← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 91

Sashe 51

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka bita mana karfa ta jiwa kanta ciwo kamar watsi take da kaya" Zubaida ta fada jin Binta na zubar da kaya a qasa se ya tafi solo solo ya shiga dakin ita dai Zubaida ta juya ta fice har sannan jikinta be dawo daidai ba daga tsoron shan suburbuda a hannun Binta.

Bata san ya suka qare ba dan har bacci ya fara fizgarta kafin ya shigo ransa duk babu dadi ganin haka yasa daman tayi shirin bacci a kwance take tana jiransa se kawai ta gyara kwanciya dakyau tayi baccinta shima ya gama abinda zeyi be nemeta na duk yanda yake cike da zumudin kebewarsu amma ya gagara yin komai, yanda Bintan ta ringa kuka tana fadin zata tafi kawai ta shiga duniya yana wulaqantata ne saboda yaga Dadynta ya goyi bayansa sanda ta koma gida ita kawai gara ta tafi koma inane tunda babu me qaunarta ya shiga tsakaninta da Iyayenta kuma yazo yana wulaqantata akan Matar daya hadu da ita daga baya tasan baya qaunarta tun sanda aka kashe mata Da amma be dauki matakin komai ba.

Haka ya kwanta ransa duk babu dadi sedai da Asubahi da yar dagwas ta kaishi gari me nisa tuni ya manta da wata Binta da Emotional blackmail dinta.

Tana can ta saki baki tana jiran ya bugo Asubanci yaci gaba da rarrashinta dan jiyan Data gama surutai bandaki ta shiga ta kulle yayi yayi ta fito taqi tace ya fitar mata a daki in ba haka ba zata kwana a ciki sannan ya tafi to ta dauka daya dawo masallaci ko kafin ma ya fita se shiga ya dubata amma taji muqus har gari ya waye tarwai se Tara saura na safe suka fito da Amarya yayi shirin fita, tana zaune kan barander dakinta Lantana na share tsakar gidan suka fito ta zube tana gaishe su.

Kamar jiya yauma harda dan risinawar Zubaida ta mata ta gaidata, bata tanka ba ta zabga tsaki bata dai yi masifar data sababa shirun nata kuma se yaji babu dadi dan haka yacewa Zubaida yana zuwa.

Falon Bintan ya shiga ya tsaya a tunaninsa zata bi bayansa amma shiru, ya leqo ya mata magana nan ma ci kanka bata ce masa ba wannan ya hasalashi ta wulaqantashi gaban me aiki dan haka ya fice fuu ko Adawo lafiyar da Zubaida take masa be amsa ba.

"Zaki san ni ba sa'ar wasanki bace wlh yau se kin gane kurenki badai jiya ya ceceki ba?

Yau naga ubanda ze kwaceki a hannuna" Binta ta fada tana miqewa bayan data tabbatar Audu ya fice daga gidan tabi bayan Zubaida data qarawa tafiyarta sauri jin abinda take fada, gudu ta saka ganin dagaske kamata take shirinyi tana fadawa daki ta turo qofa Binta ta saka hannu zata dannata ciki bisa tsautsayi ta datse mata yatsa da qarfi take ya fashe ya fara jini.
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 20*
"Akan me zaki kulle qofa?

Dukanki zatayi ko cizo da ze saka ki kulle qofa har ki hada da hannunta ki matse?" Audu ya fada cikin kaushi yana duban Zubaida dake durqushe gabansa kanta a Qasa Binta kuma na daga gefe tana yarfe hannu yatsanta data datse da qofa ya kumbura idanun nan sunyi fici fici da alamun tasha kuka ba kadan ba yau din.

Audu na yin sallama Lantana da bata tafi ba ta zube a gabansa tana fada masa uwar dakin nata babu yanda take tana daki, hankali tashe ya doshi Dakota n nata can ya tarar da ita tayi zaman dirshan a qasa tana yarfe hannu tana kuka harda majina, shiri sukayi da Bintan akan hakan dukda dagaske take jin azabar ciwon yatsan amma tuggun da take so ta hada da faruwar hakan shi ya saka ta sake rakwarkwabewa ba iyakar zafin ciwon ba.

Daya tambayeta ya akayi taji ciwon take ta gaya masa Zubaida ce, akan ta bita daki su sulhunta kamar yanda ya roqeta jiya akan tayi haquri ta kwantar da hankalinta su zauna lafiya to bayan tafiyarsa tayi tunani akan hakan kuma taga ya kamata ace tayi shine yau taje dakinta da niyyar ta bata haquri akan abinda tayi mata jiya a maimakon ta saurareta se kawai ta hau zaginta tace ta fitar mata a daki, data tsaya ta dafa qofar shine ta hada harda hannuta ta datse shi kuma kamar fulawar da aka zubawa Yeast ya shiga kumbura ya tafi fuuu ya kira Zubaidan nan gaban Binta ya titsiyeta yana tambayarta ba'asin dalilin rufe qofa.

"Ni ba a sanina na bigeta ba kuskure ne" ta fada cikin sanyin murya, Binta ta zabura tace
"Wlh qarya takeyi tana sane ai Lantana na gurin ka tambayeta kaji"
"To a tambayi Lantanar mana in har zata fadi tsananinta da Allah ko ita ta san ba ina sane na bige miki hannu ba, sannan ni bani na nace ki shigar mun daki ba bare har ki saka hannunki qofa ta datse ki" Itama Zubaidan ta katseta
"Ke!

