Sashe 67
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka taci gaba da wanke wanken tana ta qoqarin gano inda ta santa haka nan kuma ta tsaya mata a rai harta gama tana maida kwanuka ta kasa haqura ta cewa Mairo
"Nikam fuskar matar can batayi miki kalar sani ba?"
"Gaskiya Aa, ke kin santa ne?" Ta mayar mata da tambaya se ta tabe baki tace
"Oho nidai se na ga kamar nasan me kama da ita, qila kama ce to ko kuma a hidimar gidan nan muka taba haduwa da ita"
"Ta yuwu hakan" Mairo ta sake bata amaa tana cigaba da abinda yake gabanta.
Daga soro aka rafka sallama, muryar gardi ce Lantana da bata komai taja Gyalenta ta leqa taga Maza biyu da motar kayan katako a qofar gidan.
"Yauwa, kiyiwa Hajiyar magana kice ga kaya Alhaji yace a Kawo" wanda da alama shine Direba ya fada mata kafin ta bashi amsa Bilki da ta jiyo sallamar itama ta biyo sahu tana ganin kayan kuma ta gane nasu ne dan haka tace
"Ku sauke toh a shigo dasu, ga Almajirai nan su tayaku"
"Toh Hajiya" suka amsa mata kafin su fara kiciniyar kwance Belet din da suka zagaye kayan da ita.
https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 26*
"Hajiya wasu Mazane da motar kayan katako, wannan me kama da Alhajin tace su shigo dasu gashi ana kaiwa wancan dakunan" Lantana ta sanarwa da Binta.
Mamaki ya kama Bintan, kayan katako kuma na menene?
Ta tambayi kanta, to kodai Bilkince zata dawo nan gidan da zama tunda ta samu Labarin a gida take auranta ya mutu?
In ko haka ne da anyi tashin hankali da masifa kuwa, ita da gidanta bata san komai ba kawai taga ana shigo mata da kayan gado taqamar tana Qanwar Megida ko?
To dashi da itan duk basu isa ba.
Fita tayi dan taji ba'asi, a tsakar gidan taci karo da Audu da batasan shigowarsa ba tana ganinsa tace
"Yawwa gara da kazo, ban fahimci zuwansu Bilki ba ga kuma wasu kaya da akw shigo dasu na menene?"
Fuska a sake ya dubeta bayan daya bawa Direban motar da suka kawo kaya kudi dan har sun gama saukewa yace
"Kayan su Babangida ne"
"Su Babangida?
Su din ne aka siyawa kayan daki se kace na Amarya sababbin Gado da kujeru?" Ta tambayeshi fuskarta na nuna mamakin da take ciki.
Tafiya ya farayi zuwa dakin da su Bilkin keta kiciniyar hada kayan yana ce mata
"Amarya ce mana, ko bakya so a kwace miki kambunki?"
"Audu!" Ta kira sunansa a kausashe tana bin bayansa dan zuwa yanzu kanta ya fara qullewa bata fahimtar maganganunsa.
"Ina zuwa, bari mu gaisa dasu Goggo Ramma ki jirani a sama" ya bata amsa daga nan ya shige falon ya barta a tsaye tana saqa da warwara tana jiyoshi da Bilki yana ce mata
"Hajiya Bilki Tijjan Bechi"
"Kace na qulle jakata bana zan sauke farali" Bilkin ta mayar masa tana ajiye tsumman da take goge goge dashi, yayi murmushi yana tsugunnawa dan gaida Su Goggo Habi ya bata amsa da cewa
"Kusan haka, da dai layi za'abi se Yaya Mairo da Amina sunje sannanke amma yanzu kin san ance Albarkacin Kaza qadangare kansha ruwan kasko to kena Albarkacin qawarki bana zaku jera ku tafi tare in Allah ya yarda".
Bilki ta rangada gida wadda ta zama kamar saukar guduma a kwakwalwar Binta cikin karadi tace
"Nagode dan uwana Allah ya ida nufi, harna hangomu nida Bara'atu muna zagaye Ka'aba ya ubangiji ka nuna mun wannan rana" suka amsa matada Amin gaba daya.
A mutunce suka gaisa kafin ya fito ya ganta tsaye a gurin har sannan,
"To muje" ya fada mata se kuwa ta bishi kamar raqumi da akala zuwa saman nasa.
Zukudi tayi tana kallonsa tareda sauraron abinda yake cewa,
"Nasan ko a baya bakida matsala da ita, akasi aka samu akan abinda ya faru wanda da bakinki kika furta kin yafe har kika nemi dana dawo da ita kuma nayi matuqar jin dadin hakan, ina fatan zamanku ya canza salo a wannan karom dan zanja mata kunne sosai akan kar a kuma maimaita abinda ya faru a baya".
Murmushi yake yi irin rai fes din nan harya gama maganar, Binta data zama kamar wata hoto se idanu ke motsi suna yawo tsakanin fuskar Audun da bakinsa, so take ta lailayo Ashariya me maiqo sannan ta tambayeshi a gidan kut***r uban wa tace ya maido da Bara'atu sannan dawa yake zaton za'ayi zaman lafiya sedai bakinta ya mata nauyi, bata iya koda motsawa ba seda ya miqe yana mata sallama kan ze koma Kamfani, takun saukarsa daga matakala ne ya farkar da ita daga suman zaunen da tayi ta zabura ta miqe sedai kafin ta kai ga sauka harya fice daga gidan dan tana kaiwa soro taji qarar Motarsa ya bar qofar gidan.
