← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 226

Sashe 99

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Tana shiga ummu salma tace da ita
"Amira wai ina kika samu wannan babe din haka mai shegen class,wallahi tamun,ta burgeni da ganinta akwai nutsuwa"
"Ga kyau,muryarta ce ni kuma ta burgeni" inji hafsat,dariya suka bata,dukkansu 'ya'yan yar ummee ne,tasu ta bala'in zuwa daya da amira saboda halayyarsu kusan daya ce,ba ruwansu suna da matuqar kirki
"Nan fa gidan anty dije wadda ta muku fried rice da sunan hanan,a nan take"
"Masha Allah wallahi tayi"
"Ai baku ma san tayi ba sai mu da muka je gidansu...." Eesha da hassada ta cikata tace
"Me tayi,mr suke da shi a gidan nasu" amira wadda har ta sanya qafarta zata fita ta fasa ta dawo jin abinda eesham tace,dama tana lura da take takenta akan sumayya,wadda bata ga ita sumayyan abinda ta yi mata ko ta tsareta mata ba
"Basu da komai,amma suna da rufin asiri,suna da wadatar zuci,basu taba kuma roqon wani ba,baya ga haka suna da karamci kyautatawa da girmama baqo,wadan nan abubuwa sun basu komai na rayuwa koda basu da shi din" inji amira ranta a bace sannan ta juya ta fita ranta a bace,humaida ce wadda itama ke jin haushin abinda eeshan keyi ta dora
"Arziqi ba kudi bane eesha,wadatar zuci sanin darajar kai,mutunci yakana da karamci sune arziqin,kana da cin yau kana fa na gobe jibi wata ko shekara ma,kana sanya suturarka ta mutunci,baka taba roqa a baka ba,baka tashi ka rasa abin kaiwa baka me kake nema?"
"Kinga malama,ni ba wani nace mata ba da zaku isheni da dogon wa'azi,ha'an..." Ta qarashe tana jan tsaki,caaa suka mata sun fita yawa ala tilas tayi shiru.

A inda ta barta a nan ta taras da ita,suka ci gaba da takawa ba tare data nuna wa sumayyan akwai wani abu ba,bangaren anty maamaa suka soma shiga,itama bangaren nata masha Allah da mutane,suka gaisa sannan taja hannunta suka tsallake zuwa kitchen dinta,suna shiga tana yunqurin fitowa hannunta dauke da tray wanda aka jera tangaran mai garai garai guda daya wanda ke dauke da hadin salad mai kyau,sai wata qaramar butar shayi irin ta larabawa da cups dinta wanda ke dauke da baqin shayi wanda yasha kayan qamshi iri iri,su'ad ce,fuskar nan a hade tana faman kumburi,ko kunyar idon mutane bata ji,ta zama baturiyar qarfi da yaji,sanye take da dogon wando wanda ya kama jikinta da t.shirt mai gajeran hannu,kanta babu dankwali sai uban qarin gashi wanda aka dasa shi kamar nata na ainihi,ta sanya ribbom ta kameshi,takalmin qafarta kuwa irin mai igiyar nan je,wanda tsininsa ba kawai abun kallo ne,amma akace sabo da yi gawa da gatsine,da yake ta saba tafiya da abunta sam bai dameta ba,hannyenta kuwa farce ne wanda tasha nail polish,gefe suka janye bata ko kallesu ba ta wuce abinta,da kallo amira ta bita tana tabe baki kafin ta maida kallonta ga anty maamaa
"Kumburin banza kawai,shi wanda kike ma kumburin ma baisan kina yi ba,ba kuma ki isa kiyi masa a gabanshi ba,abincin ba bake zaki girki ba ki karba ki kai masa yaci kina baqinciki kamar da kudinki aka sarrafa,wallahi ni yanzu baiken ya musty ma nake gani,kana aure amma kamar ba magidanci ba,babu wani ci gaba da ka samu ko sauyi dangane da tsohuwar rayuwarka" daquwa anty maaman ta jefeta da ita tana fadin
"Sau nawa zan miki magana kan dauke ido daga rayuwarsu?,ke ke zaune da ita?,ko kinga ta kulaki sansa zata fita" shigin shagwaba amiran ke kumbure kumbure tana fadin
"Duk ku kuke sake bata su wallahi,ni da ganin wannan takacin gwara kayi aurenka ma kayi gaba a barku da su" dariya ma ta baiwa anty maaman sai ta dauke kanta tana duban sumayyan
"Qaraso amiran umman khalipha mu gaisa ki qyale wannan tuburarriyar qawar taki,rana iwar haka dai naga wanda zata yi mawa" dariya sumayyan ta saka itama tana qarasowa inda anty maman take,a ladabce ta gaidata tana tambayar yadda ta baro mutanan gidan,sai da suka gama gaisawa sannan tace
"Anty mama,bedroom dinki na bude,zamuga wadan nam kayan" kai ta kada mata suka juya suka fice.

