← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 91

Sashe 58

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daidai wanda zataci ta soyo mata da kwai ta kawo, ta kalli kayan shayin na nan yanda ta ajiye su tace
"Na dauka kin hada shayin ya sarara kafin ma gama?

To bari na hada miki"
"Baqi mukayi ne?" Suka jiyo muryar Yakubu dake fitowa daga daki yana tambaya.

Balaraba ta amsa da cewar
"Baquwa dai" ya qaraso ciki yana kallon Zubaidan sam beyi mamakin ganinta ba domin yasan halin taurin da kafiya irin na dan uwansa.

Yayi mamakin da har aka kwana hudu ma sannan ya ganta a gidan nasa.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number
08129249549*
07011401314*
Seda suka gaisa kafin ta zaro takardar da Audu ya bata ta miqa masa ba tareda tace komai ba, ya bude ya karanta yayi shiru kamar ruwa ya cinye shi kafin ya ninketa yana sauke ajiyar zuciya ya miqe tsaye.

"Ki gyara mata dakinki seta zauna ciki kafin muga abinda Allah zeyi" ya fadawa Balaraba ya shige ciki.

Balaraban ta miqe a sanyaye tabi bayansa ita kuwa Zubaida Fulas taja ta shiga hada shayi daidai wanda ze isheta ta tabbata dai saki ne a cikin takardar, ita kuma a kullum ta tashi Addu'a bata mantawa da neman zabin Allah a dukkan lamuran rayuwarta dan haka duk abinda ya sameta zata karbeshi da kyakykyawan Ikilasi.

A dakin Balaraba tayi masauki tana ta jaddada mata ta saki jikinta tamkar tana gida.

Bayan da su Dada da qannenta biyu suka tashi daga bacci su suka ringa debe mata kewa harta manta da damuwar data kawota gidansu ta ringa jin zumudin itama dan cikinta ya fito duniya ta tabbatar koshi ya isa ya ringa bata nishadi yana debe mata kewa.

Ta tuna sanda tayi cikin da bayan zubar dashi Audu ya maidota gida a lokacin taso ta bar cikin ta haifeshi saboda ta shirya barin rayuwar Bariki.

Ta so ta haife dan ta raineshi da yaqinin wannan abin ya saka ta samu rangwame a gurin ubangiji na daga tarin zunuban data dibarwa kanta sedai daga baya tunanin irin rayuwar da Da ko yar da zata haifa da qalubalen da zasu fuskanta yasa ta kasa idar da qudurinta.

Sanda wannan cikin ya bayyanar mata tayi murna kwarai musamman dataga irin tarin murna da Zumudin da Audun ya ringayi shima ta ringa hasaso yanda zasu raini abinda zata haifa tare ashe duk mafarki takeyi zanen qaddararta daban abinda take tsarawa a zuciyarta daban.

Bayan fitar Yakubu har ya dauki niyyar zuwa gidan Audu se kuma wani tunani yasa ya fasa hakan, a karo na biyu kenan daya sake yanke danyan hukuncin da yake ganin hakan daidai ne a rayuwarsa.

A bangaren Audu seda hantsi ya daga kafin ya shirya ya fito ya nufin dakin Zubaida dan ya karbo takardar jiya.

Ya tura qofar dake a bude ta sakayata yana sallama ciki ciki shiru babu motsi Tv da Radio da take yawan kunnawa duk a kashe dan haka ya dauka bacci takeyi seya wuce uwar daki nan ma qwalam bata nan.

Tsaf ya bincike ko ina be ganta ba kuma bega takardar ba, yanayin dakin da be nuna alamar an dauki wani abu ko an hada kaya ba yasa yayi tunanin ko maqota ta leqa amma wannan ba halinta bane musamman da duk maqotan yan fadar Binta ne dukda haka ya qaddara wani gurin ta leqa seya koma daki da niyyar kafin ya gama shiryawa ta dawo.

Binta ta kawo masa abin kari yau din jinta take kamar wadda akawa Bishara da Aljanna.

Lantana ce tayi mata albishir din taga Zubaida a hanya da jaka sanda take tahowa ta gaji kenan ta tafi ba kuma zata dawo ba.

Tana so ta zungureshi da maganar taji ko ya sani amma dai tayi shiru harya karya ya fito ta rakoshi ta ringa dariya qasa qasa ganin ya doshi dakin Zubaidan yana kwazara mata kira nan ma shiru bata amsa ba.

