← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 226

Sashe 36

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana jin qarar tsaiwar motarsa ta miqe da hanzari ta shige dakin sumayyan,kanta tsaye ta nufi kan drower din ta kwaso magungunan dake ajjiye a kai ta riqe a hannunta tana kallon sumayyan taba murmushi sannan tace
"Yanzu zaki ga babban kaidina don na tabbatar bakisan da zaman wadan nan magungunan ba,baki ta saki tana kallonta tare da jijjuya kai cike da azaba,ko magana ma ta kasa yi,sai da taji takun shigowarsa yana qwala musu kira ta saki kuka tana jujjuyasu tare da matso hawaye tana fadin
"Me yasa kika aikata haka sumayya?,me yasa zaki raba shi da farincikinsa?,abinda ya jima yana nema sumayya shine yau zaki zama silar rabashi da shi,ina ma ni Allah ya bawa sumayya kin cika butulu ta gaske,wayyo Allah yau mun rasa yaronmu"sai ta rushe da kuka,wani duka zantukanta suka yiwa dodon kunneta,sai ta daga kai tana duban baki qofa saboda ganin inuwar mutum,take idanunta suka sauka cikin na mukhtar wanda ke dauke da tsantsar bala'in da bata taba katarin ganinsa cikin idanun nashi ba,tsaf mukhtar yaji duka abinda zainab din ke fada,yi tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da cewa
" yanzu har da maganin 'yan shaye shaye sumayya da tarbiyyarki da komai......
"Kasa ci gaba da daukar batun kunnuwanta sukayi,dummmm taji sunyi mata,a hankali ta soma jin jiri na kwasarta tana daga zaune,cikin 'yan sakanni wani duhu ya mamaye idanunta ta daina gani ta daina ji.

**** ***** *****

Sannu a hankali ta soma yunqurin bude idanunta har taci nasara ta kammala budesu baki daya,idanunta suja sauka kan ruwan dake rataye yana shiga jikinta sannu a hankali,take abinda ya faru da ita ya dawo mata tar,tayi hanzarin fadin
" la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin"bakinta ya furta
"Hmmmm,kamar gaske" muryarsa ta daki dodon kunnuwanta,da sauri ta waiga ta dubi bangaren da sautin ke fitowa,mukhtar ne tsaye hannayensa nannade a qirjinsa,duba daya zaka yi masa ka fuskanci a yamutse yake,har yanzu idanunsa jajur suke tamkar an badesu da barkono,kafin tace wani abu ya tako zuwa gaban gadon da take. Babu shakka da zata iya da tashi zata yi ta arta ana kare saboda yadda kamanninsa suka sauya baki daya kamar wani mayunwacin zaki
"Sumayya,ban taba zaton soyayya zata juye ta koma qiyayya ba sai yau,babu shakka kin cuce ni kin zalunceni,kuma Allah ya isa tsakanina dake,don bazan taba iya yafe miki ba,na zauna da ke tsawon shekaru ina kare martaba da mutuncinki,ina tattalin farincikinki ashe ni nawa kike rusawa,meye aibuna da bakison ki haihu da ni?,me yasa baki gaya min ba tun wuri nayi nesa da rayuwarki?,a yau na tsaneki tsanar da ban taba yiwa wata halitta makamanciyar irinta ba,na gani da idona ba gaya min akayi ba"zuciyarta na mata wata iriyar muguwar suya ta bude baki don kare kanta duk da rashin qwarin gwiwar da take da ita,sai ya watsa mata magungunan da kuma sakamakon gwajin da ka yi mata na dalilin barinta wanda ya nuna maganin zub da ciki ta sha
"Allah ya saka min sumayya na dora buri kanki amma kin zalunceni" abun mamaki kawai saiga hawaye na fita a idonsa,abinda bata taba tsammanin ganin ba agreshi
"Zan bar rayuwarki kije kiyi duk yadda kika ga dama da ita,KIJE NA SAKEKI SAKI UKU don bazan tab iya ci gaba da rayuwa da ke ba" wani tashin hankali ya rikito mata,sai ta ware baki daya idanunta tana son tabbatar da gaskiyar lamarin,ko dai barin da tayi ya shafi awaqwalwarta da jinta?.

"Haba my dear wannan danyan hukunci haka?,ai yayi tsauri" ta fada tana isowa gareshi cike da kisisina
*Dakata da Allah!"ya katseta cikin kakkausar murya,gabanta yayi mugun bugawa saboda ta tuno da sharadin da malam ya gindaya mata nacewa kada ta kuskura tace komai har a qare lamarin,saboda ba qaramin so yakewa cikin ba hakanan har yau duk da daurin da aka yiwa zuciyarsa da sanya masa ganin baqin sumayya har yau sonta na da sauran tasiri cikin zuciyarsa,itadai kawai ta sanya layarta cikin bakinta tayita taunawa,jajayen idanunsa da suka firgitata ya zuba mata
"Tunda sumayya ta iya yimin haka a rayuwa,to babu macen da zan aura ta kasa aikata min haka,saboda haka kema kije na sakeki saki uku!"
"Iyeee!" Ta fada cikin madaukakiyar murya fitsari na kubcr mata take ya fara bin qafarta saboda azabar rudewa,kai ya sanya ya fice daga dakin,wanda kammala fita su mama(babar sumayya) suka sanyo kai da alama dama suna cikin asibitin.

