← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 182 OF 226

Sashe 182

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kansa ya haura saman don kiran sumayyan suje su gaida baban,umme ta gaya mishi tana daya dakin tare da su farida,sanda ya shiga anty farida na toilet,huda ta shiga kitchen damawa yaronta madara,sai amira dake zaune kusa da sumayyan wadda ke rabawa husna gashinta tana daure mata shi suna hirarsu qasa qasa da amira da alama gulma suke,turo qofanshi ya dakatar da su,idanunsa har yau a kanta,da idanu ya yima amira alamun ta fita,tsam ta miqe
"Koma ki dauketa" ya nuna mata husna da ido,komawa tayi ya dauketa daga cinyar sumayya ta fice,bata motsa daga inda take ba sai ta wayance ta karkade jikinta duk da ba wami qura ko gashinda ya zuba,ta soma hada qananun ribbom din dake zube qasa tana maidawa cikin ledarshi,gabanta ya qaraso ya tsugunna,ya riqe hannunta tsam dake tattare ribbom din,sai ra dagi ta dubeshi da fararen idanunta
"Shariya?.....ni zaki dinga sharewa haka?,hmmm lallai yarinya bakisan waye almustapha ba" zuciyarta ta karye,wani irin qaunarshi lokaci guda taji tana kutsawa cikin zuciyarta,kallon da yake mata kadai na dabanne,zuciyarta ta raurawa wanda batasan dalili ba,ta shagwabe masa ba tare data shirya ba
"Ni kuma?.....me kuma nayi?"sai tsugunan ya gagareshi ya zauna sosai a gabanta
"ki tashi da safe baki neme ni ba ki fice binki?,kiyi breakfast abunki duka babu ni?,kin daina damuwa da ni ko?"
"Ni vance haka ba sai kai zaka fadi?" Ta furta a zuciyarta,ta bude baki zatayi magana qofar bandakin ta bude,anty farida ce ta fito,ganinsu a hakan ya sanyata qara mai ta fice a dakin
"Ya man abun ya motsa kenan,yanzun ne ake baje kolin da da ba'a baje ba" take gulmarshi cikin ranta a haka ta qarasa dakin umme tana tuntsirewa da dariya
"Me haka lafiyarki?'ummee ta tambayi farida
"ba komai ummee,eata soyayya na gano ana bajeta yanzun nan" shiru ummeen tayi tana ci gaba da sabgarta,don ta gane inda zancan ya nufa.

"So kake naje na buga muku qofa?,ko so kake na yi ma abinci ba ranar kwana na ba?"
"Ko?" Ya fada yana dage mata gira tare da kallon lips dinta da suka burgeshi,shiru tayi ba amsa,tana qoqarin sadda kanta ya riqe fuskarta,sai da ya tsotsi lebunan son ranshi sannan ya kamata ya miqar tsaye
"Muje mu gaida baba",yana tsakiyarsu haka suka jera,kowacce da abinda take ji cikin ranta.

Ranar kusan wuninta tayi wajensu huda,sai da yammaci laila tazo da su khalipha harda hafiz,nan ta dinga kwasarshi
" kai kam hafiz rashin son jama'arka ya baci wlh,yanzun sai yau zaka zo gurina"dariya yayi
"Kiyi haquri anty sumayyanmu" basu bar gidan ba sai wajen gab da magariba,bayan laila ta bawa sumayyan saqon da anty dijen ta kawo mata.

Washegari gidan anty dijen ta yiwa tsinke,da qyar ya barta,sai da hamza ya kirashi zasu fita sannan ya mata tattaki har qofar gidan ta shige,sosai taji dadin wunin wajen antyn,ta rabauta da sirrika masu yawa,da kanta ta baiwa antyn kudi a sake kawo mata dilkar nan saboda yadda ta karbi fatar jikinta,saidai a sanyaye ta dawo gida saboda albishir da antyn tayi mata na cewa uncle farouq ya sanyi gida zasu tashi daga nan,hakan ya daga hankalinta,amma abun alkhairi ne ci gaba ne ya samesu dole ta tayasu murna.