"Wai ina wannan yarinyar ta tafi?" Ya jefawa Binta tambayar ta watsa hannu tace
"Yo ka bani ajiyarta ne da zan san inda zataje?"
"Shikenan sena dawo" ya fada daga nan ya fice yana mamakin ina zataje dan sam be kawo gida ta tafi ba tunda ai bata san abinda takardar daya bata ta qunsa ba, haka ya dawo gida da yaqinin ze tarar da ita amma wayam bata nan, ya diririce, ta tabbata gidansu ta tafi kenan amma me yasa zata tafi to?

Ya jefawa kansa tambayar rainin wayo.

Bayan Isha ya shirya tsaf ya cewa Binta zeje wata unguwa, gidansu Zubaidan ya tafi zuciyarsa ta ringa tuhumarsa me ze kaishi gidan amma hakan nan ya zungura kai yaje.

Malam Hassan ya rasa ina ze sakashi saboda murna bayan sun gaisa ya tambayeshi Iyali yace
"Dazun Babarsu take cewa gobe In Allah ya kaimu zata leqa ta ganota kuwa jiki yayi nauyi har tana cewa ko zata dakkota tazo gida tunda haka akeyi a Al'ada haihuwar fari"
Cikinsa ya bada wani sauti quuuu, bata zo nan ba kenan?

To ina yarinyar nan ta tafi kardai fa ta hefashi a masifa in duniya ta sake shiga ai da seta bari seta zo gidansu ta gayawa Mahaifinta komai sannan seta tafi amma yanzun ta ina ze fara yi masa bayanin shima nemanta yazo?

"Aa bafa abin dole bane idan baka so ta dawo gidan se tayi zamanta dan naga fuskarka ta canza daman matane da Al'ada kasansu basa wasa da ita" Mala Hassan ya katse masa tunani a zatonsa zancen dawowarta gida ne ya canza fuskar Audun besan Al'amarin yafi gaban haka ba.

Tilas ya masa sallama a gurguje ya taho bayan ya ajiye masa na goro.

A gida ma rkicewa Binta yayi da tambayar ina zasu nemo Zubaida ina ta tafi?

"Ya wuce ta koma inda ta fito ne, wai kai meye ma naka na damuwa ina ka saketa duk ma inda zataje taje mana kana da matsala da ita ne?" Ta fada cikin jin haushin yanda yake ta safa da marwa cikin damuwa.

Washe gari da farar safiya ya tafi gidan Yakubu ya ringa buga musu qofa kamar za'a tashi duniya Yakubun ya fito yana ganin shine ya shiga surfa masa fada shima yana tambayar ba'asin wannan bugu kamar ya masa sata.

Daya masa bayanin abinda ya kawoshi qiris ya rage Yakubun yayi dariya amma ya kanne a ransa yayiwa Allah tasbihi wato tun ba'aje ko ina ba aiko ze gane kuskurensa domin baze fada masa tana gidan ba.

"Ni meye nawa a ciki yanzu Audu?

Kashedi nawa kamun akan na fita daga sabgar gidanka?

Ashe da nace kayi haquri ka bar maganar nan baka daddara ba to ka saketa ta bar maka gida meye kuma abin damuwa a ciki ko daman ka dauka zata zauna ne kuci gaba da ci mata mutunchi kuna aibatata kaida matarka?" Yakubun ya fada yana tsareshi da ido.

Audu yaja tsaki yace
"Ni bance ta zauna ba amma data tashi tafiya ai seta tafi gidansu ko amma yanU naje jiya bata can yanzu me take so na gayawa mahaifinta idan suka zo ganinta basu sameta ba?"
"Se ka gaya musu ka saketa ita kuma tana tsoron ta tayarwa da mahaifinta hankali idan ta koma gida s
hine ta sake shiga duniya, ni dana san wannan shirmen ne ya kawoka wlh bazan bude qofata ba haka nan ina bacci na me dadi ka daga mun hankali da bugu.

Ka tafi ka nemo yarinyar mutane dai kafin iyayenta su farga, kaga daman ba'a jima nayi wani case Mata ta bata Iyayenta sukace Mijin ne ya siyar da ita yayi kudin jini AAllah ya tsareka kaima kar suce kayi kudin jinin da ita daman an fiyi da masu ciki" yana gama fada masa hakan ya maida qofarsa ya rufe ya bar Audu cikin tashin hankalin daya ninka na farko akan maganar da yayi ta karshe.

Daman a Bechi ana rade radin qungiyar Asiri ya shiga yayi kudi farat daya da yawa sun qaryata cewar wai sirikinsa kuma ubangidansa ne ya buda masa yake samun kudi haka?

Su kance shi din har nawa ya mallka da yake bawa Audun kudi haka?
Chapter 58 · 0% Book details