← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 91

Sashe 39

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ta yaya mutum kamarka me kamala, na fahimci ba halinka daya da Abokinka ba ya za'ayi kace zaka auri Karuwa kamata wadda bata da mutunchi ballantana daraja?" Ta fada hawaye na sake sakko mata.

Audu ya zauna da kyau ganin ta sakko tana so suyi magana yace
"Nima ban sani ba, amma na tabbatar qila Allah ne yaso dana zama silar fitar dake daga wannan rayuwar shiyasa ya doramun sonki.

Sannan maganar Mutunchi ko Daraja, ban sanki ba bansan daga inda kika fito ba amma na tabbatar koma daga ina kike kin kasance Mace me Mutunchi da Daraja a baya, qaddara ce ta kawoki nan domin mata kadan ne suk shiga Bariki da son ransu, mafi aka sari Qaddara ce take afka musu wadda mutane suke kasa yi musu uzuri harsu ingizasu ga zuwa abinda yafi wanda ya same su a baya muni.

"Duk abinda dan Adam yake aikatawa muddin be mutu ba yana da damar shiriya ya nemi yafiyar ubangijinsa, kema lokaci be qure miki ba.

Ki bar wannan rayuwar da babu komai cikinta se qasqanci, ki koma gida wlh da gaske nakeyi zan aureki bada wasa nake sonki ba".

"Mahaifina ya koreni, yace karna sake komawa gidansa idan har naje be yafe mun ba.

Ina so naje, ina kewar mahaifiyata amma bana son na sake shiga wani fushin nasa akan wanda nake ciki" ta fada cikin sauti me ban tausayi.

"Ke din yar wane gari ce?

Kuma meya fito dake daga gida?" Audu ya tambayeta.

Bata boye masa komai ba na daga labarin rayuwarta ta gaya masa gaskiya, yaji tausayinta kwarai dagaske ya kuma ga baiken Mahaifinta.

Irin wannan qaddarar ta fadawa mata da yawa, idan da ace iyaye suna taya Yayansu karban qaddararsu a yanda tazo musu da an samu raguwar masu fantsama Bariki.

Da yawan iyaye Sukan manta cewar Abin kunyar da suke tunqahon yayan sun jawo musu har yasa suka kada su duniya kadan ne akan rayuwar da suke jefasu suyi, ga dakon zunubi domin duk abinda suka aikata na barna tare za'a raba musu Sakamakon da iyayen saboda sune suka turasu zuwa ga barnar.

A tunanisa da a ringa zunden mutum ana cewa yarsa ta zama Karuwa gara a kira shi uban wadda aka tabayiwa Fyade ko tayi cikin shege ya barta a gabansa ta shiryu har ya aurar da ita wannan haqurin da mutum yayi se ubangiji ya dubeshi ya shirya masa zuri'a amma korar yara akan wata qaddara mara kyau ba daidai bane, su kansu Iyayen sunyi bankwana da kwanciyar hankali daga ranar da suka kori Yayan nasu basa sake samun nutsuwa.

Audu basuje Zariya da niyar kwana ba amma Alamun cin galaba akan Zubaida daya gani ya sakashi kwana a garin.

Yayi mata alqawarin ze nemo mata mahaifinta muddin yana raye ze hada su kuma koya mutu ze maida ita gida gurin ragowar yan uwanta.

Ya roqeta akan ta shirya su tafi Kano tare, ze bata mafaka har zuwa sanda zata daidaita da iyayenta amma taqi, tace dai yaje ba zata dawo idan har mahaifinta ya mata izini.

Haka washe gari suka dawo Kano gaba daya Audu bashi da kuzari, Bashir nata yi masa shaqiyanci da cewar shima ya zama dan hannu dan tunda suka rabu basu hadu ba seda safe da zasu wuce Kano dan haka besan duk abinda ya faru tsakaninsa da Zubaida ba.

A gida ya tarar da Binta cikin yanayi na neman tashin hankali dan yana shiga tambayar data fara jefa masa itace
"Daga gidan uban wa kake?"
A lokacin yanayin sanyin jiki da kuma martabar mahaifinta da ya wuce ya zageshi ya saka ya qi tanka maka amma kaitsaye zuciyarsa ta ringa raya masa ya gaya mata daga gidan ubanta yake ko da abinda zatayi akai.

Bata haqura ba ta bishi har daki tana ihu da hargagi tareda fadar maganganu.

Baturiya matar Ali ce ta gaya mata Audun sun tafi wani gari gurin Mata tareda Bashir itama tsintar zancen tayi a gurin Mijinta yana gayawa wani Abokinsa daya je gidan shine ta wanke qafa ta tafi gidan Binta ta gaya mata ranar bata iya runtsawa ba a tsaye ta kwana tana jiran taga ta inda ze bullo amma be dawo na se yanzun.

