Sashe 134
Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da suka fara tafiya a titi sannan mahmoud ya dan zunkuda kadan,tun dazun daya tsinci maganar ake mintsininshi,so yake yaji shin abunda yake zato ne?
"Am....baba daurin auren waye kuma nan da sati guda?" Waiwayawa baabaan yayi ya dubeshi sannan yace
"Yayanku almustapha in sha Allahu" idanu suka waro mahmoud yace
"Shi da wa?"
"Diyar sule aminina sumayya mai sunan mama na" ya basu amsa kai tsaye,duk sai kasa furta komai,babu abinda ke yawo kansu irin halaye da tsare tsaren yayan nasu almustapha wanda babu wanda baisan halayyarshi ba,shin baabaa na shirin daura masa aure kenan baida masaniya da yarinya 'yar afrika?,
"Yarinyar tayi,tayi wlh bata da makusa,ga nutsuwa ga hankali,koni a lokacin da na soma ganinta don dai kawai akwai alqawari tsakanina da rahma da tuni na saka kai" ya fada yana dan kauda ido waishi kunyar baabaa,murmushi baban ya saki,idan da sabo ya saba da irin wannan barkwancin tsakanin mus'ab da mahmoud,yaso ace haka halayyar mustaphanshi take kan barkwanci,saidai kowa da yadda Allah ya tsara masa halittarsa,suna hira da raha sosai da shi,sun maida shi tamkar kakansu,yabon da ya sake yi kan sumayya ta sake faranta masa rai,kafin ya sake cewa komai mus'ab ya muskuta yace
"Hmmm,dan gaban goshi,auren gata wannan karon za'a masa,yana can yana harkokinshi an nema masa aure,mu kuwa gamu nan tamu maganar ma ko ya ake ciki ne mahmoud?" Ya maida tambayar kan mahmoud,dole dariya ta qwacewa baabaa saboda salon yadda mus'ab din yayi furucin,daquwa ya watsa masa sannan ya dafa kafadarshi
"Kai ka jawo tsaiko da karatunka bai gama kammala ba,amma ku din ma ba zaku wuce nan da wata biyar ba" sai suka saki dariya kuma suna jin kunya,su kamsu sunsan yayan nasu yana buqatar dauki,sunsha rayawa a ranau idan sune ba zasu iya wannan auratayyar ba,saidai da yake maza ne babu wanda ya gayawa dan uwanshi ko suka zauna suka tattauna batun,saidai kowa yayi shida zuciyarshi,da haka suka qarasa gida ko zuciyarshi fes.
****** ******** ******
Washe gari tun tara na safe suka gama shirin fita ci gaba da shirye shiryensu,sabida a yau sumayya keson su gama rabon i.v saboda ta gaji,gashi uwa uba kuma so take da anfarawa zainab din gyaran jiki kada ta sake fita,tuni anty dije wadda yau tare zasu fita ta iso,tana wajen malam suna hirarsu ita da shi da yaya abubakar wanda yau bazai fita kasuwa ba ya taho gidan hira,amina ma na nan zuwa anjima don kusan gidan take wuni tunda satin bikin ya kama,sai da suka kammala sumayyan ta leqa falon malam din tana fadin anty dijen ta taso su tafi sun gama shiryawa don ma nafisa ta tsaidata ta tsaya amsa kiranta wadda ta tabbatar mata zata halacci bikin zainab,don zata zo kano dama gaida iyayen mijinta mahaifan auwal
"Jeki ki kira min babarku ku taho tare ke da ita" inji malam,haka kawai taji qirjinga ya buga,tashin farko jikinta yayi sanyi,ta juya zuwa bakin fanfo inda maman ke daura alwalar sallar walha ta gaya mata,qafafunta kawai ta kammala wankewa ta bita suka nufi dakin.