Har bedroom din ta dangana da ita,aljannar duniya sumayya ta kira dakin,cupboard din antyn ta bude ta jawo wata akwati ta ajjiye gaban sumayyan,ta sake janyo wata ta ajjiye sannan ta fara hudewa tana fadin
"Ga kayan da zaki saka na biki baki daya,komai da komai,sarqa kawai zaki buqata bansan choice dinki ba" baki kawai sumayyan ta sake tana kallonta,ta soma ware mata wanda zata sanya gobe kamu,wani dandatsetsen lace ne brown mai yarfin milk wanda aka yiwa dinkin fitted gown,rigar ta dinku iyaka,sai takalmi milk na companyn vinci wanda ke da tsini dunduniya,sake dago wata doguwar riga tayi wadda ta tafi da imaninta,ire iren rigunan da baabaa ya basu da salla ita da laila mai dauke da tambarin companyn MM,itama da takalminta ruwan kwalliyar duwatsun dake jikin rigar tace wannan ta jibi ce ranar arabian night,sake janyo wani shegen yadi tayi wanda bata tantance wanne ba,baqi ne baki dayansa an masa ado da milk din zare tsalli tsalli da milk din qulalai a jiki,shima fitted gown ce,har tafi ta farko fitinuwa,sai wani shegen hill shoes mai igiyoyi ruwan adon jikin yadin da jaka purse mahadin kayan ga
"ankon dinner dinki" amira ta fada tana murmushi,rasa bakin magana kawai tayi tana duban amira,dariya ta sanya sanda ra motsa zata yi magana
"Wallahi idan kika ce wani abu sai mun bata,baabaa ne duka ya bada yace na zabi na dinkawa babbar qawata" kai kawai ta dinga kadawa kafin ta furta kalaman godiya,kunnuwanta ta tasihe da nufin bata son ji.

Daya akwatin kuwa baki daya kayan amarya ne da zata yi fitar biki,fadin irin kyawunsu ma bata baki ne,sai data daga mata su daya bayan daya sannan ta rufe ta maida ma'ajiyarsu tana cewa
"A nan zamu dinga shiryawa,don haka anan zamu bar kayanmu,sai muje kiga lefe dama baki gani ba" dariya tayi
"So kike dai dare yamin banje naga anty ba,ai basai na gani ba amira".
" shikenan,muje ki rakani na miqawa waccan kayanta,sai na rakaki qofa kije ki dawi din"fuska ta narke,ta langabe kai duk don amiran ta haqura da wannan rakiya
"Habbaaa amira,muje dai ki wuce ki kai mata ni kuma na wuce gida"
"Ke kika ce sai na amso mata dinkin ina zaman zamana,saboda haka dole ki rakani" tayi maganar tana gyara nadin mayafinta,miqewa tayi jikinta babu qwari tabi bayan amiran suka fice.

