← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 226

Sashe 116

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

       Da murmushi baabaa ya masa nuni ya iso har gabanshi,ya sanya masa ludagi cikim furar da yake sha,kasancewarsa yasan almustaphan da son fura,kadan ya sha saboda qagara da yayi da jin dalilin zuwanshi nijeria cikin qanqanin lokaci,sai da baban ya kammala ya kira anty maamaa ta kawo masa wayarta ta fita sannan ya soma magana da shi
"Almustapha,kowa na da labarin bayyanar tsohon abokina sule ciki kuwa har da kai nasan labari ya isa gareka" qaramin murmushi ya saki don har ga Allah ya taya mahaifin nashi murnar ganin wannan amini da tun haihuwarsu suke ji labarinsa sai a yanzu ya bayyana,kai yake jinjinawa yana murmushi,yana zaton malam zaice ne yaje ya gaidashi
"Almustapha ungo nan" ya fada yana miqa masa wayar anty mama,babu musu ya sanya hannu ya karba yana duba wayar,hotonta ne,daya daga cikin hotunanta na bikin amira,ta fito tayi tar ta cika screen din wayar fuskarta qunshe da murmushu da ya sake fidda sigarta mai sanyi da kyau,janye wayar yayi daga fuskarshi yana duban baabaa,gabanshi na faduwa yana addu'ar kada Allah yasa baabaan yace ya auri wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar ne,amsar wayar baabaa yayi sannan ya dora
"Nasan maiyiwuwa zaka iya ganeta,yarinyar dake gidan farouq maqotanmu na abuja,diya ce ga aminina sule?,almustapha" ya sake kiran sunanshi cikin yanayi na gaske,fararen idanunshi kawai ya daga ya dubi baaba
"Na nema maka aurenta saboda mutuncinta,na nema maka aurenta saboda nutsuwarta,na nema maka aurenta saboda addininta,na nema maka aurenta saboda daga gidan data fito daga tsatson data fito,uwa uba na nema maka aurenta saboda TA DACE DA KAI!" baki daya kalmar baabaan ta qarshe taso tafiya da majiyar kunnensa,bai gama lalubo duniyar da yake ciki ba yaji wani sautin na cewa
"Ta taba aure tana da yaro daya,tana da hankalin da zata iya zama da kai ta baka dukkan abinda ya kamata" ai wannan karon bansan sanda ya daga kai ya dubi baabaa ba,take wasu irin jijiyoyi suja fito a goshinsa,qoqarin danne zuciyar tasa yake da irin bala'in da yake ji cikinta amma bakinsa yaqi bashi hadin kai
"Baabaa,ban santa ba,bata sanni ba,bata sona bana sonta,baabaa aure yanzu?,auren ma na bazawara da d'aa baabaa,please baabaa i beg you idan na maka wani laifin ne ka yimin duk wani hukunci da ya kamata amma banda wannan"murmushi baban ya saki
" ba hukunci bane mustapha gaata ne na maka"
"Gaata baabaa" ya fada cikin nuna shakku da taraddadi
"Baabaa ba wannan gatan nake so ba baabaa ka sauyan wani umarnin zanbi amma banda wannan" nan ya shiga roqo iri iri yayin da baabaan ya zuba masa idanuwa yana kallonsa,yasan dole za'a samu rudani amma bai tsammaci abun zaya kai haka ba,ganin yanata zuba ya sanya baabaan daka masa tsawa
"Muhammad almustapha!" Sunan da ya kira shi da shi yasanya hankalinsa dawowa jikinsa
"Ni muhammad mukhtar!,indai ni na haifeka na baka umarni ka karbi auren sumayya umarni ba shawara ba,tashi ka bani waje!" Da qyar ya iya miqewa kamar wanda ya sha abun maye ya lalubi hanya ya fice.

     Ya jima zaune gefan gadonshi aqalla awa guda yana yamutsa hannayensa cikin kwantacciyar sumarshi mai santsi da laushi,gumi ko ina yana keto masa,miqewa yayi ya soma zare kayanshi yana jefarwa cikin dakin,sai da ya rage saga shi sai boxer sannan ya fada bandaki,ruwan sanyi ya sakarwa kansa tsakiyar shower,ya jima tsaye sanyinbruwan na ratsashi tare da qoqarim control din kansa,ya sake barnatar da awa guda cur a haka har sai da tunaninsa ya dawo yadda ya kamata,qwaqwalwarsa ta fara yi masa bita,ya tabbatarwa kansa bai yi kalaman da suka dace ba ga mahaifinsa,baabaa ne,masoyinsa,wanda qaunar da yake masa ta daara ta dukkan wani daa ko jika dake cikin zuriyarshi,dakin gadon ya dawo ya sake lalubar wasu kayan ya sanya,wannan karon jallabiyya ce,ya gabatar da sallar la'asar,zama yayi kawai yana karanta yadda wannan QADDARAR ta fadowa rayuwarshi a lokacin da bai zata ba,yana nan a haka bai ankara ba yaji kiran sallar magariba,a nan gun itama ya yita a haka isha'i ta ruske shi,sai a sannan ya samu qwarin gwiwar miqewa ya sake daura alwala ya sanya hular tashi ka fiya naci ya nufi masallaci.