Sai da suka samu gu suja zauna suka nutsu sannan malam din yace
"Haqiqa na tabbatar da cewa duk wanda ya kwana ya tashi cikin gidan nan yasan abun farincikin da muka kwana da shi na bayyanar aminina,to bayan mun gama farinciki na ganin juna muna hira bayan ke sumayya kun shigo kun fita ya bijiromin da wata buqata,na sani kun san cewa duk da baku taba ganin muhatari ba amma kunsan muhimmancinsa gareni da irin shaquwa da halaccin da yake tsakanina da shi,ya bijiromin da wata buqata wadda na tabbatar yagi qarfinta a wajen iyalina,duk da nasan cewa haqqin sumayya ne amma na amshi buqatar hannu bibbiyu saboda nasan cewa na isa da ita sannan ba zata taba watsan qasa a ido ba" tun kafin yaci gaba qirjinta ya fara wata iriyar sukuwa,kanta yayi nauyi ta kasa dagashi,maganar da sukayi da shi kafin tahowarta kano da fassarar da anty dije tayi mata suka fara dawo mata daki daki
"Ya nemi na bawa yaronshi auren sumayya bisa wasu hujjaoji daya zayyanamin wadanda sun isa sun kai baya ga matsayin muhtarin a gurina a bashi auren ita sumayya,saboda haka na bada auren sumayya ga yaron nashi wanda za'a daura auren ranar juma'a tare da na zainaba insha Allah" wani kuka ne ya qwace mata wanda sautinsa yaso fitowa tayi hanzarin sanya hannu ta rufe bakinta,
"Alhamdulillah" kawai anty dije ke jerowq,kamar ta tashi ta taka rawa haka ta dinga ji,ta kasa zama waje daya sabida farinciki,ba shakka tana mai tabbatarwa kanta sumayyan tayi kyakkyawan gamo mai dauke da dumbin alkhairai
"Kiyi jaquri sumayya,na miki shishshigi,saidai ina mai baki haquri tare da neman alfarma kan ki yimin wannan alfarmar kada ki watsan qasa a ido" maganar malam din ta hadu ta sake yi mata nauyi a ka,duk da halin ha'ula'in da take ciki amma haka ta tattara kalaman
"Don annabi ka daina fadan haka malam,ka daina bani haquri,ni bani da wani da na cancanci a nemi alfarmata a kansa,kaine silata kai ka haifeni,duk yadda kayi da ni malam daidai ne,na tabbatar ba zaka taba cutar da ni ba,na amince na miqa wuya a gareka,roqon da nake maka kadai shine malam ka bini da addu'a,ka sakani cikin kowacce addu'a taka,Allah ya qarfafeni,ya hanani gazawa bare na watsa maka qasa a ido,na samu juriya mai yawa da zata kaini ga cika burinka" tana kaiwa nan ta gaza dairewa,sai ta fashe baki daya da kuka zucuyarta na tuna mata abubuwa masu yawa,wadanda suka faru da wadanda kan iya samunta a gaba,fata take Allah yasa SHAFUKAN KUNDIN QADDARARTA sun qare ashe akwai wasu sabbin shafukan kar a gaba,sai yaushe ne zata kammala bitar wannan kundi mai dan karen wuya da sanya zuciya da gangar jiki yin rauni,rauni kuwa bana wasa ba,ya barwa zuciya da rayuwa tabbai masu wuyar warkewa,masu wahalar sha'ani da sarrafawa tare da tanqwara zuciya a kansu,duk wanda ke dakin jikinsa yayi sanyi,sunsan mai take tunawa
"Insha Allahu sumayya daga wannan karon ba zaki sake kuka ba,da yardar ma duka lokacin dariyarki ne yayi,na tabbatar da cewa ban kaiki imda zaki wulaqanta ba,na kaiki ne cikim ahalin da suka gaji karamci da mutunci tun daga tushe,ko bana raye ina da yaqinin muhtari ya isheki uwa da uba ma baki daya,addu'a kuwa kullum kina cikin addu'o'ina,zaki rabauta sumayya da yardar Allah,tashi kije,Allah ya albarkaceki da dukkan wani abu da ya shafeki"
"Amin" baki daya mazauna dakin suka amsa,sai ta kasa tashi saida anty dije ta kamata,kai tsaye dakinta ta kaita ya zaunar da ita sannan ta zauna gefanta tana kallon yadda take kuka kamar hawayenta zai qare,bata cemata ta tafas ba har sai data soma tsagaitawa don kanta,bawai don ta gaji bane ko ta samu sassaucin da take son samu,ta tsagaita ne saboda yadda idanunta suka soma radadi da kuma yadda ta fuskanci antyn nason tayi magana da ita
