← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 91

Sashe 40

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah ka yafe mun, wlh sharrin shaidan ne da zuciya ya ingizani na kori yarinyar nan.

A sanadiyyar haka abubuwa da yawa sun faru.

Baqin cikin rashinta ya saka mahaifiyarsu kwanciya jinyar da har tayi Ajalinta nima kuma na gamu da hawan jini har mutuwar Barin jiki na samu seda na shekara biyu ina jinya bayan rasuwar Habiba kafin Allah ya bani lafiya, wallahi nayi nadamar abinda na aikata babu inda kuma ban shiga ba a garin nan ina cigiyar Zubaida, har gidajen Mata masu zaman kansun na ringa zuwa ko Allah ze saka na samu wanda ya ganta amma ba'a dace ba se daga baya wani bawan Allah ya sanar mana wata Mata ce ta tafi da ita amma besan motar garin da suka hau ba.

Tu daga nan na fawwalawa Allah na ke kuma Addu'ar idan har Zubaida tana raye Allah ya gama fuskokinmu kafin na koma gareshi kona nemi yafiyarta, dan Allah Samari tana ina?

Ka kaini naga yata karna mutu da haqqinta a wuyana" Malam ya fada yana sake rushewa da kuka.

"Kayi haquri ka kuma kwantar da hankalinka Baba, naso ace mun taho tare da ita amma taqi tace ba zata dawo Kano ba se idan har kai da kanka kace ta dawo dan bata so ta sake shiga wani fushin naka amma yanzu tunda anyi haka zan koma Zariya gobe idan Allah ya yarda a gidan nan Zubaida zata kwana" da wannan Audu yayi musu sallama tamkar Malam Hassan ze bishi haka ya ringaji, bayan ya fito daga gidan su Zubaida harya dauki hanyar gida ya fasa kaitsaye ya wuce gidan Mai.

Full tank yayi, a nan ya tsaya yayi magriba ya dan ci abinci dan rabonsa da abincin kirki tun safiyar jiya kafin su tafi Zariya.

Musbahu ya dauka, Dan Yaya Baba ne daya dakko ya sakashi a gidan Mai yace yazo ya rakashi a daren ya dauki hanyar Zariya.

Musbahu ya ringa zare ido ganin inda sukaje, to me ya kawo su nan kuma.

Zubaida na bacci taji bugun qofa ta tashi ta bude mamaki ya cikata ganin Audu.

"Dama baka tafi ba?" Ta tambayeshi, ya kalli Musbahu kafin ya kalleta yace
"Ki hada kayanki Asubanci zamuyi na je na samu Baba kuma ya yarda ki dawo gida"
"Qaryane, yaushe kaje Kano har ka dawo nan?" Ta fada tana kama qugu, yayi gaba yana ce mata
"Qanwarki Surayya ta girma kamanninku daya tamkar Tagwaye"
"Innalillahi dagaske kaje gidanmu, kaha Innata me tace maka?" Ta fada tana fashewa da kuka tareda bin bayansa da sauri seya dakata yace
"Kije ki hada kayanki, mahaifinki na cike da zumudin ganinki na tabbatar yau baze iya bacci ba".

Washe garin kuwa Asubanci sukayi, shidai Musbahu bakinsa fal da tambayoyi amma babu me bashi amsa.

Har qofar gidan Malam Hassan ya isa da mota, tun daga nesa ya hangoshi zaune kan kujerarsa ya rafka tagumi gefe Aminan sa na jiya na tsaitsaye.

"Ina ga shine wancan" daya ya fada yana nuna motar dake tun karo su, Malam Hassan ya miqe jiki na karkarwa, Zubaida ta fashe da kuka ganin da gaske Mahaifinta ne tsaye qofar gida yanayinsa kuma ya nuna ita yake jira.

Audu kasa jure wannan yanayi na haduwar Uba da Ya yayi bayan wasu shekaru, be ko yi mata sallama ba yaja mota suka tafi.

"Wlh idan naji zancen nan a bakin wani nida kai ne" ya fadawa Musbahu sanda ya sauke shi a Gidan Mai.

Gida ya wuce, yayi tsammanin tarar da yaqi saboda fita daya sakeyi ya kwana amma se yaga akasin haka.

Bintan bata nuna damuwa kamar jiya ba daya shiga wanka ya fito ya tarar ta shirya masa abinci ya zauna kuwa ya nadi abinsa dan a yunwace yake yana ci amma zuciyarsa da kwakwalwarsa suna kan Zubaida ko me takeyi oho.

Binta kuwa abinda ya faru jiya bayan ya shiga wanka fita tayi ta tafu gidan Baturiya.

"Bari kiji, duk matar da kikaga ta isa to wayo, dabara, kissa da kisisinarta ya kaita.

Karki bata wayonki a gurinsa bayan kin rigada kin fara kafa gwamnatinki.

Wannan ihu da hayagagar baze saka ya fasa abinda yayi niyya ba amma cikin salo da dabara se kiga kin rabashi da koma wacece dan haka ki koma gida ki bashi haquri da sannu ki gano bakin zaren sannan muyi qoqarin daukar mataki, sannan banda abinki ai da kishiyar gida gara ta waje.

Kinsan duk Namijin daya saba zama da Mace biyu ma wuyaci ne ya iya haquri da daya dan haka in har ba so kikeyi ya aurota ya kawo miki ku zauna tare ba ki rabu dashi yayi sabgar gabansa" abinda Baturiya ta gaya mata kenan shiyasa ta dawo gida amma fa a zuciyarta bata jin zata iya jurewa kamar yanda tace mata amma zata gwada dauke kai dan kamar yanda Baturiyar ta fada tabbas da Kishiyar gida gara ta wajen.

