← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 226

Sashe 122

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna zaune suna hira bayan sun idar da sallar azahar suka ji sallamarsa,sanye yake da jallabiya ruwan madara mai haske,kanshi babu hula sai takaddu masu yawa dauke a hannunshi,idanu suka hada da sumayya wadda ke amsa sallamarsa
"Hala batan hanya kika yi?,ko ba sumayya bace?" Ya fada tamkar da gaske yake,dariya suka bushe da shi baki dayansu har ita,ya qaraso ya samu gefan hajiya ya zube cikin gajiya yana ajjiye tarin takardun hannunshi abdallah ya maye gurbin takardun ya haye masa cinyar,surutu ya fara yi masa yana biye masa yayin da yake amsa gaisuwar halima
"Hala ke kika tuna mata da mu ko halima?matar da ko ki sanarmin zaki dawo nijeria banyi wannan matsayin ba" Ya fada yana dubanta,hararar wasa tayi masa sabida hajiya ta bar wajen
"Tunda ita ta tunamin sai na tafi sai na tuno don kaina sai na dawo"
"Ni kike harara?,lallai idanunki sai isa yanka" dariya ya bata suka dara sannan ya soma tambayarta gajiyar tafiya mutanen abuja da sauran abubuwa tana amsa masa,saidai ta kasa sakewa saboda wani kallo da yake binta da shi,hakan ya sanya babu shiri qarfe uku na rana tayi haramar tafiya,ko ya lura a takure take ya sanya ya sauke abdallah bayan ya kammala cin abinci yace
"Bari na shiga na watsa ruwa sai na zo na kaiku" kai kawai ta daga ba don taso ba,ta sani dole a yau akwai abinda zai faru,tana tsananin kunya da jin nauyinsa a yanzu,ba yadda ta iya tilas suka jirayi fitowarshi.

Cikin wani yadi ruwan omo ya fito,yayi kyau sosai,yace su sameshi mota sanda suka tsaya yiwa hajiya sallama,ta ajjiyewa hajiyan turare da turmin atamfa data siyo mata,sai wata qaramar jaka mai kyau mai garai garai wadda ke dauke da set na kayan makeuo data siyawa bahijja,murna sosai bahijja ta dinga yi,yayin da ta dauki mayafinta tace zata rakasu dama ta gaji da kwanciya ko zata ji qwarin jikinta,godiya sosai hajiyan ta dinga mata tamkar bata fi qarfin abun ba,dama shi alkhairi dadi gareshi koda wanda ka yiwa din yafi qarfin abun indai yasan karamci.

Duka baya suka shiga ita da shi ne a gaba,bini bini ya juya ya kalleta,wani lokaci su hada ido wani lokaci ta basar,bai dai ce komai bar zuwa sanda wani go slow ya riqesu,wasa wasa sai gashi suna shirin cin mintuna goma bai motsa ba,ga hadari ya soma haduwa ya sanya garin yin duhu duk da har yanzu bai fara zubda ruwan ba sai zafi da ake fama da shi,bata mantawa lokaci iwar haka suka bar nijeria lokacin damina sai gashu sun sake dawowa sanda take shirim kamawa.

Baki daya motar dake gefansu wajen guda uku sun rufesu kasancewar sunfi nasu tudu,sai ta sauke glass din motar qasa,abdallah dake sit din baya ya zuro hannunsa yana qoqarin sanya mata yoghourt a bakinta wanda hajiya ta bashi wai tasha,bata kai ga sha din ba ya zuba mata a jiki,baki daya ya bata saman cinyoyinta
"Ya salam,ya salam abdallah ka bata min kwalliyar mata" abdur rahman ya fada yana laluba gefanshi ya dauko ruwa a cikin jarka ya miqa mata
"Budr murfin motar ki dan wanke gefan da ya baci kafin mu qarasa gida" karba tayi ta balle murfin motar ta dan zura jikinta waje zata soma wankewa,ganin mayafinta na niyyar shiga ya shafa shima ya sanyashi sanya hannu yana janye mata,dai dai lokacin da motar dake daura da su aka sauke nata glass din wanda zafi ya ishi wanda ke zaune sit din baya,tsaki yaja mai qarfi saboda ko kadan baisan a.c din motar ta lalace ba,driven bai gaya masa saboda sabbabi ne ko wata daya basuyi ba,wannan ne kuma hawanshi na biyu zashu rano,yayi niyyar hawan jirgi kuma babu jirgin da zai tashi kano to abuja a irin lokacin da yake son ya taho din,hakan ya sanyashi hawa mota.

Kyakkyawan gani idanunshi suka yi masa,da fari ya dauke kanshi kasancewarsa wanda baison shiga sabgar da ba tashi ba amma sai qwaqwalwarsa ke gaya mishi kamar ya santa,sake maida idanuwansa yayi wajen,ita dince,gaban motar wani yana janye mata mayafi,ci gaba da kallon wajen yayi har ta kammala ta ta maida kanga ciki taja murfin ta rufe
"Yammatan yanzu?,duka sammakal suke ne?" Ya tambayi kanshi,sai ya danna madanni glass din ya koma ya rufe yadda yake,wani tsakin ya kuma ja,gwara ya yita shan zafin da idanuwansa su dinga shishshigi kan lamuran da ba huruminsa bane.

Sam bata ma san abdur rahman ya janye mata mayafin ba,ta kammala ta kiqa masa gorar tana masa godiya
"Ai yiwa kaine" ya fada yana murmushi,itama murmushin tayi don a yanzu ita ba qaramar yarinya bace ta fuskanci me yake fadi.