"Sumayya kuka kike saboda auren almustapha?" Ta jefa mata tambayar kamar wadda batasan batun ba
"Na tabbata bakisan waye almustapha ba,banda haka da sai nace kukan da kike kin yiwa Allah butulci" jajayen idanunta ta daga ta kalleta alamar tamabaya,ciki yaqini anty dijen ke kada kai
"Tabbas abinda na fada hakan yake,kinsan irinsu mustapha suke tsada a wannan lokaci?,kinsan yadda mustapha ya tara managartan halaye kuwa?,kin taba tambayar kanki me yasa su'ad ke tsananin kishinsa duk da kishin banza take tunda batasan yadda zata riqeshi ba?,kin manta waye baabaa da karamcinsu?,kina zaton idan kika qi aurensa zaki ci gaba da zama haka ba tare da kinyi aure ba?,kinwa kanki wadan nan tambayoyin?" Kai take girgizawa bayan ta gama sauraronta,cikin rawar murya ta soma furta
"Anty a fuskata almustapha bashi da kirki,bai taba kyautata min ba ko sau daya,anty...kin manta yadda auren soyayya ke kayawa a wannan zamanin ina ga irin wannan?,baki daya almustapha anty ba ajina bane kamar yadda nake nima ba ajinsa bace,babu dacewa tsakanina da shi anty,komai nawa da nashi ya sha banban,ra'ayi yanayi al'ada wayewa da dabi'u,ta yaya zamanmu zaiyi daidai,baya ga haka ma baki daya anty KISHIYA!,kishiyar ma irin su'adah,kin manta anty ina kika baro wannan?,kin manta kishiya duk inda na shiga itace babbar qalubalena,bayan bansan me na musu ba,ko don ni yarinyace?,ko din bani da qarfin qwatarwa kaina 'yanci,ko don ban iya mugunta da baqin hali ba,wadan nan sune dalilan?" Ta fada wasu hawayen masu dumi na bin kuncinta,hannunta anty dije ta riqe tsam cikin nata,madadin taga tashin hankali bisa fuskarta sai taga murmushi ne ma kwance kan fuskarta
"Almustapha?,ko ba haka bane sunanshi?,kin manta shi namiji ne?,namiji kuwa ko wayeshi ta bangaren zamantakewar auratayya dole ya sakarwa mata,ki manta da wannan ki cire rashin soyayya a tsakaninku a matsayin matsala,kishiya ita kike tsoro?,ina zaton zuwa wannan lokacin kin horu sumayya,meye yayi saura meye bakiji baki gani ba,sai d'ai d'ai,wannan karo ki sama ranki cewa kishiya ga gama yin nasara a kanki da yardar Allah,waccan karon ma dan dai kawai yana cikin KUNDIN QADDARARKI ne,ke mai bawa wata labari ne,dame kishiya zata tsorataki sumayya,bayan kina da Allah,kina da tsarkakakkiyar zuciya,ke matuqar su'ad ma ta baki tsoro sumayya ke kika so,ki kwantar da hankalinki damuwa ba taki bace,bakisan sirrin da Allah ya boye ba har ya turo baabaa dai dai wannan lokaci,bana son qara ganinki hawayenki daga yau" Kai kawai ta gyada mata ba don tana tsammanin samun salama cikin ruhinta ba,komawa tayi kawai ta lafe kan gado kanta na sarawa,ita kadai tasan me take ji,kai kawai take mirginawa tana jin nauyi da girmam zancan a qirjinta,su halima da zainab ne suka shigo a sanyaye saboda ganin yanayin sumayyan,antyn tace suje kawai ba zata samu zuwa ba ita da sumayyan,bata son ta tafi ta barta a yanayin da take ciki,wayarta dake gefanta tayi ruri,kiran abdur rahman ne,idanuwanta ta runtse tana kiran sunayen Allah,sai a sannan ya fado mata,me zata da shi?,me zata gaya masa ya yarda da ita,tabbas bata da abinda zata ce masa,hakanne ya sanya ta qyale wayar taci gaba da rurinta har ta katse don karan kanta,qarar wayar kawai qara mata ciwon kai yake,wanda zuwa lokaci wani zazzafan zazzabi ya rufeta ta kwanta sosai,saidai bata bari kowa ya gane ba.
****** ******* ********