Sanda ta dawo gidan gimbiya su'ad na zaune a falon qafa daya kan daya,an tsuke ana danna waya,yayin da ma'aikatan ta da aka dawo mata da su suke kitchen suna girka abincin dare,ko sallamarta bata amsa ba,itama bai dameta ba tunda ba zamanta take ba,ta wuce dakinta kai tsaye abinta,sai data gama duk abinda take sannan tayi wanka,sallar magariba ta soma yi,ta shirya cikin riga da skert na atamfa,tana son atamfa har cikin zuciyarta,lite make up tayi ta murza daurin dankwai sannan ta fesa turare,ta dubi kanta a mudubi yadda fatarta ta sake kyau,juyawa tayi ta fice a dakin don shiga kitchen ta samarwa kanta abinda zata ci kafin akira isha'i,tunda kowa zai dinga girkinsa ne shi da mai gidan ranar girkinsa.

Har yanzu tana falon zaune,saidai wannan karon ta sauya kayan jikinta,riga da wandon ne amma fari da yellow,fukarta radam da makeup,tsaki ta jiyota ta ja sannan ta furta
"Villager,always atamfa atamfa,thats d problem of arewa women" maganarbummee na kada ta soma yarda suyi cecekuce ta fado mata,don haka ko ta waiwayo ta dubeta batayi ba bare ta nuna taji abinda take fada,bata da lokacin cecekuce sam tana tunanin ta wuce wannan babin,a da can zamanin da take da qananun shekaru ma bata yiba ballantana yanzu?,daqiqi shike maimaita aji amma ba mai qwaqwalwa ba,kai tsayi ta nufi kitchen,gab da zata shiga qofar tata kitchen din ma'aikatan suka fito sanye da unifoarm da warmers da suke shiryawa wajen dining,a ladabce suka gaisheta,ta amsa musu fuska sake tayi gaba,tana jiyo ashariyan da su'ad ke dura musu saboda gaidatan da sukayi
"Uban wa ya dauko ku wa kuke wa aiki?,zaku koma inda kuka fito wlh duk randa naga wata na mata wani abu,talaka talaka ciwon kai ne wallahi" kai ta gyada tana mata fatan shiriya,ita sam mai aiki ma bata burgeta bata cikin tsarinta,idan bata tashi ta yi hidamawa gidanta ba daga wayewar gari zuwa faduwar rana to meye amfaninta?,taci ta kwanta tayi bayan gida?,idan ya cika akwashe?,abinci mai sauqi ta dora cikin tukunya mafi qanqanta a cikin tukwanenta,cikin kitchen din ta zauna hannunta harde a qirji tana tunani kadan kadan har ta kusa kammala ta juye ta fito.

Tana fitowa a kitchen din yana shigowa falon,da ita ya soma tozali tunda tana tafiya ne zuwa dakinta,boyayyen murmushi ta saka tana son basarwa,saboda duba daya tayi masa ta karanci tsantsar gajiya tattare da shi,batasan ina hamza ya jashi ba dai yau kam,ido daya ya kashe mata alamun na ganki ne zamu gamu,ta kauda kai tana masa sannu da zuwa,yana amsawa ta kutsa kai corridor dinta abinta ta barshi da su'ad wadda ta taso da dan hanzari tana tsammanin wajenshi sumayyan ta nufa,murmushi ya sake mata kamar yadda ta sakar masa,saidai baki daya rabun hankalinshi na gun sumayyar,wayoyinsa ya miqa mata ta karba yana kama qugunta
"Kinyi kyau" ya furta yana kallonta,idanunta ya juya kanta na kumbura,a duniya tana son taga ta fifita fiye da kowa,tana son taga tafi kowa,sama suka haura tana zuba masa yauqi.

Turus yayi sanda ya dubi bathtube din yaga wayan babu ruwan wankan da ya sanya ran samu ciki,yana daga bandakin ya qwala mata kira,ta ajjiye wayarta da take dannawa ta amsa cikin qosawa ta miqe,tunda ta dawo ta tsiri chart da qawaye da abokai tunda yanzu ba'a kusa ba kuma ranar komawa,da idanu ya mata inkiya da bahon wankan sai ta tambayeshi me yake nufi
"Ruwan wanka" hannunta ta yarfar sannan ta taka a hankali ta soma tara masa ruwan
"Ka fara zama sangartaccen,naga da kai ke hada ruwan dear da kanka ko?,gaskiya an bata min kai" ta fada sanda ta duqa yadda bazai iya gano fuskarta ba taba hade rai
"U can go if you can'nt do it"
"Sorry" ta fada cikin wani salo,yana tsaye har ta gama hadawar ya zare towel dinshi ya shige,ruwan ya masa zafi amma bai tanka mata ba ya miqa hannunshi ya kunna famfon ruwan sanyi ya saisaita zafinsa.

