Sashe 44
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saboda ina tunanin a daura Auran kawai idan an kai kudin"
"Ina da Ayyuka da yawa a gabana bana jin zan samu halarta sedai daga baya nazo naga Amarya amma a ina ka samo matar?" Yakubu ya tambayeshi, Audu yayi shiru kamar mara gaskiya kafin yace
"Amm yar nan cikin gari ce unguwar Alkantara, yarinyar nada hankali da nutsuwa sosai se ka ganta ma"
"Amma da zan baka shawara ka dauka da nace kayi haquri ka maido da Bara'atu kodan darajar yayanta ka dubi rayuwar da zasuyi a Bechi babu wadataccen Ilimin Islamiyy ada Boko"
"To ya kake so nayi da wannan din bayan na sanarwa da Iyayenta zan turo so kake na zama qaramin mutum?" Audu ya fada a dake dan ya gaji da maganar ya maido Bara'atu da suka dameshi da ita, Yakubu yayi murmushi yace
"Bance ka fasa ba kana iya hadasu su ukun ai Alhamdulillahi Allah ya hore maka abinda zaka iya riqe su nidai yaranka nake dubawa saboda zuwan nan da nayi na gansu banji dadin yanda suka koma ba gashi sun fara tasawa"
"Naga muma a Bechin nan aka haifemu muka girma, yanzu kai bada shekarunka ba harda Aure ka kammala sakandire ka tafi Jami'a?
Suma idan sun girma sun kai munzalin da zasu iya wahaltawa kansu se su dawo nan gidan su zauna yanzu dai ba wannan maganar mukeyi ba ka daure dan Allah kazo kasan dai nan duniya bani da kamarka" Audu ya fada.
Yakubu yayi dariyar takaici yace
"Zanyi maka Addu'a daga nan kuma da ace abinda ka fada da gaske be baka da kamata da baka qi karbar shawarata ba muddin ba cutar da kai nayi niyya ba, yanzu ina aiki ne zamu sake magana idan na samu lokaci" daga haka ya ajiye waya ya bar Audu sororo da waya a hannu seda ya kashe ma sannan ya tuna dayar maganar da yake so ya masa ta jin dalilin daya saka ya dauki Baballiya ya tafi da shi Lagos zeyi hutu ba tareda su.
Sanar masa ba seda sukayi magana da Alhaji Zakariyya yake gaya masa dan a gidan Baballiyan yake zama idan sun samu hutu yanzu haka yana ma yana shekararsa ta qarshe shirye shiryen fita sukeyi.
Duk yanda Audu yayi da Yakubu akan yazo Auransa qi yayi dole ya haqura badan yaso ba kuma har ransa yaji rashin jin dadin hakan saboda bashi da tamkar Yakubu sannan ya rasa abinda yasa Yakubu ya dauki wannan fushin dashi.
Yanzu kenan yana so ya nuna Bara'atu ta fishi a gurinsa kenan?
Haka nan ya tura su Yaya Baba da wasu Abokanansa sukaje masa neman Auran wanda ba'a tashi daga gurin ba seda aka daura shi.
Yana gida ranar be fita ba yana tsammatar dawowarsu Binta natayi masa gwalgwaso ta aje wannan ta kawar da wancan surutu kuwa har kunnensa ya gaji ga babu halin yace tayi shiru ko ta fita ta barshi ya huta.
Lantana ce ta kwankwasa musu qofar saman, rawar kan matar ya zarce misali seda Binta ta taka mata burki sannan ta dena zirgillin shigar mata turakar Miji.
Bintan ce ta bude qofar ta leqa fuska a hade tana cewa
"Meye?
Wai sau nawa zanja kunnenki akan tako benen nan ballantana kiyi tunanin shiga dakin nan?
Ke wace irin daqiqiyar mace ce ne Lantana?"
"Kiyi haquri Hajia, baqi kukayi shine nace bari nazo na sanar miki" Lantana ta fada cikin qasqantar da kai amma a ranta zagin Binta takeyi.
