← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 91

Sashe 30

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da Asuba bayan sun tashi kuma yace mata ta shirya kayanta kala biyu su tafi tare saboda duk sanda yaje se yan uwansa sunyi qorafin rashin zuwanta kuma ya manta Gobe daurin Auran Saleh Yaron Yaya Baba na Biyu.

Rabonta da Bechin tunda aka kaita tana Amarya se zuwa daya da sukayi gaisuwar rasuwar Wan Baban Bara'atu shima a tsaitsaye ba kwana tayi ba watanni takwas kenan.

"Yanzu a sanyin nan kake so na tafi qauye?" Ta fada tana kumbura baki sanda yace ta shirya din, Audu ya kalleta yace
"Gida fa zamuje ba Jeji ba balle kice zakiji sanyi.

Yaushe ma rabonki da can?

Karki manta Bechi tushe na ne.

Badan iyayenmu basu da rai ba kin san baki isa ki kwashi wata daya ba ba tareda munje kin gaishe su ba, ko yanzun ayyuka ne suke shan kaina su hanani zuwa ziyara akai akai amma ina ganin zan nemi direba wanda ze ri ga kaiku duk hidima Biki ko suna be kamata ace kuna qin halarta ba tunda ba kullum bane sannan tunanin da nakeyi zan gyara gidan mu nacan duk sallah mu ringa tafiya munayi tareda yan uwa"
"Tabdi" ta fada a ranta, a fili kuma ganin yanayin da yayi maganae kamar ransa a bace yake yasa tace masa
"Nima bawai ina nufin wani abu bane kawai dai saboda cikin jikina kaga ya girma be kamata na ringa dogayen tafiye tafiye ba"
"Kwananki nawa da dawowa daga Kaduna?

Bechin ta kai nisan can ne?

Ko da qafa zaki tafi?

Kinga karki bata mun rai idan ba zakije ba ki zauna" ya fada yana ficewa daga dakin.

Ita da take neman hanyar da zata kama shi a hannu ina ita ina neman fitinarsa shiyasa ta tashi ta shiga shirya kayan kamar yanda yace a ranta kuma tana ayyana irin abinda zatayi idan taje.

Ta tsani qauyen da mutanen cikinsa.

Su ba kowan komai ba se Izza da girman kai ya yayan Sarakai wannan shegiyar Bilkin ko nan Kanon tazo haka take mata rashin mutunchi Audun na kallo ba zece komai ba ti duk zatayi maganinsu.

Ta shirya kala biyun kamar yanda yace sannan ta kwashi kayan shayi, Biskit da cincin din da Mero matar da ta samo tana mata girki tayi mata harda dubulan se Sauran Miya duk ta hada kamar me zuwa wata qasar.

Audu be shigo ba se gurin takwas lokacin har tayi wanka ta karya da Mairo da Lantana ita kuma share share take mata duk da suka zo cewa tayi su tafi se bayan kwana biyu zasuje qauye.

Ganin ta shirya ya saka shima shiga wanka a gaggauce ya shirya suka kulle gidan suka tafi.

Sun isa Bechi ana ta hidimar daurin auren da za'ayi washe gari.

Gaisuwar ma kamar sun roqa haka tayiwa wanda taga zata iya.

Wadanda ta raina kuwa ko kallon Arziqi basu samu ba.

Bara'atu na cike da murnar zuwan Audu sedai ganinsa da Bara'atu ya saka duk karsashin ya barta, gabanta ya ringa faduwa dan ita tsoronta takeyi ko kuma tace tsoron kaidinta.

Ita wlh daze barta a nan Bechin yaci gaba da zuwa koda ba duk sati ba zata yarda.

A zaman da tayi harta murmure tayi tas abinta babu damuwar Miji babu ta kishiya kuma idan yazo mata kwana biyun sosai yake tarairayarta yana riritata sabanin a Kano da a suna ne kadai take da girki dan ko Binta ta barshi ya kwanta a dakinta to fa ba zasuyi bacci zur ba tareda tazo ta tashe su ba da sunan ciwo na damunta wanda se a ranakun girkin Bara'atun take ciwo.

Audun da kansa yake ce mata idan a can yake watara ta kwanta ko farkawa batayi se Asuba.

A dakin Bara'atun Binta ta sauka kamar yanda ya tsaya.

Ta haye mata gado tunda ta zauna Sallah kadai ke saukar da ita abinci da duk wasu tarkace dataci nan ta zubar sedai ta matsa gefe ta miqe qafa tana hura hanci mutane na tsakar gida ana hidimar girkin gobe, lokaci lokaci Bara'atu na leqata taji koda abinda take da buqata shara kuwa tayi takai sau biyar daga zuwansu Bintan.