Hannunshi riqe da cokali yana dubanta har ta gama zuba mishi ta zauna a gajiye
"Kai,wai dama haka hidimar aure take?,dole mata su dinga cewa aure akwai wuya" ta fada tana langabe kanta tana dubanshu,haushi bai barshi ya tanka mata ba,sai yaja plate din kawai gabanshi ya sanya cokali ya fara ci,duka duka me tayi yau din?,zai iya lissafa dukkan abinda tayi da yatsun hannunshi
"Dearrrr" ta fada a shagwabe
"Ni zanyi feeding dinka nima yau"ware hannyenshi yayi sannan ya ajjiye cokalin,ta matso cikin zumudi ta soma bashin,ci kawai yake,sai yake jin akwai banbancin dandano mai girma tsakanin girkinta da wannan girkin,hakan ya ma su'ad daidai yadda take bashi abincin ya mata dadi,saidai zata so ace sumayyan na wajen,don itama ta cusa mata haushi
"dear ka kira ta mana ko akwai abinda yayi mata a nan ta diba?" Hakan ya burgeshi,sai yayi zaton hankali ta soma,ba musu ya janyo wayarshi ya kirata.

Wayar na hannunta tana neman number malam tunda ta kira ta mama bata shiga ba,gaidashi take sonyi,tunda ta zubo abincin taji ta kasa ci,baki daya cikinta ya cushe bayan yau ba wani abun kirki taci ba,a nutse ta daga kiran ta amsa,to tace sannan ta miqe,sai data sake tsayawa gaban mirrow ta sake shafa hoda ta mutstsika turare sannan ta fito,idanunta ya sauka kansu sanda take kai cokalin abincin bakinsa,da hanzari ta dauke kanta zuciyarta na bugawa,sai ta dinga karanto la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalilm,tana gayawa kanta matarshi ce,kema kinyi gabanta,so meye itama don tayi,dubanta yake sanda take takowa,fuskarta sake da murmushi har ta iso,dadi ya kama su'ad,sai ta sake tura plate din gabanshi tana ci tana bashi
"Sannunku,wai *our man*, wannan abinci sai da ruwa ko anty na,let me help you" wani kallo ya jefeta da shi mai cike da ma'anoni masu tarin yawa sautin muryarta dab da kunnenshi na ratsashi,,salon maganar kadai abar burgewa ce,sumayyan ta balle murfin gorar ruwa ta tsiyaya cikin cups guda biyu ta tura gabansu
"Thanks" inji almustapha
"No thanks,albarka" murmushi ya sake yana hadiye lomar bakinsa
"Allah yayi albarka,ga abinci wai ko zaki ci?"ya fadi cikin ginshira da ajjiye kowanne lafazi d'ai d'ai,Sai ta soma bude warmers din,ba abinda ya bata sha'awa,ta qarshe ce taga farfesun zallar tsoka da kayan lambu,sai ya bata sha'awa har da hadiyar yawu,sam bata so ci ba amma sai ta tsinci kanta da zama sosai ta sanya plate ta dibi gwargwadon wanda take tunanin zata iya cinyewa
"Wannan ya isa" ta fada tana duban su'ad wadda take jin wani abu ya tokare wuyanta,sam wannan dabarar batayi ba,me zata yi mata ne ta huce?
"Na gode anty" ta fada tana sakar mata murmushi,don ta tabbatar ba'a banza tasa aka kirata ba,akwai wata a qasa,koma meye ta tura mata aniyarta,juyawa tayi a nutse ta wuce abunta zuwa dakinta,ba haka su'ad sam taso ba,taso taga zallar bacin rai baqinciki da kishi idanunta,idan da hali ma ta tanka ayi bacin rai,kuma daga bisani ta janye almustapha su wuce sama,hakan ya dagula ranta,fara'arta da walwalarta ya ragu sosai har suka kammala suka bar wajen.
Chapter 182 · 0% Book details