Kusan sati daya da dawowar Zubaida gidansu kafin Audu ya sake zuwa, har cikin gida Malam Hassan ya saka ya shiga.

"Nayi ta neman inda zan zameka ashe itama ko sunanka bata sani ba, Yaro na gode, yanda kayi mun wannan Alfarmar ina fatan ubangiji ya jibanci lamarinka ya rabaka da iyayenka lafiya, nagode kwarai daka maidomun da Zubaida gabana, nagode daka zama silar barinta rayuwar barna" Malam Hassan ya fada daga nan ya basu guri shida Zubaidan dayaga tayi wani sanyi qalau tamkar ba ita ba.

"Nagode da abinda kayi mun Allah ya biya maka buqatunka na Alkhairi" tace daga nan sukayi shiru kamar kowannensu ya rasa abin fadi shi ya gaji da shirun yace mata
"Ina fatan abinda ya faru a baya ze wuce, ki cire komai daga ranki ki faro sabuwar rayuwa.

Abinda ya faru qaddararki ce kuma Imanin mumini baya cika har se ya yarda da qaddara me kyau ko mara kyau sannan, ina fatan hakan ya zame miki kaffara.

Sannan kuma ina nan akan bakana na neman yardarki, ina so da zarar kin kammala Istibra'i za'a daura mana Aure"
"Kayi haquri bana zaton na dace da nagartaccen Namiji kamarka, nagode da abinda kayi mun kuma in Allah ya yarda zan yita yi maka Addu'a Allah ya baka mace daidai da kai" ta fada cikin sanyin jiki.

Babanta na cikin daki yana jiyosu yayi gyaran murya yana cewa
"Wannan wace irin maganace Zubaida, kana jina ko Yaro kaje in Allah ya yarda bata da wani Miji idan ba kai ba.

Banda rashin wayo ki samu miji kamarsa har ki tsaya kinibibi ai yafiki sanin abinda ya dace dashi din kuma yace ke yake so"
"Shikenan Baba nagode, in sha Allahu kuma zan turo da magabata na e a tsaida magana".

Watanni uku bayan dawowar Zubaida gida, a hankali tun tana sharewa harta yarda ta sakarwa Audu fuska soyayya me sanyi ta qullu tsakaninsu, du
kda tana matuqar jin kunyarsa kasancewar yasan komai na rayuwarta ta baya, ta kanga kamar wata rana ze goranta mata bama shi ba babban damuwarta yan uwansa take zaton ya zasu dauketa idan har sukaji ita din wacece a baya gashi yace mata yana da mata ire iren wadannan tunanin yake sare mata guiwa taji kamar ma Auranta da Audun baze yuwu ba.

Watanninsu hudu tare Malam Hassan yace ya turo magabatansa saboda yana so ya hada da Auran Surayya ayi gaba daya, su uku suka rage cikin yaya shiga da mahaifiyarsu ta haifa ukun sun rasu suma bayan rasuwar Mahaifiyar tasu se Surayya da Ibrahim Wanda yake bin Zubaida ne suka rage masa be kuma sake Aure ba tun rasuwar Habiba shekara bakwai kenan.

Babu damuwar komai Kai tsaye Audu ya tafi Bechi ya samu Yaya Baba ya gaya masa cewar zasuje nema masa Aure nan da sati daya, mamaki ya kama Yaya Baba saboda Yakubu yaje Bechi ba'afi sati daya da tafiyarsa ba kuma beyi musu zancen Auran Audu ba dukda yaga alamar kamar Audun ma be san yaje din ba, tun rabuwar Auransa da Bara'atu abubuwa sukayi zafi tsakaninsa da Yakubu.

Yakubun Yayi fushi me tsanani shi kuma Izza da ganin yanzu ya isa ya hanashi ya neme shi su sulhunta.

Yaya Baba bashida ta cewa dan haka ya amsa masa da Toh, ya kuma sanarwa da sauran yan uwansu abinda ake ciki take Hashimu yace ba zashi ba.

Aminu ya samu Audu ya tambayeshi Yakubu yasan da magabar kuwa yace masa Aa.

"Wannan abinda kukeyi sam be kamata ba, kaine qarami dan haka ka nemeshi ku sasanta.

Me yasa kakeyin tufka kana warwara?

Kayi nasarar hade kanmu sannan kuma ka koma ka bata da Yayanka da kuke ciki daya akan Mace wannan wane irin abu ne?"
"To ni Aminu menene laifina a ciki, Shi ya fiya damuwa ne kawai idan ba haka ba menene nayin fushi akan na rabu da Bara'atu nifa nake zaune da ita ni nasan matsalarta amma shi ne da fushi dan na saketa?"
"Saboda yafika hango abinda yake daidai ne shi yasa kai kanka kuma da zakayi duba na tsanaki zaka gane abinda ake qoqarin fahimtar da kai.

Da ace zaka ji shawara da ka haqura da sabon Auran nan ka maida Bara'atu dakinta" Aminu ya sake fada.

Audu yayi shiru kafin ya kalle shi yace
"To kai ka aureta mana ko kuma shi din ya aureta tunda kun fini sanin darajarta".
https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE17*
Badan Audu yaso ba sedan Yaya Baba dayace muddin ba sanarwa da Yakubu ba bazasuje masa neman Aure ba tilas ya kirashi ta wayar Landilayin wadda ya hada a gidansa shima kuma Yakubun suna da ita a Ofishin da yake aiki dan haka ya kirashi.

"Allah ya sanya Alkhairi yasa ayi a sa'a" abinda Yakubun ya fada masa kenan bayan daya shaida masa zancen Auran se kuma yaji babu dadi dan haka yace masa
"Amma zaka zo ko?
Chapter 40 · 0% Book details