfo ya lalace kafin ya koma falon ya harde kamar gidansa ya shiga cikin Abinci yana ayyana abubuwa dayawa a ransa.
Yana da manyan burika da yake fatan Allah ya cika masa.
Ze ginawa Bara'atu irin wannan Aljannar duniyar, ya hasko kansa yana tuqa mota irin wadda aka dauko su a ciki ha ma'aikata ko ta ina idan ya wuce su ringa zubewa suna gaishe shi dan shidin mutum ne me Izza yana so a girmama shi matuqa.
Seda yayi damkafin ya tattare sauran gefe ya rufe, can dakin ya leqa ya hango Baballiya kan gado yayi rashe rashe yana bacci ya girgiza kai kawai yana murmushi, falon ya koma ya kishingide kan kujera bacci ya sace shi besan tsayin lokacin daya dauka ba sunansa da ake kira ya farkar dashi ya hau murza ido.
"Sannunku, na tayar dakai ko?" Tunde ya fada fuskarsa da Fara'a.
Audu ya zauna sosai yana cewa
"Aa babu komai ina zaune ma bansan bacci ya dauke ni ba"
"Ai kun sha gajiyar hanya, daman Alhaji ne ya dawo sannan kuma anyi Magriba shiyasa ma yace a kirawo ku masallaci" Tunden ya sake fada.
Audu ya kalli qaton Agogon dake jikin bango kafin ya miqe da hanzari ya wuce dakin Tunde kuma ya fita.
Seda ya dalawa Baballiya dukan gaske dan ya gaji da kiran sunansa yana jijjiga qafarsa kafin ya miqe yana soshe soshe.
Audu ya wuce yayo Alwala, a bakin gadon ya ganshi ya sake kifewa aiko ya kuma kai masa mari ya farka da gudu ya fada bandaki.
A rayuwarsa zece be taba bacci me dadin na yau ba.
Yana ganin babu wata Katifa data kai tasu ta gidan Yaya Audu dadi da laushi seda ya hau wannan yaji ashe shi akan sumunti yake kwana.
Yanda Alhaji ya ringa haba haba da Audu har seda abin ya bashi kunya, mamakin daya sake kamashi ganin tamkar duk mutanen gidan sun san labarinsa,
"Aboki nane na Kano da na gaya muku" abinda Alhajin yake fada kenan kowa se ya fara
"Ikon Allah shine sannu da zuwa ya hanya" a haka sukayo sallah suka dawo cikin gidan kai tsaye Alhaji dake riqe da hannun Audu ya wuce dashi Asalin ginin da suka wuce dazun.
Falo na Alfarma da ya qawatu da jere tamkar a qasar turawa.
Alhajin ya zauna kan Kujera Audu yayu qasa ze zauna ya riqo shi yana cewa
"Haba zauna nan sama mana, kaima samu guri ka zauna" ya fada yana kallon Baballiya daya zubawa chandler ido kamar ze kamota.
Qofar glass din dake cikin falon ta bude, wata farar Mace kalar Madara ta fito cikin kwalliya ta kece raini tamkar me tafiya biki qamshinta ya baza gurin ya hade da sanyin Ac dana freshner da aka saka.
Fuskarta dauke da murmushi take takowa tamkar yanda shima Alhajin dake kallonta yake murmushin.
"Lale maraba da baqin Kano" ta fada tana zama gefen Mijinta.
Audu ya zame ya shiga gaisheta ta amsa tana tambayarshi Hanya, seda ya mintsili Baballiya kafin ya shiga hayyacinsa ya gaisheta itama.
Da daddaya yaran sa suka fara shigowa falon, Namiji daya fara shigowa wanda zasuyi sa'anni da Audu se mata guda biyar da suka biyo bayansa gaba dayansu farare ne tamkar Alhajin da Hajiyar gasu yan gayu abinda ya burgeshi dasu yanda suke da fara'a sunata haba haba dasu babu kyama ko nuna banbancin sun fisu matsayi.
A kan qaton Dining din gidan suka zauna duka sukaci Abinci dukda Audu yaqi da farko Amma Alhaji yace se sun zauna shima Dansa ne kuma baqonsa a dole ya dan tsakuri abincin dukda damab cikinsa a cike yake har sannan Baballiya kuwa be kwari kansa ba yaci iyakar geji, har addu'a Audu ya ringa masa a zuciyarsa ta cewar Allah rabashi da lalacewar ciki irin yanda ya zage yana narkar Abinci kamar kwancen Yunwa koda yake sabon dandano yaji a harshen sa.