Fita sukayi dukansu har bahijja tace zata shiga ta gaida mama,bai hanata ba don yana da buqatar sararin da zaiyi magana da ita,kallonta yake har ta gaji ta tanka
"Kada fa ka cinyeni"
"Da hakan zai yiwu da nafi kowa farinciki,kinga idan ma cinyeki kin tabbata mallakina ni kadai har abada,wani ma bazai ganki ba bare ya qyasa" kunya kalamansa suka bata,saita maida kanta daya barin tana sauke murmushi
"Naga ma sai wani shamin qamshi ake,ko da yake girmanki ne,shekara kwana inji 'yan magana,ina maganarmu ta kwana sumayya?,nayi haquri sosai fa,dukkan kuma wani abu da nake saka ran kammaluwarshi ya kammala,jibi in sha Allah za'a bude asibiti,ya muke ciki,ko baki yarda ba wannan karon inajin ta qarfin tuwo zan qwace ki"
"Amma dai kasan ko budurwa bai halatta ayi mata auren dole va bare bazawara" ta fada tana dariya qasa qasa
"Kada ki yimin haka sumayya" ya fada a marairaice,ta jima tana nazarin abdur rahman din,bata da wata mafita yanzu,babu hanyar tsira,koda bata auri abdur rahman ba dole ta auri wani a gaba wanda bata san wayeshi ba,ta tabbata malam bazai barta ta rayu haka ba tunda har ya fara yi mata gugar zana,zata tanqwara zuciyarta,ta kwatanta karbarsa taga ni,bata san me gaba zata haifar ba,amma me mutane zasu ce idan sukaji zata auri dan wan baban mukhtar,wanda shi saurayi ne ita din bazawara ce?,wacce iriyar fassara zasu masu,meye matsayar hajiyarshi?,da wace fuska zata kalli batun
"Ka cancanta abdur rahman,bazan hanaka damarka da Allah ya baka ba,amma kamim haquri kada ka sanar da malam har zuwa sanda za'a kammala bikin zainab,na tabbata idan ka gaya masa yanzu zaice zai hada da ni ne,wanda ya kamata kafin sannan ace mun sake fahimtar juna kan zaman da zamu tukara da tsara abinda ya dace" hannunshi ya dunqule kawaj saboda tsabar farinciki
"Amincewa da yardarki kawai ta isheni farinciki,na godewa Allah,bazan takura ki ba ki kammala shirinki a nutse,amma don Allah a yimin alfarma nayi azumim bana a dakina"ya fada a marairaice,dariya ya bata har sai data qunshe bakinta,wai a dakinsa sai kace wani mace
"Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi"
"Amin ya Allah,ki shiga ki sauya kaya ki huta naga kaman yoghourt din dake jikinsu ya hanaki sakewa,bazan iya shiga gun mama ba kunyarta nakeji kinsan ta zaka suruka,sai gobe insha Allah zan kawo musu katin gayyatar bude asibitin shi da yaya abbakaf,ki turon bahijja" ya fada yana sanya mata kudade a jakarta,kudi sam ba matsalarta bane yanzun amma tun kafin tace komai yace baiso tace komai din,tilas ta dauki jakar tana masa godiya ya bita da kallo har ta shige gidan wani madaukakin farinciki na ratsashi.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣9⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*KU SHIGO CIKI KUJI*

*ALLAH YANA FADA CIKIN QUR'ANINSA MAI GIRMA*

*MISALIN ALJANNAR DA AKA YIWA MASU IMANI ALQAWARI,A CIKINTA AKWAI QORAMU  NA RUWA WANDA BAI JIRKITA BA,DA QORAMU NA NONO WANDA DANDANONSA BAI SAUYA BA,DA QORAMU NA GIYA WADDA TAKE MAI DADIN DANDANO GA MASU SHA(WADDA BATA SAKA MAYE KO TAMBELE),DA QORAMU NA ZUMA TATACCIYA,KUMA A CIKINTA SUNA DA(SU 'YAN ALJANNA)NAU'IN KOWANNE IRIN KAYAN MARMARI(DAN ICE)*

*kai jama'a wannan ni'ima da yawa take,idan kaso ka zama TATACCEN QASAITACCEN DAN GIYA AMMA FA NA ALJANNAH,ya Allah ka sanyamu cikinta don rahamarka*
________________________________________

       Kafin su kai ga fita daga airphort din ruwan sama ya sauka,hakan ya hadu da duhun magariba ya kawo qarancin jama'a bisa titi,idanuwan sumayya qur bisa kwalta yadda ruwan ke sauka yana wanketa,a duk sanda ruwam sama zai sauka sai ya mata tunin mukhtar kamar ko yaushe.

        Rashin daukewar ruwan har suka isa gida shi ya sabbaba driban ya shige da su baki daya cikin gidan baaban ba tare da sumayya ta samu damar sauka ba kamar yadda taso,saboda Abdallah wanda ya jima da yin barci kan cinyar amira,ruwan na iya tabashi,da ita daya ce da da sauqi.

       Lema kubra ta shiga ta dauko musu sannan suka fito,suka taka har cikin gidan.

     Lallai kam wannan biki ba qarami bane,baki daya harabar gidan ko ina an kafa tempol,duk da gidan bai wani cika rana ba,duk da ruwan da ake tsulawa hakan bai hanaka ganin mutane na kai kawo daga wannan sashi zuwa wancan sashi ba,a haka suka qarasa bangaren ummee,falonta cike yake da baqi,yan uwa qawaye da abokan arziqi,ga 'yan rano nan wanda ko ba'a gaya ma ba kana kallonsu kasan jinin ummee ne,jinin sarauta,ga 'yammata nan ko ina zazzaune kowa na nashi harkan,shigar amiran ya sanya hanaklin sh dawowa kanta,masu tsokana nayi masu mata barka da dawowa nayi,da qyar ta yakice suka hau falon sama na ummee wanda tana can.
Chapter 122 · 0% Book details