Binta ta yatsina fuska tace "Baqi kuma daga ina?
Ni yau babu wand
a babu wanda nayi da ita zatazo"
"Ai Hajiya Maza ne ba mata ba kuma kamar yan Uwan Alhaji ne dan naga wasu suna yanayi dashi"
Tsaki me qarfi Binta taja, ta tsani wannan zaryar maukar da yan uwan Audu suke musu.
Ba'a rufa sati se wani yazo daga Bechi badan ta taka burki bama har kwana suke so su ringayi amma duk zatayi maganinsu dan ba zata dauki wannan abun ba suzo su dabaibayeshi su cinye musu dukiya to bada ita ba.
Ciki ta juya ba tareda tacewa Lantana komai ba, Audu na kwance kan kujera tace
"Kayi baqi"
Da gaggawa ya miqe kamar wani mara gaskiya, be ko tambayeta su waye ba ya shige daki ya zuro rigar wandon jikinsa ya sauka qasan seta bishi da sauri dan se anyi komai a gabanta.
Haka take duk sanda yan uwansa suka zo seta kasa ta tsare komai zasu fada ko ya basu seta gani idan akayi dace kuwa saqo ya biyo ta hannunta daman se abinda mutum ya gani.
Qannensa Mata dai da suke ciki daya tun fitar Bara'atu babu wadda ta sake taka qafarta gidan se yan dakin Goggo Maryo ne suke zaryar zuwa ko gajiya basayi da wulaqancin Binta dan Mazan sun fisu kamewa da wadatar zuci muddin sukaje to dole ce ta saka ko kuma maganar Gonarsa wadda Aminu da Yaya Baba ne suke kula masa dasu yanzu.
Bayan Audu ya sauka qasa a tsakar gida ya tarar da Baqin nasa a tsaitsaye.
"Bismilla muje can falon" ya fada yana musu jagora zuwa falon da Bara'atu ta fita can ya gyara ya saka kujeru yake sauke baqinsa amma haka Binta zata bisu har can din.
Suna zama tana shiga ko gyale bata yafo ba ta dirirce ganin harda Yaya Baba ko babu komai shidin babbane a cikinsu yanayin rayuwa yasa take ganin kamar ma ze girmin Dadynta dan wahala tasa tsufa ya masa sammako banda yanzu da Al'amura suka fara daidaitar musu ya dawo hayyacinsa dalilin Alkhairan da yake samu daga kula da Gonar da yakewa Audu amma da kam anji jiki ga tarin iyali ga Abinda suka Dogara dashi na Noma Hashimu ya ringa Ha'intarsu yana Azurta kansa su da wahala amma shine cikin walwala da jin dadi wannan ya saka suka yada makaman yaqinsu suka rungumi su Audun hannu bibbiyu gashi kuwa suna sharbar romon damakaradiyya har ya sauke farali a dalilin hakan.
"Au kune sannunku da zuwa ina wuninku?" ta fada tana jada baya tareda sunne kai, suka amsa mata a tare, ta tsaya daga qofa bata fita ba bata shoga ciki sosai ba Audu ya kalleta yace
"Kawo musu ruwa mana"
"Ayyo toh, bari a kawo" ta fada ta juya tana dannan masa Ashar a ranta.
Mairo ta kwalawa kira ta gaya mata ta kawo ruwa tayi sauri ta koma bakin qofar ta labe.
"Munje kuma Babanta ya sanar mana da daman kun gama magana shiyasa bamuyi gardama ba dayace a Daura auran, to Alhamdulillahi anyi komai kamar yanda shari'a ta koyar yanzu ya rage kuma ka saka ranar da matarka zata tare, Allah ya sanya Alkhairi ya sa Abokiyar arziqi ce" Yaya Baba ya fada.
