Sashe 26
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yakubu sun kwashe kayansu wanda Bechi ya aika dasu Bilki ta dauki Gado Aisha Kujera ragowar tarkacen yan uwa suka raba sun rabu da Audu akan ze nemi fili nan kusa a tayar masa da wani gini domin siyan bangaren Yakubun yayi dukda Yakubu yace Aa ai gida gaba daya na Audu ne dan da kudinsa ya siyi fili ya gina amma shi yace ba haka ba koda shi ya gina kyauta ce yayiwa Yakubun dan haka yanzun siya yayi kuma in Allah ya yarda kafin su zo Kano ze maida masa da wani.
Ya tada gyaran gurin, anyi toshe toshe da liqe liqe, maginin gaske ya dakko Injiniya akayi masa aikin se ga guri ya fito fes an fitar da Sef cinten daki biyu da falo a tsakiya harda bandakin tsakar gidan aka shigar mata a daki se kitchen aka lailaye ko ina da Torazo gida dai ya fito na zamani a ganin ba za'a kushe ba dukda yasan dai a matsayin Bintan tafi haka amma ai ita tace taji ta gani ko a bukka ze ajiyeta zata zauna.
Bara'atu ma ta samu arziqi an saka mata torazo a dakunanta dana su Abdullahi da tsakar gidan, Gadonta ta maida musu can aka saka mata sabon da Audu ya mata ga kujeru da kafet harda kayan Kallo se danqareriyar firiza duk a kayan fadar kishiya ita kuwa me ta manta?
Audu nata doki da murna sanda yan uwan Binta sukazo ganin guri se kuma murna ta koma ciki.
Babu kara suka ringa kushe gurin da yada maganganu akan an asirce musu yar uwa banda haka me Binta zatayi dashi balle har ta yarda ta zauna a gurin da ko Boyis kwatan su Albarka.
Basu kwana a gidan ba kamar yanda ya shirya musu otal suka kama washe gari suka juya sukaje can sukayi ta cece kuce da fadar maganganu abinda ya saka Mamansu magantuwa kenan saboda yanda suka fasakta muhallin Bintan abin yayi muni.
Tayi tsammanin yanda ya zage yayi lefe haka ze qerawa yarta gida kodan ya rage mata radadin auransa da bata so yar tayi, meye amfanin Kudin da Ubanta ya sakar masa domin tana da labarin qanin Kyauta yake bashi mai, idan an kai masa tanka goma kudin Biyar Alhajin yake karba haka tsayin shekara daya bata taba jin yace ga kudi Kaza na Ribar Mai da Audu ya kawo ba amma shine zeyiwa yarta wani Akurkin kaji a sakata a ciki.
Cikin fushi da tari Alhaji da maganar, takanas ya tashi Tunde suka tafi Kano kwanaki biyu bayan komawarsu su Salima a sannan Biki ya rage saura kwanaki goma se ganinsa kawai Audu yayi ba zata.
Shidai Alhajin bega aibun gurin da suka ringa fada ba domin a abinda ta rasa a gidansu baze wuce girma da kuma taswirar gini ba dukda haka domin gujewa duk wasu surutai na matar tasa da bata taba qalubalantar wani hukuncinsa ba yasan tayi kawaici matuqa akan lamarin auran tunda har ta magantu yanzu tabbas abin ya kaita maqura dan haka yacewa Audu
"Me yasa baka sanar dani baka da gurin da zaka ajiye Mamana ba?"
Audu yaji wani iri, wato shima ya raina gidan kenan?
Amma dai a qarfinsa sunsan yayi abinda ze iya harma ya zarta.
Shiru yayi bece komai ba gudun kar zuciya ta kwashe shi ya gayawa Alhajin mara dadi dan be gama hucewa daga fushin cin zarafin da Yayansa suka masa ba daman.
"Ina ganin zan saka a duba gida ginanne idan yaso se a siya a sakata ciki ko ya ka gani?" Alhajin ya sake fada se sannan Audu ya daga kai ya kalleshi.
Wato zancen Labahani gaskiya ne da yake cewa idan ka auri yar masu kudi rainin arziqi se abinda ka gani sannan su zasu ringa yi maka iko da gida to idan kuwa haka ne shi ba za'ayi akansa ba, baze bada qofa ba balle daga baya idan ya hana ace yayi Butulci.
"Kayi haquri Alhaji ba ina nufin raini a gareka ba amma maganar gaskiya wannan ne muhallin da nake dashi da zan saka Binta a ciki.
Ka sanni ka san Asalina haka itama tun gabanin tafiya tayi nisa a tsakaninmu tasan komai a kaina kuma ta yarda da hakan zata zauna dani a kowanne.
Kayi haquri ka barni na ajiyeta a inda Allah ya horemun a yanzu, ina fatan zuwa gaba na gina mata daidai da tsarinta amma a yanzu abinda ya sawwaqa kenan".
Badan Alhaji yaso ba gudun kuma karya takurashi yaga kamar ya masa kutse a cikin lamarin gidansa yasa ya haqura ya tafi kuma kamar yanda Audun ya fada ita Bintan taji ta gani dan ya zaunar da ita kafin a kawo kudin Aure ya tambayeta ta amice tace koda can Qauyensu ze kaita tana sonsa a haka zata aureshi.
Haka akayi Biki Amarya ta tare, iyayenta sun zuba mata abinda dakin ze iya dauka.
Danma kuma babu laifi ginin an fitar da dakunan da baga dan haka sun dauke gadajenta Biyu kantama kantama yan Dubai.