_kuyi haquri fa kawai ku ci gaba da bibiyata don cimma darasin dake cikin labarin da kuma rayuwar sumayya_

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣1⃣
________________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa bashshiris sabirin,Allazi a iza asabathum musibatun qalu innalillahi wa inna ilaihi raji'un*

_ka yiwa(ya annabin Allah) masu haquri bushara,sune wadanda idan musiba ta samesu suke fadin daga Allah muke kuma gareshi zamu koma_

*Allah ka sanya mu cikin wadanda zaka yiwa kyakkyawan sakamako sanadiyyar fadan wannan kalma*
_________________________________

      Zainab qanwarta ce akan gaba,sai mama da yaya abubakar halima na biye da shi,umma sadiya qanwar babansu na biye da su
"Yaya sannu yanzu muka ga ya mukhtar din ma ai ya fita" ta fada ba tare da sun ankara baki daya da yanayinda take ciki ba,haka ma basu lura da zainab dake tsaye gefe ba tana tsuma tare da kallon fitsarin da ya gama wanke mata qafafu. Kallo daya mamanta ta yi mata ta fuskanci ba dai dai taje ba duk da cewa akwai ciwo tattare da ita.

        Da idanu kawai take binsu tana fata ta farka daga mummunan mafarkin da takeyi,sai da maman ta qarasa gefan gadon ta zauna ta soma yi mata sannu sannan sumayya ta tabbatarwa kanta idanuntq biyu,a zahiri komai ke faruwa,wata cukuikuya ta yiwa maman nata tana sauke wata ajiyar zuciya tare da fadin
"Ya sakeni mama,ya rabu da ni bayan bani da wani laifi",cikin rudani suke kallonta duk suna zaton zafin ciwo ne
"Sumayya zafin ciwo ne duka hakan?" Sai ta fashe da wani kuka mai azabar cin rai tana maimaita fadin
"Walllahi mama ya sakeni,yanzun nan da kuka ganshi ya fita sakina yayi mama" salati suka saka baki daya wanda ya dawo da zainab hayyacinta
"Allah ya isa 'yarku ta jawo min masifa,ta jawo min zawarci kashi na biyu garin qoqarin zubar da cikinta" ta fada tana wucewa fuuuu ta bar dakin.

       Shiru ya ratsa dakin,babu wani abu dake tashi sai shashsheqar kukan sumayya wanda zainab da halima ke tayata saboda tsantsar tausayin 'yar uwarsy,yayin da zuciyoyin sauran ke quna,zancan zainab kuma ke musu kai kawo
"Mama har saki uku yaya mukhtar ya yimin,mama wallahi ban aikata ba,na fishi son naga na haihu mama ki......." Sai ta fara jan numfashi da qyar wanda hakan ya sanya su sake rudewa,da sauri yaya abubakar ya nufi reception don kiran nurse ko likita,cin qanqanin lokaci sai gashi tare da likita wanda yake gab da tashi Allah yasa bai fita ba,waje ya fid dasu baki daya sannan ya rufe dakin,take suka rude da koke koke cike da tashin hankali.

       Kusan mintina talatin sannan likitan ya fito bayan ya gama dubata ya mata allurar bacci tare da sanya mata wani ruwan,ya sanar musu bata buqatar hayaniya,sannan don Allah su guji tada mata hankali idan baso suke ta hadu da hawan jini ba,don ko a yanzun jini nata ya fara sama,bugu da qari kuma ta zubda jini mai yawa,godiya suka yi masa sannan suka koma dakin kowa ya samu gu ya zauna zugum,dukkansu da abinda suke saqawa zukatansu,daga bisani yaya abubakar ya fice dan yi musu siyesiyen abubuwan da zasu buqata kafin suga yadda hali zaiyi.

       Tun a hanya take sumbatu,ko da wasa bata taba zaton ramin da ta haqa zai rufta da ita ba,bata taba ganin masifa irin wannan ba,taga samu taga rashi,gidan da takewa kanta hasashen samun abun duniya yau dare daya an rabata da shi
"Ina!!!,wlh sam bazai yiwu ba,mukhtar ko baka qaunar Allah sai ka ci gaba da zama da ni,babu wanda zan sanarwa ma ka yimin saki uku,wallahi yanzu na fara aurenka" maganar da tayi kenan wadda ta sanya mai adaidaitam juyowa ya dubeta,banda kayan jikinta da basu nuna alamun akwai hauka tattare da ita ba da babu abinda zai hana yace mahaukaciya ce,a qofar gidansu ya sauketa ya juya ya kama gabansa.

        Tunda ya bar asibitin gida ya wuce kansa tsaye tamkar wani mahaukacu,kuka yake wiwi da haka ya kashe motarsa qofar gidan ba tare da ya samu qwarin gwiwar tura dan matsakaicin get din ba bare ya iya shiga da ita,dakinsa ya wuce ya fada saman gado yana dafe da kansa,me yasa sumayya zata yi masa haka?,wanne abu ya mata da zata saka masa da wannan?,zata rabashi da gudan jininsa,sata rabashi da burin rayuwarsa,shin ta manta cewa samun d'a shine CUKAR BURINSU shi da ita?,wani kukan ya sake saki kamar qaramin yaro,sai a lokacin ya fara ambaton sunayen Allah daya bayan daya,sannu a hanakali nutsuwa ta fara saukar masa,yabar tumurmusa gadon da yake yayi luf saman gadom cikin yanayin na kwanciyar rub da ciki idanunsa na ci gaba da fidsa qwalla masu zafi.

      ****    *****   *****

       Kwana daya rak amma sunfi kwanaki dubu ciwo da wahala a rayuwarta,baki daya ta sauya kamar ba sumayya ba,tayi wani mugun dashewa wanda ya sanya nurses suka soma tunanin tana buqatar qarin jini ko babu jini jikinta,da likita ya duba sai yaga magungunan qarin jini ma kadai sun isheta sai maida kai gun cin abin mai lafiya.
Chapter 36 · 0% Book details