Zaman dabaro tayi ta dora hannu biyu a kai ta zunduma ihu kamar wadda aka aikowa da mutuwar Mahaifinta su Lantana da Mairo suka zaburo dan ganin menene, a dakin Bara'atu ma goggonninta biyu sun niyyaci fita banda Hadiza da Bilki da suka san za'a rina Bilkin ce ta dakatar dasu tana dariya ta cewa Goggo Habi
"Kinga abinda nake gaya miki ko?
To yanzu aka fara, Hadiza rufi mana qofar nan dan ba hankali ne da ita ba se ta fado mana be kuma kamata mu biye mata ba dan ko gaban shari'a akaje mu za'a bawa laifi saboda gidanta muka zo"
"Hakane" Hadizan ta fada tana tura qofar ta rufe kamar kuwa sun san nan ta nufo dan zabura tayi kamar zakanya ta durfafi dakin tana kuka tana koro ruwan Ashariya tamkar zararriya ta shiga jijjiqa qofar da niyyar cirera sedai ko Gezau.
"Wallahi tallahi na rantse da girman Allah in baku bude qofar nan ba sena babbake ku a ciki, sena nuna muku ki qananan yan iska ne, ni za'ayiwa haka?" Ta fada cikin qaraji tana cigaba da bubbuga qofa.
Dattijai biyun suka tsure, Goggo Habi fadi take
"Me gado a bude qofar nan karta qona mu kinji abinda take cewa"
"Kyaleta Goggo duk kurarin banza ne baki ne da ita babu abinda zata iya a aikace wanda zeyi abu ai baya fada" Hadiza ta bata amsa, Bilki dai bata tanka ba se jera samiru takeyi abinta tana yan waqoqi tamkar ma bata jiyo hauka da Tijarar da Binta takeyi a tsakar gida.
Iyakar masifa, bala'i da duk kalar Ashar wata ma a Bakin Bintan goggonnin Bara'atu suka fara jinta yau seda kamar yanda Hadiza ta fada kurarin banza take dan data gaji da buga qofar gefe ta zube tana kuka kamar me tana maganganu da cin Alwashi kala kala.
Mairo data ga abin bana qare bane ta koma kan aikinta ranta duk babu dadi da wannan al'amari, ita kuwa Lantana tana nan tsugunne daga gefenta tun bayan data samu tsarabar hambari a qoqarinta na riqeta ta gwabje mata fuska daga nan ta matsa gefe amma taqi tashi daga gurin se fadi take
"Kiyi haquri Hajiya, ki tashi mu koma can daki kisha ruwan sanyi"
"Se naci "gi***n du***in uwarki Lantana idan kika sake cewa nayi haquri, Allah ya tsinewa haqurin kema Allah ya tsine miki" ta fada dole Lantana taja baki ta kame tana sosa fuska dan inda ta mangaretan har sannan be dena mata zafi ba tsabagen neman gurin zama da iya gulma yasa take zaune a gurin har sannan.
Binta na kuka wiwi kamar Jifa se ga Turai ta shigo gidan ita da wata mata, tun daga qofar gida ake jiyo ihu da kururuwar Bintan dan haka cikin sauri suka shigo dan ganin me yake faruwa.
"Na shiga uku ni Amina, me ya faru?
Waya mutu Binta?" Turai ta fada tana nufar qawar tata da ta ke nan zaune kamar kayan wanke ta miqe qafafu kanta ya tuje dan tun fara Tijarar tata dankwali ya cire.
Qoqarin kamata ta shigayi danta miqe amma ta kasa saboda yanda ta saki jiki ita aba ba kadab ba ganin Turan kuma yasa ta sake sakin wani kukan me ban takaici kamar wata yarinyar goye tana fadin
"Na shiga uku Turai Audu ya kasheni, wai Bara'atu ya mayar be gaya mun ba"
"Har naji sanyi a raina ashe ba mutuwa akayi ba, dan Allah kama jikinki ki miqe, Zainab zoki tayani mu dagata" Turai ta fada jin abinda Binta tace.
Dakuar da sidin goshi bayan sun hadu su uku harda Lantana suka kai Binta daki se sannan ma suka tuna da Yaron da suka baro a daki ya fado daga Kujerar data kwantar dashi yana ta tsala kuka gwanin Tausayi.
"Dauke shi Dan Allah kuje waje ki rarrashe shi" Turai ta fadawa Lantana, ta dauke Nazirun tayi waje dukda ba haka taso ba, so tayi taji komai dukda ta tsinci kan zancen amma zata so ayi komai a gabanta yanda zata fi jin dadin bata labari idan ta fita.
"Yanzu saboda Allah me kikayi haka?
Akan wata baquyiyar Bara'atu shine kika kwanta tsakar gida gaban masu aikin ki kina tumami kamar wadda ta kwace daga Turu wani irin abin kunya ne wannan Binta?" Turai ta fada cikin fushi.
Binta dake kuka tace
"Ki qyaleni, saboda ba'a taba miki kishiyar nan bane shiyasa duk abinda nayi kike daukarsa shirme ke kinsan zafin abin ne balle ki gane yanda nake ji?"
"Koma menene, kome kikeji be kai ki zauna kina zubarwa da kanki mutunchi ba a samu abin fada akanki, wannan haukan da kikayi wlh Allah yasan inda ze tsaya dan wannan munafukar me aikin naki kina kallonta kinsan nadar rahoto takeyi.
Allah na tuba ba Bara'atu ba ko mata uku Audu yace ya daura aure dasu ya kai ki kwanta kina kuka akai balle Bara'atun da ko kashin jikinki ya fita a gurinki, har meye abin tashin hankali a matar da kika san idan kinga dama ko ruwa ba zaki barta tasha da dadi a cikin gidan nan ba.