Seda suka gama cin abincin gaba daya suka koma cikin falon.
Alhaji ya kalli iyalansa yana cewa
"Wannan shine bawan Allahn dana baku labari ya taimake ni a Kano, duk tsayin lokacin nan babu ranar da ba zanyi Addu'a Allah ya sake gama fuskokinmu ba se gashi ubangiji ya karbo Addu'ata"
"Aiko dai ranaku daddaya ne Dady bazeyi maganarka a gidan nan ba, babba da yaro dan gida da me aiki babu wanda be haddace Abokin Dady na Kano ba ni na dauka zanga wani tsoho irinsa ashe ma Dan Saurayi ne" Daya daga cikin yammatan ta fada wadda kuma da alama duk ta fisu kaudi da iyayi.
Baze iya fadar ko ta nawa bace a jerin haihuwa saboda su biyar din kusan kansu daya, da gani irin haihuwar kwanika ce kuma da yake suna da garin jiki shiyasa suka tashi kai daya.
Namijin ya kalleta yace
"Kodai kin qyasa ne kike kiransa wani dan saurayi?"
"Kai Yaya" ta fada tana rufe fuska alamar kunya, Alhaji yayi dariya cike da nishadi ya nuna Namijin yana cewa
"Wannan shine babban Da na Jamal, likita ne ya kammala karatunsa shekara biyu data wuce a Jami'ar qasar Ingila harya fara aiki kuma ina kan kammala gina masa Asibiti nasa na kansa daze cigaba da kulawa dashi, wannan Sakina kenan ita take bi masa se Salima, Ummulkhairi, Mamana Binta se kuma Auta Munira" ya qarasa yana shafa kan Autar da ita ce bata kai girman sauran ba.
Ya sake nuna Sakina,Salima, da Ummu yace
"Wadannan duk suna da Aure Sakina nada Yara biyu ragowar nada daddaya kaga jikokina hudu kenan, saboda zuwanka yasa duk suka zo Mamana da Auta kadai suka rage se Yayansu"
"Masha Allahu" Audu ya fada yana sake kallonsu gasu nan abin sha'awa.
Sakina ce tace masa Mijinta yana zuwa Kano da akwai Yayansa acan yake zaune shi a unguwar goron dutse.
Audu ya washe baki jin an an bato unguwarsu yace
"Wurin ina a Goron dutse?
Ai anan nima gidana yake"
Da mamaki Alhaji ya kalle shi yace
"Oh daman a cikin Kano kake da zama?" Ya shafa kai yana cewa
"Eh a nan nake gwadago, da ina zuwa ina komawa gida amma yanzu bayan rasuwar Innarmu nayi qaura gaba daya da Iyalina muka koma cikin Kanon"
Take fara'ar dake kan Fuskar wadda aka ambata da Binta ta bace, yanda ta hade ran lokaci guda yasaka kowa ya fahimci sauyin nata banda Alhaji da ke jajantawa Audu rasuwar Dada yayi masa ta'aziyya ya dora da cewa
"Kace kana da Iyali?
Ikon Allah"
"Kwarai kuwa Alhaji, idan watan Sallar tsofaffi ya kama shekarata biyar kenan da Aure ina kuma da Yara biyu Maza"
Alhaji da Hajiya suka hada baki gurin cewa
"Ikon Allah ashe harda zuri'a, kai amma abu yayi kyau masha Allahu Allah ya raya yayi musu Albarka, wannan dai qaninka ne ana gani base an tambaya ba" ya fada yana nuna Baballiya dake zuba gyangyadi, bayan ci ai se a kwanta kuma a huce gajiya.
A fusace Binta ta miqe, Mamanta dake ankare da ita ta kalleta tana cewa
"Ina kuma zakije ana hira?" Tayi kwalwal da ido kamar haqaye zasu zubo mata tace
"Kaina ne yake ciwo Mama kwanciya zanyi" bata ko jira me zata ce mata ba ta wuce har tana hadawa da sassarfa saboda yanda take qoqarin fashewa a gurin, wani irin tuquqin bacin rai takeji data rasa na menene.
Ta rasa gane meye hadinta da wannan dan qauyen da daga jin yace yana da mata zuciyarta ta fara kumbura wannan shi ake kira da daukar Dala babu gammo kenan.
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*HALIN KISHI*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*FREE PAGE 10*
Qarfe tara na bugawa daya daga cikin ma'aikatan ya shigo cike da ladabi ya sanarwa da Alhaji Mijin Sakina da Mijin Ummu na waje Alhajin yace yayi musu iso.