A gaban nawa ma rashin kunya zaki mata?

To bari kiji daga yau koda wasa karki sake kullemun qofa tunda dai gida nawane ba na wani ba, sannan dukanku matana ne babu wadda nayiwa shamaki daga shiga dakin wata a cikinku, yanzu kalli ciwon da kikaji mata ji yanda hannun ya kumbura fisabilillahi hakan da kikayi yayi kyau?" Audu fada yana zare mata ido, Zubaida sadda kai qasa saboda kukan dake shirin bada ita tace
"Amma dai tsakani da Allah ba haka ya kamata kayi ba, seka tambayeni abinda ya hadamu tunda dai kaji daga bangarenta"
"Ke zaki tsara mun abinda zanyi a cikin gidana?

To banyi hakan ba nace banga damar yin hakan ba koda abinda zakiyi?" Ya hayayyaqo mata seta fashe da kuka saboda takaici tama rasa abinda zata kuma ce masa
"Tashi kije" ya
bata umarni yana wani dauke kai dan kukan nata ya tabashi amma shi a dole ta masa laifi shiyasa ya dauke kai.

Cikin kuka guiwoyinta a sanyaye ta wuce dakinta.

Zubaidan na fita itama Binta ta fashe masa da kuka tana cewa
"Yanzu shikenan ta jimun ciwo taci bulus iyakar abinda zaka ce mata kenan sannan saboda makirci ta fita tana kuka kamar ita aka zalunta?"
"To ya kike so nayi, so kike na rufeta da duka ko kuma na riqe hannunta ki rama abinda tayi miki?

Ina kinji dai tace kuskurene?" Audun yayi kanta a fusace, yanda yayin yasa tayi shiru bata kuma cewa komai ba wato tuggunta be samu shiga ba so tayi ya rufe Zubaidan da fadan koma ya falla mata mari koya rufeta ma da duka amma dai ko banza hakan ma babu laifi tunda ya sakata kuka a gabanta da haka zata cigaba da nunawa Zubaidan ita din ba kowa bace a gurinsa Audu, kuma duk yanda ta dama haka za'a sha.

Qarawa kukanta volum tayi babu ko dadin sauraro Audu yaja tsaki yace ta tashi suje gurin wani wanzami dake qasansu a duba hannun.

"Wlh ba zani ba idan ba zaka kaini Asibiti ba sedai na zauna da hannun haka kuma gobe karka saka ran zaka fito ka tarar dani a gidan nan Kaduna zan wuce" ta fada cikin kuka.

Wannan tasa ya kaita Asibitin suka bata magu gunan rage radadi bayan an mata allurar kashe kwayoyin cuta sannan suka dawo gida lokacin goma harta gota, seda taci abinci tasha magani kafin ya wuce dakin Zubaida.

Tana zaune a falo ta kunna Tv amma hankalinta baya ga abinda ake nunawar tayi nisa cikin tunanin da tunda ta baro dakin Binta takeyinsa.

Se taga kamar shari'ar ta Audu ba haka ya kamata ya gudanar da ita ba, tambayarta ya kamata yayi abinda ya hadata da Binta har wannan tsautsayin ya faru bawai ya dora mata laifin matsewa matarsa hannu haka nan ba kuma da yake maganar kowa tana iya shigar dakin yar uwarta babu shamaki a ina ake haka fusabilillahi?

Yanda ya shiga fuska a daure haka tayi masa sannu da zuwa jiki babu karsashi guiwoyinta suka sake sanyi da Al'amarin Audun, to fushin na menene kuma?

Ba an gama magana ta wuce ba?

Ya gama uzurirrikansa data bashi abinci yace ya qoshi, bata sake tsinkewa da lamarin ba seda ya juya mata baya da sukaje kwanciya a ranta tace lallai abin babbane.

"Kayi haquri in dai akan abinda ya faru jiya ne kake fushi wlh ba ina sane na matse mata hannu ba ita ta biyo ni tana zagina tace zata dokeni ni kuma tsoron haka yasa na shigo na tura qofar bansan ta saka hannunta a ciki ba" Zubaidan ta fada hawaye na saukar mata sanda Audu ke shirin fita da safe ba tareda ya ko kalli kayan karin data jera masa ba.

"Oh, bayan abinda kikayi shine kina da bakin sake magana harda sharri zaki mata a yaushe ta zageki harta biyoki zata dokeki?" Ya fada yana dakatawa daga fitar dayayi niyya.

Hawaye suka balle mata na takaici, wato sharri tayi mata?

Ita Bintan Allah kadai yasan abinda ta fada masa wato natane gaskiya se ita data fadi ainihin abinda ya faru shine zece ta mata sharri?

Muryarta na rawar kuka tace
"Akan me zan mata sharri?

Sannan ai kaima zaka iya bada shaida akai dan ba shibe karo na farko data zageni ba ko tayi yunqurin dukana a gabanka ma anyi shekaran jiya ba kai ka kwaceni daga hannunta ba?" Ta fada tana tsare shi da ido.

Yayi jummm alamar ya gasgata abinda ta fada din amma saboda qi fadi da rashin son gaskiya irin nasa se ya murje yace
"Rashin kunya zakiyi mun har kina tsareni da ido kamar wani sa'anki?

To bari kiji muddin kina neman zaman lafiya a gidan nan dole ki zauna lafiya dani da kuma matata.
Chapter 51 · 0% Book details