Sashe 56
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka suka dawo Kano nan kuma zamansu ya dauki sabon zama ya fita a sabgarta tsakaninsa da ita ya ajiye mata kudin cefane idan ya kwana a dakinta kenan in tayi abinci bayaci gaba daya ya birkice saboda rashin nutsuwa daya sakawa ransa.
A bangaren Zubaida kuwa gaba daya ta maida hankalinta gurin Ibada ne da kuma kula da lafiyarta data abinda yake cikinta tayi matuqar qoqari gurin ganinbata bari damuwar Audu tayi tasiri a ranta ba haka duk iskancin da Binta zata mata bata daga kai ta kalleta yanda kuma be sake mata tambayar da yayi mata randa sukaje Bechi be itama bata daga maganar ba a haka suka kwashi tsayin sati biyu cikin wannan hali.
Da safiyar ranar Asabar tana zaune daga bakin qofarta ta cire saiqoyin data jiqa ta shanya su kafin ta gama shanye ruwan daya jiqun seta maidasu, tana zaune kan Tabarmar data shimfida da yar Radionta a gefe tana sauraro ita kadaice a gidan tun safe Audu da Binta suka fita kamar yanda taji a bakin Bintan tana bawa qawarta da taje gidan labari Audun ya biya mata Aikin Hajji fitar da sukayin tana kyautata zaton duk cikin shirye shiryen tafiyar ne dan abin ya matso a kwanakin kusan kullum se sun fita.
Taja Qaton kofin robar dake cike da ruwan magani ta kurba ta ajiye ta saka hannu biyu tana shafa cikinta da taga kamar yayi qasa sosai kuma ya dan rage girma, sam bata ji shigowa ko sallamarasu ba saboda ta nitsa cikin tunani se maganar Binta taji akanta tana cewa
"Ahaf, ka gani ba?
Wasu jiqe jiqen aka qara kawo mata bana gaya maka wannan tsohuwar Matar Babanta ce take mata safara ba kullum tana tafe gidan nan yau ta kawo wannan gobe ta kawo wancan gashi nan kuwa cikin ya fara komawa za'a sake danne shi qila ace mana anyi bari se wata shekarar a haife shi tunda mun ramfo wannan wayon ko?" Bintan tayi maganar tana zuba mata ido fuska a washe irin duniya ta mata dadi babu abinda yake damunta duk da cewar bata tsammaci za'aja lokaci ba wannan Bam din data dana be tashi ba amma kamar yanda Turai ta gaya mata tabi komai a hankali dai kar suyi gaggawa to tana zuba ido taga yanda wasar zata kaya.
Audu bece komai ba ya wuce samansa, jiki a sanyaye Zubaida ta miqe ta shiga tattara abubuwanta Binta natsaye tana zubda mata habaici,
"Ke kin dauka zaki kawo mana shege wato kici bulus bamu gane ba?
To qaryarki tasha qarya wlh tun wuri ma ki nemo farkan daya dibga miki ciki ki nana masa abinsa badai a gidan nanba kar muke kallonki"
"Wlh Binta ki tsoraci gamuwarki da Allah" Zubaidan ta fada hawaye na sakko mata, Binta tayi shewa tace
"Nan da sati i yanzu ina gaban Ka'aba yarinya in shafata in roqi Allah yayi gaggawar tona miki asiri ki tattara ya naki ki barmin gida gayyar tsiya gayyar na'ayya"
"Allah baya bacci" Zubaidan ta sake fada daga haka ta shige dakinta.
Tana zaune Audu ya shiga ya zauna akan Kujera yana fuskantar ta, irin zaman da yayi yass gabanta ya shiga faduwa, cikin kaushin murya yace
"Zan sake tambayarki bana buqatar qarya ko wani alaye ki fada mun gaskiyar magana Cikin da kikace kin zubar dagaske kike ko kuwa kwantar dashi kikayi?"
Kuka ta fashe dashi ba tareda ta sgirya ba tace
"Yanzu ka dauki maganar da take fada dagaske kenan?
A ina ka taba ganin an kwantar da ciki?
Idan ma anayi tayaya ciki ze kwanta tsayin sama da shekara daya a Jikina ace baka lura ba wai me yasa akai baka amfani da kwakwalwarka se abinda matarka ta kitsa maka ba tareda bincike ba ka hau kai kawai ka zauna?"
"Nine bana amfani da kwakwalwata?" Ya fada yana nuna kansa, a duk maganganun babu abinda ya tsinta se wannan, ta miqe cikin kuka tace
"Kwarai, kwakwalwarka hotoce Audu domin bata aiki se abinda wani ya kitsa maka dashi kake tunani.
Ya za'ayi ka kasa tantance gaskiya da qarya?
Se yaushe idonka ze bude ka gane tuggu da makircin da matarka take shirayawa a cikin gidan nan?
Ta laqawa uwargidanka sharrin Kisa shine zata shegantaka maka Da ko Ya ka hau kai ka zauna?
To wlh na gaji bazan iya wannan rayuwar ba, ba zan zauna da mutumin da besan daidai ko abinda ya kamata yayi a matsayinsa na Namiji ba, bazan cigaba da zama ace Kishiya ita zata tsara mun irin zaman quncin da zanyi a cikin gidan aurena ba.