       Sahunsu daya da baabaa,har aka idar bai motsa ba sai da ya ga baabaan ya gama addu'o'inshi ya miqe zai fita sannan ya mara masa baya,yana gaba yana binshi a baya,baban ya san da haka amma yayi banza da shi bai ko nuna ya ganshi ba,sai da zai bude qofar gidan yayi sauri ya bude mishi yaci gaba da binshi har sanda ya isa falonshi sannan ya waiwayo yana sake tamke fuska duk da yasan dama hakan zata faru,yasan halin mustaphan zai sake waiwayowa a duk sanda nutsuwarshi ta dawo jikinsa
"Lafiya kake bina,zan shiga na kwanta ne idan akwai bashin da kake bina ban kammala biyanka ba sai ka gayan ko?" Kai ya sadda yana jin nauyi da kunyar maganar da baabaan ya fada,qarasawa yayi gabanshi sannan ya zube kan gwiwarsa
"Kayi min afuwa baabaa kayi haquri kan baata makan da nayi,nayi kuskure wanda bana fatan sake yinsa,na amshi dukkan hukuncin daka yanke me kake buqata yanzu daga gareni" dawowa yayi ya samu waje ya zauna sannan yayi masa nuni da ya dawo kusa da shi ya zauna,sosai baabaan ya dinga kwatanta masa manufofi da hujjojin da yake jin sun isa su sanyashi qara aure,daga bisani ya rufe
"Ka gwada zama da ita mustapha na cika maka baki tare da kurin samunta fiye da yadda kake zato ko tsammani,nasan jinin sule ba zai taba kasa gadon halinshi ha,mustapha,ka riqemin sumayya da mutunci da amana,idan ka wulqantata ka dauka ni ka yiwa,haka idan ka bata daraja,bazan iya maka afuwa ba aduk sanda na sameka da lafin wulqantata ba bisa haqqi ba"
"Na yi maka alqawari insha Allahu"
"Allah ubangiji ya albarkaceka,yq cika makq burikanka,ya kyautata rayuwarku kai da ita baki daya,kiran da nayi maka kenan zuwa nijeria,yaushe zaka dauki matarka?,sannan a ina kake son ajjyeta?"
"Duk yadda kace baba haka za'ayi" murmushi ya saki yana dukan kafadarsa
"Kaine fa mijin kuma kai ke aurenta bani ba da zaka turon zabin"
"Ka isa damu ne baki daya baba"
"Idan ta nine ko yau kaje ka dauko matarka,sannan ka wuce da ita dubai,don nima ina son naga daana ya fara dandanar zaqin aure" duk da rudin da yake ciki maganar baban ta qarshe sai data sanyashi jin nauyi
"Zanyi yadda kace,amma amin afuwa zuwa gobe"
"Ba lallai bane ai,kana iya barinta abuja idan kaso,amma sai bayan kun gama fahimtar juna da ita kun fara sabawa,fatana ka riqeta da mutunci"
"Insha Allah baaba" addu'a yayi masa mai kyau da tsaho,wanda tilas mustapha ya dinga lallaba kansa da zuciyarsa ya zauna sukayi hira da malam din na wasu mintuna sannan ya tashi ya wuce.

       Kamar zai zauce cikin dakin shi daya haka ya dinga ji,kiran hamza ya shigo wayarshi,wata bahaguwar harara ya ballawa wayar,ganu yake hamzan ne da shegen bakinsa ya masa wannan fatan,to amma ai ba fatan hamza bane tunda baifi awanni da yi masa shi ba,anya kuwa hamza baisan da wannan maganar ba ya munafunceshi?,yana kallon kiran har ta ya gaji da kiran nasa ya haqura,yana tsagaitawa lambar su'ad ta danno kai,wanda shi sam yama mance da ita,ya kuma mance rabon da suyi waya,hannu ya sanya cikin mutuwar jiki ya daga kiran ya kara akunnensa,tun kafin yace wani abu sheshsheqar kukanta ta cika kunnuwansa wanda hakan ya hadu da tashin hankalin da yake ciki take suka saukar masa da ciwon kai,sai ya runtse idanu yana saurarenta
"Almustapha,ni zaka ci amana?,ni zaka yaudara almustapha,dama zakq iya kqllon wata mace macen ma 'yar afrika bayan ni?,almustapha kana jina kayimin banza da kai nake musty!" Ta fada cikin qaara da qaraji,tasan sarai yana jinta tafi kowa sanin halinshi na rashin son hayaniya da kuka,shirunsa ya sake tunzurata,mamanta dake gefe ta rada mata abinda zata yi,itama a ganinta hakanne ya dace tunda da irin wannan taci nasarar aurenshi
"Wallahi almustapha sai na kashe kaina,sai nasha poison don bazan iya hada ka da wata can ba,wallahi sai na kashe kaina....." Ga mamakinta tun kafin ta kashe wayar shi ya kashe,bama kashewa kadai ba sai da yaja mata wani mugun tsaki sannan ya kasge wayar baki daya ya cillar,miqewa yayi cikin tangadi ya sauya kayan bacci ya koma gado ya duqunqune cikin bargo,yayin da qwaqwalwarsa ta kasa aikin komai a tsaye take cak.

   ******   ******   *******

      A shirye ya fito cikin baqaqe sidik three pieces slim fit suit,ba qaramin kyau suka yi masa sun haskashi matuqa,saidai shi kadai yasan izayar da yasha daren jiya,tilas ya dauki sun glases wada ya dace da shigarsa ya sanya,tamkar don ado ya sanyashi ba don kare idanunshi da suka sauya launi ba saboda rashin wadataccen bacci yayi masa kyau sosai shima,ya yanke shawarar gwara yaje asibitinsa ko wasu daga cikin marasa lafiyan da zai iya dubawa ya duba ko hakan zai rage masa zafi da radadin da yake ji.
Chapter 116 · 0% Book details