Kujerune dai seda aka canzo ainin wanda aka siya mata saboda falon ya matse ga Divida bango guda yar waje kujerun ma irin bajaj din nan ne 1 sitter su takai girman two sitter matsakaitan kujeru dan haka suka matse matuqa dole aka mayar aka canzo mata wanda gurin ze dauka.
Kwana biyu yan uwanta sukayi suka juya dalilin seda suka kaita Bechi wanda basu kwana ba ko banda ruwan gora da aka basu babu abinda suka iyaci na daga abincin tarbar Amarya yamma lis suka tada jaraba seda aka kaisu Kano gidan Amarya dan sunce ba zasu iya bacci a garin ba wannan Abu ya qona ran Yan uwan Audu ya ku.a darsa tsanar Binta a ransu duk da ba ita ta musu ba amma sun ce itama haka halinta yake kenan tunda bata hana yan uwan nata yar musu da magana da izgilanci ba
Audu kansa ya qara hasala wannan karon dan haka babu wata sallamar Arziqi suka koma Kaduna suka yita fadar qarya da gaskiyar abinda ya faru na wai an aura masa ita buqata ta niya ya fara musu rashin mutunchi.
Todai babu yanda suka iya aure ya qullu Amarya da Ango na son junansu sedai fatan a zauna lafiya.
Sati gudan da Audu yawa Amarya Binta an barji soyayya irin wadda ya dauka a fina finan turawa kadai ake irinta.
Baiwar Allah Bara'atu aikinta ta dafa abinci wanda take qure duk basirarta da abubuwan da Balaraba take koya mata idan sunzo tayi musu takai musu idan sunci ta debo kwanuka safe rana dare haka take wannan Bauta tsakaninta da Audu kuwa da safe idan ya dawo sallar Asuba ze shiga ya duba su shikenan se wata safiyar ko idan taje kai musu abinci baya fita ko ina yana daki suna barzar Amarci a haka ya kwashe sati dayansa gurin Amarya wadda zuwa sannan ba zatace ta mata wani abu ba tsakaninsu gaisuwa ce tana da Fara'a da kuma son yara dan kullum zata kira su Abdullahi ta basu abin dadi ita Bara'atun cema wani lokacin take hana su zuwa saboda karsu takurawa Babansu da kullum yana daka.
Sati daya Audu ya tara su yayi musu nasiha sannan suka raba girki kwana bibbiyu kuma kowacce girkinta zata ringayi.
Hakan yawa kowacce dadi, a falon Binta akayi zaman dan haka bayan ya sallame su Bara'atu tayi mata seda safe ta tafi.
Yara duk sukayi bacci ta sake gyarawa tayi kwalliya da wasu kayan bacci da ta siya gurin Maman Kabir Maqociyarta saboda wannan rana.
Tayi gyaranta daidai gwargwado na cikin jiki dana fata ga sabon kitso da lalle da tayi dukda kullum ta kalli Amaryar tata Da take Jajir ga jiki duk madara da tsoka se taji kamar Audu ba ze sake yi mata kallon Mace ba wannan tunanin ya sakata damuwa har tayi yar rama daman babu jikin se ta sake komawa yar yarinya firit da ita.
Tana nan zaune falo tana kallon Tv da tsumayen Audu har bata san bacci ya kwasheta ba.
Motsin rufe qofa ya farkar da ita, ta kalleshi kafin ta kalli Agogo, sha biyu da rabi a saninta tun Tara da mintina take zaune a gurin kusan awa uku kenan.
"Bakiyi bacci ba?" Tambayar daya fara jefa mata yana shigewa cikin daki, ya gotata qamshin turaren Binta ya bigeta yanda kasan yanzu ya shafashi.
Ta yunqura tabi bayansa tana cewa
"Ina zaune bansan bacci ya kwasheni ba" ta dakata ganin harya kwanta.
A tausashe tace
"Har zaka kwanta bakaci abinci ba?"
Fuskarsa washe da murmushi me kama dana rainin wayo yace
"Au na manta qanwarki tace kiyi mata aikin gafara ta bani abinci".
Tayi zukudi tana kallonsa kafin ta sauke ajiyar zuciya ta juya to me zatace?
Kwanukan Tuwon shinkafa miyar gyadar datayi wanda ciki ta dibarwa Bintan iyakar cikinta dan tun da safe yace a gurinta zeci abincin dare yanzu kuma ya canza shawara yaci a gurin Amaryarsa "to Allah yasa ya ishe su" ta fada a fili tana Adana abincin a cikin Fridge duk Balaraba ce ta koya mata tace a can miyar sati takeyi ta saka abarta a firinji sedai ta dumama idan zasuci haka sauran abinci duk adanawa takeyi shiyasa itama tunda ya siyo mata ta fara wannan dabarar da yake koda yaushe da wuta hankalinta kwance yanzu bata rasa abinda zata bawa yara kafin ta gama abinci.
Seda ta gama kintsa komai ta dauke Babannan da bata san sanda Abdullahi ya kawo mata shi falon ba dan ya saka rigima a gurinsu ze kwanta dukda bata yaye shi ba ta kaishi daki abin mamaki har Audu yayi bacci, jiki a sanyaye ta kwanta itama ranta cike da saqe saqe.
Washe gari da safe tana hada abin kari ta jiyo sallamar Binta.
Tun daga cikin kitchen din take jn tashin qamshin turarenta, gabanta ya fadi sanda suka hada ido.
Kwalliyarta kamar me zuwa zaben sarauniyar kyau.