Tavi gyada, tasha rake taci goruba duk akan zanin Gadonta na kwalliya data shimfida mata saboda karramawa gashi me haske amma haka tayi daqal daqal dashi kamar yarinya dole ta canza wani da Bintan ta fita yin Alwalar Magriba.

Bayan tayi isha ne ita da kanta zaman dakin ya isheta dan haka ta fita tsakar gidan tana Kallon Faccalolinta dake hada miya suna hirarsu gwanin sha'awa.

Babu wadda tabi ta kanta tubda suka zo se Laure uwar gidan Hashimu ita ta ringa shishshige mata ta kuwa yi mata qusa daga nan itama ta kama kanta.

Can qofar dakin Sauda Amaryar Aminu ta zauna kan Tabarmar da aka shinfida, Bara'atu na kai tana bawa Babannan tuwo Goggo Fadi na daga qofar nata dakin itama kaca niyar tukwane da mata ta cika gidan.

"Yanzu nake so na qarasa bashi na kawo miki naki tuwon, ko a kawo nan tunda kin fito?

Bara'atu ta fada kamar me tsoronta.

Tayi wata yatsina tana kallon kwanon tuwon.

Tuwon farar shinkafa ne da miyar gyada taji nama da kayan qamshi Bara'atu ce tayi ta dakanta saboda Bintan.

"Kawo" ta fada kamar bataso, ta miqe ta wanke hannunta kafin ta dauko mata fulasan data saka tuwo da miyar a ciki.

Yaro yayi sallama ya shigo da qatuwar baqqar leda, Bara'atu ta karba jin yace inji Audu, dumi da qamshin tsire taji ta wuce dashi daki Idon Binta akan Ledar.

Seda ta raba tsaf ta zubawa Bintan wanda tasan duk hadanarta ba zata iya cinyewa ba, ta dibarwa Goggo Fadi ragowar ta fita dashi tabi duk Matan dake aiki kowa ta taba.

"Amma kinsan ni aka kawowa shine saboda tsabar iyayi da kadifiri kika bude harda rabawa mutane tsabar kwadayi su kuma suka karba, to ze shigo se ki fada masa wanda ya sakaki" Binta ta fada sanda ta ajiye mata nata.

Bata tanka ba ta miqe, Bilki ce ta bata amsa tace
"Allah ya kawo shi din se ya daketa saboda ta baiwa yan uwansa tsire sunci"
"Ni banyi dake ba" Binta ta fada dan bata shiga sharafin Bilki, ta dameta a tijara kuma taga shi kansa Audun yana shakkarta shiyasa bata takakarta ko zuwar musu can tayi.

Haka lokacin kwanciya yayi dare dare ta haye nata Gado ita da yara qarshe se a qasa tayi musu shimfida suka kwanta.

Washe gari aka tashi da hidimar daurin aure, shayi Bara'atu ta dafa mata da safe ta soya kwai dan an kawo Buredi tun cikin dare.

"Ko zakici Waina ko Tuwo a kawo miki?" Bara'atun ta tambayeta.

Binta dake shiryawa bayan ta fito daga wankan da har bandakin ta kai mata ruwa tayi banza da ita ganin haka yasa ta fita itama ta shiga wanka.

Daurin auran na safe ne, kafin goma gida ya cika danqam da mata harda Mazan ma masu shigowa yiwa Goggo Fadi Allah sanya Alkhairi.

Binta tasha kwalliya da Leshi ta baza turare ta kafa kujera a tsakar gida tana kallon kowa daidai.

Bara'atu bata daddara ba ta sake yi mata tayin wainar daurin Aure ko tuwo wannan karon tace ta bata.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number
08129249549*
07011401314*
Wainar Masara ce tayi kyau matuqa ta zubota ta ajiye mata ta tafi kawo miya.

Ta rage miyar tuwon Jiya daman saboda Bintan dan ta san ba lallai ta iya cin wadda akayi ta taro ba, ta bincike Kitchen din inda ta ajiye babu miya se ganin kwanon tayi ma a wanke an ajiye bata da zabi dole ta debo mata ta Bikin.

"Ni zaki kawowa wannan miyar kamar ruwan wankin kan mahaukaciya ni zan ci miki wannan kawai kice kasheni kike so kiyi" Bintan ta fada a fusace sanda ta dire mata miyar, kamar me magana da Babarta Bara'atu tace
"Kiyi haquri, na rage ta tuwon jiya bansan waya juye ba.
Chapter 30 · 0% Book details