Daf da zasu shiga bangaren wanda ta baya suka biyo da yake qofofi biyu garesu,akwai qofar gaba wanda zaka shiga ta falo,akwai qofar baya wanda zaka shiga ta kutchen wannan qofar suka biyo,daga hannun hagu na bakin qofar,a qawace yake da wasu irin nau'in furanni da shukoki masu kaloli daban daban da kuma kyau,baki dayansu kansu daya babu wadda tafi wani tsaho,an qawata gun tamkar wani dan gurin hutawa,kaf gidan nan dinne kadai ke da irin wadan nan shukokin,wanda qilan mamallakin bangaren ne ya siyi abunshi yasa aka tsara masa su a haka,yara ne kusan su hudu,maza biyu mata biyu,a qiyasce zasuyi sa'annin juna baki dayansu,kowanne qananun kaya ne a jikinsa,sun kunna fanfunan suna ta faman wasan ruwa,amira ita ta fara hangosu,sai ta dakata tana daga murya
"Hibba!!,yayi muku kyau da wasan ruwa kunji ko" baki daya suka waiwayo suna dubanta,kyawawan yara ne wanda kallo daya zaka yi musu ka tabbatar jinin gidan baabaa prof ne,wadda aka kira da hibba ita ta matso
"Anty amira,gasar yin alwala muke,su hibban duk basu iya ba,zo kiga na fisu iyawa"
"Matsa ki ban gu,yanzu ban da lokacin shirmenku kinji,tawa ta isheni" sai ta karyar da kai fuskarta kamar mai shirin yin kuka tace
"Don Allah anty amira kizo ki gani" idanunta ta zaro tana dubanta
"Ina wasa dake ne,bakiga ina cikin hidima ba,matsa a wajen nace" sumayya na tsaye tana murmushi tana dubansu,yarinyar ta burgeta,zuciyar son yaranta ta motsa mata,dauke idonta yarinyar tayi daga duban amira ta maida kan sumayya
"Tunda ba zaki ba ai ga wata antyn ko?anty zaki je ki gani?"
"Me zai hana" sumayya ta fada tana murmushi,tsalle ta fara wanda hakan ya sanya sauran yaran qarasowa din jin me ya faru
"Ba inda zata,Allah hibba kin baci da yawa,itama tana da abunyi"
"A'ah,nifa sai naje" inji sumayya wadda dama hanyar kubuta take nema
"Kije ki fito kya sameni a nan" ta fada tana yin gaba din tuni yarinyar ta riqe mata hannu
"Anty muje waccan fanfon,wannan na uncle man ne,zai zanemu ya ganmu a gurin,amma idan mukayi kuka sai ya bamu chaculet yace mu daina" murmushi tayi kawai tace
"Allah"
"Allah anty,kuma duk yafi sona" hibba ta fada suna qarasowa wani waje wanda shima akwai fanfo saidai baikai wancan kyau ba.

Jin muryar yara ya sanyashi daga idanunshi daga kan laptop din dake gabanshi yana duba wasu sababbin design na dogayen riguna da kamfaninsa ke son fitarwa a sabuwar shekara,gefanshi butar shayi ce da cup qwaya daya,a rayuwarshi yana son ababen nan,yanayi na damuna irin wannan bayan gama saukar ruwan sama,da guri wanda ke da wadatar korayen tsirrai,iskar wajen mai dan sanyi sanyi kadan hade da qamshin qasa da qamshin furanni na masa dadi qwarai,ganin yaran tare da wata ya sanyashi maida kanshi yaci gaba da abinda yake.

Daya yaron ne ya tabe fuska yana cewa
"Qarya ne anty,yafi sona,ko za'a tambaya ma" yatsanta ta dora kan lebenta tana zaro masu idanu alamun yayi abunda ba mai kyau ba
"Bakasan ba'a cewa babba qarya yake ba,lala ba kyau,kace Allah na tuba" kan kunnensa kalaman suka sauka sai ya daga kai ya sake duban inda suke tsaye,har yanzu bai gane wace ba,amma yana iya gane yaran saboda baki daya yasan muryoyinsu,hannunshi ya sanya ya tsiyayi shayin ya kai bakinsa yana ci gaba da sauraronsu,a rayuwa Allah ya zuba masa qaunar yara,zama cikinsu yana debe kewanshi a duk sanda ya samu kansa cikin kewa,hakan ya sanya wani lokaci yakan bata lokaci cikin gidan marayunshi,akwai yaran da suka shiga ransa da dama a gidan,baisan so yaushe ne zai daina rayuwar kadaici ba.
Chapter 99 · 0% Book details