Ka fito fili ka fadi abinda yake ranka ka fadi cewar kana kokwanton cikin jikina karka sake sakayawa ko ka titsiyeni da tambayar abinda ya shafi rayuwata ta baya, ka fadi kai tsaye Matarka ta kitsa maka cewar cikin jikina ba naka bane kuma ka hau ka zauna babu abinda zance maka kuma banida amsar da zan baka a yanzu se dai nace maka mu jira lokaci, ubangijin daya wanzar da samuqar cikin ze qarware duk wani qulli da ake qoqarin laqaba masa amma kafin nan ka sani bazan iya cigaba da zama da kai ha Audu gidanmu zan tafi zanje na qarasa rainon cikina a can har Allah ya saukeni lafiya abinda na haifa ya raba gardamar zargin da kake neman laqabamun" tana gama fadar haka ta shige daki tana Kuka ta hau hada kaya.
Laqwas yayi akan Kujera kamar kazar dataji ruwan zafi, ya yunqura ze miqe kenan Burum Binta ta fado dakin tana cewa
"Babu shakka daman ance tabarmar kunya da hauka ake nadeta kana zaune tayi maka wasan kwaikwayo da salonso na Tsofaffin kikali ko?
To ai idan kina da gaskiya fitowa zakiyi ki kare kanki baqai ki hau koke koke kina hada kaya ba kaga magana ta tabba da ciki aka shomigo mana so take ta tafi se ta koma inda za'a rufe maka baki ruf ka kasa cewa komai koda yake yanzun ma naga kamar bakin naka a rufe yake ai"
"Banida lokacinki ki kuma jirayi sakamakonki komai nisan tsahon zamani" Zubaida data fito da jaka ta fada tana gotata.
Tana fita Audu da Bintan suka rufa mata baya Binta na shewa kamar sabon shigan hauka tana tafa hannu.
"Subhanallahi me yake faruwa haka" suka tsinkayi muryar Yakubu da shigarsa gidan kenan yana fada, Zubaidan taci burki kuka yana sake kwace mata Binta ta gyara tsayuwa murya a sama tace
"Me fa ya faru Yaya Yakubu?
Abin kunya tayi asirinta ya tonu kuma shine take mana qaramin hauka".
Zuciyar Yakubu ta tsinke ya tafi wani tunani na daban seya kalli Audu dake nan tsaye qato dashi kamar wanda kwakwalwarsa ta bata se zare ido yake yace
"Me ya faru?
Ban fahimci abinda take cewa ba?"
"In maka gwari gwari Yaya Yakubu, ciki.
Shege tayo take neman laqawa qaninka ta gurbata muku Zuri'a" Binta ta sakeyin caraf ta amshe tamkar sunanta ya koma Audu.
"Hasbunallahu wani'imal wakeel, Audu dagaske ne abinda take fada?" Yakubu ya fada yana ja da baya dan ya samu balance sosai jin wannan babbar magana.
https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 22*
Wuta ta daukewa Yakubu sanda Binta ta gama rattaba masa abinda ya faru dan ita ta zama bakin Audu yau.
Ya ringa kallon Audun yana jira yaji ya qaryata ko ya fadi akasin abinda Bintan ta fada amma yaga yadauke kai gefe yana wani cin magani se ya maida kallonsa kan Zubaida dake irin kukan nan da meyinsa ya gaji dayi, tausayinta ya rufeshi gefe daya takaici da tsanat Bi ta me girma tareda qyamatar Hali irin na dan dan uwansa suka kamashi.
"Ku Fita ki bamu guri" ya fadawa Binta da Zubaida.
Zubaida ta miqe ya kalleta yace
"Kar kije ko ina ki koma dakinki" ta juya ta fita Binta ko ta gyara zama, cikin kaushin murya yace mata
"Zaki fita ko sena kwasa miki mari a nan gurin?"
shidin ba ma'abocin zafi bane amma bashida wasa musamman a gurinta sam basa ga maciji yanda kuma ya hade gida ya tabbatar mata ze iya kwasa mata mari idan bata tashi ba kamar yanda ya bara umarni dan haka ta miqe tana qunquni.
"Nayi maka uzuri domin bayan Kaidin Mace Jahilci da duhun kai suna dawainiya dakai Audu lokaci yayi daya kamata ace ka koma Makaranta Both Islamiyya da Boko" Yakubun ya fada bayan fitar Binta wadda ta labe a bakin qofa ta kasa kunne tana jiran taji me zasu tattauna.
A zabure Audu ya kalle shi yace
"Ni kake kira jahili?"
"Qasurgumi ma kuwa" Yakubun ya bashi amsa idonsa fes a kansa kafin yaci gaba da cewa
"Banda kai wawane wanda bashida tunanin kansa se abinda aka kitsa masa kuma Jahilci yana dawainiya da kai ta yaya Mace zata zo maka da irin wannan maganar shirme wadda ko yaro qarami aka gayawa dariya zeyi amma ka hau kai ka zauna harka sheganta cikinka da kanka wane kalar wawanci ne yake damunka Audu?
Binta ce ta auro maka Zubaida da zatayi maka lissafin cikinta ka yarda ko kuwa?
Watanta nawa yau a gidanka?
A lissafin watan sama auranku ya shiga wata na goma ma kaga kenan cikinta har yazarce watannin da Da yakeyi kafin a haife shi kuma da zata ce maka Da ciki ta shigo kwantar dashi tayi kai mahaukacine da ka kwashe tsayin lokaci tare da Mace da ciki amma baka gane ba ko kuwa akanta ka fara Aure balle kace baka san yanda alamar ciki take ba?