Ihun da Binta ta fasa ya hanshi yin magana se ya miqe da sauri ya fita suka rufo masa baya kowa da tunanin abind aya sameta, tana tsaye ta dora hannuwa biyu a kai, ganinsu yasa ta qara fashewa da ihu me firgitarwa da tayar da hankali har tana dira qafafu kamar qaramar yarinya.
"Lafiyarki?
Meya sameki?
Ko kunama ce ta harbrki?" Audu ya jera mata tambayoyin cikin rikicewa yana qoqarin riqeta amma taqi tsayawa, ihu take tsalawa duk qarfinta kuma taqi magana haka nan bata dena dire diren ba.
"Kodai shafar jinnu ne tana dasu?" Yaya Baba ya tambaya yana ja baya, takaici ya qume Audu na abinda takeyi ya juya yana ce musu
"Muje dan Allah lafiyarta qalau wulaqancine da rashin son a zauna lafiya ya sakata haka" seta ruqo rigarsa ta baya cikin gunjin kuka tace
"Wlh baka isa, idanna yarda shegiya uwata ta haifeni aure?
Aure fa naji suna zancen an daura maka ni zaka munafunta kayi mun kishiya da kudin ubana har yaushe ka nemi auran ban sani ba?
Na rantse da Allah kayi kadan" ta fada tana cukuikuye masa riga, bayaninta ya fahimtar dasu dalilin kukan, Yaya Babba ya baza riga yace
"To mu bari mu wuce dan me motar daya kawomu yana waje dama yana jiranmu, Allah ya zaunar lafiya ya kade fitina idan an tsaida ranar Biki ka sanar mana mu shirya a can ai za'a kai Amaryar kamar wannan itama ko?" Ya qarasa yana nuna Binta.
"Ku koma ciki Yaya bamu gama magana ba ke kuma sakeni" ya fada yana qoqarim banbare hannunta daga rigarsa amma ta qara riqewa tam tana qara tabbata masa idan ta sake shi shegiya take.
"Kaga ka kashe wannan wutar tukunna bari muje Allah ya rufa Asiri" daga haka suka fice suna waiwayen Binta dake ihu tana qara maimaitawa Audu be isa ya mata kishiya da kudin ubanta ba.
Mari me kyau ya kwasa mata bayan fitarsu daya saka ta sakeshi babu shiri.
Ya nuna ta da yatsa yana cewa
"Kinyi na farko kinyo na qarshe ni ba sakarai bane da zaki cimun kwala a gaban mutane, Aure kuma nayi, ba'a qaro mata ke na Auroki ko ba wata kika tarar a gidan ba?
To ki kiyayeni wlh" yana gama fadar haka fuuuu ya wuce cikin gida ya barta a tsaye taba sharbar kuka.
A haukace ta zari mayafi tabar gidan bata ko dauki Zakariyya ba ta tafi gidan Turai can ta tarar da ita a wani birkitaccen yanayi dan itama gyale ne a hannunta da alama fita zatayi qiris ya rage suci karo kowacce taja baya.
Binta ta fashe da sabon kuka tana shigewa cikin falon Turai tabi bayanta tana cewa
"Gidanki zani"
"Ai gani nazo, Turai ni Audu ze wulaqanta a duniyar nan ni ya tozarta yayi mun kishiya ban sani ba da kudin ubana?"
"Danqari, Binta amma Audu ya shammace mu kuma wlh ko a bakin Ali banji zancen auran nan ba se yau, to ya akayi haka?
Kin ma san wadda ya aura wai?" Turai ta fada cikin Tashin hankali.
Binta na sharar hawaye da Majina tace
"Ina na sani, badan nabi bayansa bama da yan uwansa sukazo da qila sedai naji ana gafara za'a shigo da Amarya ki taimaka mun Turai ya zanyi?
Wlh bazan dauki wannan wulaqancin ba Audu be isa ya tozartani a duniya ba yayi kadan har marina fa yayi yanzun me kike tsammanin zeyi mun idan matar ta shigo".