Duk kalar rashin mutunchin data ringa zazzagawa be tanka mata ba ya shige daki ya kullo qofa ya shiga wanka.

A ranar yake so yaje ya fara binciken iyayen Zubaida data gaya masa ita din haifaffiyar unguwar Alkantara ce, sanda ya fito Binta ta sauka daga saman harya fita kuma beji motsinta ba ya dauki mota ya bi kwatancen da Zubaida tayi masa besha wahala ba saboda sunan Mahaifinta data gaya masa Malam Hassan Na'ibi yana fada aka kaishi har qofar gidan lokacin qarfe biyar na yamma rana tayi sanyi a qofar gidan ya tarar da Malam Hassan din da wasu dattijai guda biyu kan tabarma suna hira.

Ya ringa kallon mutumin, kamanninsa daya da Zubaidar, sedai yanayinsa ya nuna kamar bashi da lafiya saboda a kishingide ma yake be iya zama sosai.

Audu ya qarasa kan tabarmar ya zauna suka gaisa duk suna masa kallon rashin sani.

"Gurinka nazo Baba, idan babu damuwa ina so zamuyi magana ne" ya fada yana kallon Malam Hassan ganin haka ya saka ragowar suka gane baqonsa ne.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number
08129249549*
07011401314*
"To ai babu damuwa samari ina jinka ka fadi abinda yake tafe da kai wadannan ba baqi bane Aminaina ne koma menene yake tafe da kai ka fada suji" Malam Hassan ya fada.

Audu ya kalli mutanen da ya kira da Aminansa kafin ya sunkuyar da kai, bashida tabbacin basa cikin wadanda suka zugashi harta kori yarsa tunda yace Aminansa ne su dan haka baze fadi maganar a gabansu ba balle su hanashi karbarta.

Qara qasa da kai yayi yace
"Kayi haquri Baba amma daka daure munje gefe dan maganar da take tafe dani dakai kadai zan iya tattaunata"
"Ka je mana Malam kaji abinda yake tafe dashi" daya daga cikinsu ya fada, Malam Hassan yayi shiru yana kallon Audu kafin ya yunqura ya janyo sandarsa dake gefe ya tashi, Audu ma ya miqe yabi bayansa yana kallon yanda yake tafiya a gicciye tamkar wanda ya taba samun ciwon mutuwar barin jiki".

A soron gidan suka tsaya, Malam din ya kwalawa wata yarinya me suna Surayya kira ta fito da sauri, kamarsu daya da Zubaida dan seda gaban Audu ya fadi daya ganta.

"Kawo mun kujerata" ya fada mata ta amsa da "toh Baba" kafin ta juya babu dadewa ta dawo da kujera me qafafu hudu irin ta qarfen nan doguwa Malam din ya dogara ya zauna akai yana nunaqa Audu wani tudu me kama da Dakali dake cikin zauren amma da Qaton dutse akayi shi.

Audu ya zauna yana fuskantar Malam din.

"Ina jinka samari, meke tafe da kai?"
"Kayi haquri da abinda nazo maka dashi Baba sannan ina fata ka fahimce ni"
"Ka tafi kanka tsaye bana son wannan alayen me yasa kake son magana dani?"
"Akan Zubaida ne" Audu ya fada yana kallon Malam din dan ganin yanda zeyi reacting aikuwa ya zabura tamkar ze fado daga kan kujerar Audu ya tare shi.

Jikin Malam Hassan ya dauki rawa ya qanqame Audu yana cewa
"Zubaida naji kace?

Ina ka ganta?

Kasan Zubaidata?

Dan Allah tana ina daman tana tana raye?" Malam din ya fada cikin rawar baki tareda daga sauti abinda ya fito da yarinyar dazun da gudu kenan tana tambayar
"Baba lafiya?"
"Sunan Yayarku ya ambata, dan girman Allah ka gaya mun a ina kasan Zubaida tana ina?" Malam din ya sake fada babu tsammani se ganin hawaye yayi a fuskar Malam tamkar yanda Surayya ta fashe da kuka itama tana ce masa
"Ina Yayarmu?

Dan Allah ka gaya mana a ina ka santa?"
"Kayi haquri Baba zan gaya muku amma se ka nutsu ka dena daga murya karka janyo hankalin mutanen waje" Audu ya fada yana zaunar da Malam din a kan Kujerar daya tashi.

"Muje ciki Samari wannan maganar bata zau bace muje ka sanar mun inda kaga Zubaida" Malam ya fada yana miqewa, Surayya ta dauki kujerar jikinta na rawa suka shige ciki Audu ya mara musu baya.

"Tausayin Malam da Surayya ya rufeshi ganin yanda suke kuka tamkar ransu ze fita bayan daya gama basu labarin inda ya hadu da Zubaida.
Chapter 39 · 0% Book details