← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 226

Sashe 20

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

           Sumayya ce ta fara fitowa,cikin tashin hankali taje dubansu idanunta a waje,dambe da yaya yahanasu?,tab,lallai fa'iza ta kai,dakin mukhtar ta nufa da hanzari tana mamakin me ya hanashi fitowa,ga mamakinta yana tsaye bakin window yana kallonsu,saidai idanun nan sun kada sunyi jazur,a hankali ya juyo ya zuba mata su,itama sai jikinta yayi sanyi,tausayinta ya kamashi,babu shakka wata jarrabawa ce ta fado rayuwarsu,idanunta suka cika taf da qwalla ta tausayin mijin nata,sai kawai ya saki labulen ya taka a hankali ya fita tsakar gidan,wata gigitacciyar tsawa ya sakarwa fa'iza dake tsakiyarsu tana cin na jaki wadda tsawar sai data sanya hanjin sumayya hadewa ya cure guri guda,ta runtse idanunta tana jin ruguginta na ratsa kunnanta.

         Nuni kawai ya yiwa fa'iza da hanyar dakinta yana mata wani irin kallo mai cike da tsana,ba musu ta wuce jikinta na rawa,ya juya ya dubi yaya yahanasu sai kawai ya kamata yayi dakin sumayya da ita.

          Bakin rijiya ta zauna,sai ta kasa daurewa idanunta ya shiga fidda qwalla,wannan wacce iriyar masifa ce lokaci guda,duk wani farinciki da zaman lafiya na gidansu yayi qaura lokaci daya?,tana share hawayen idanunta tana tausayin mukhtar dinta.

           Tana zaune a nan mukhtar din ya fito ya shige dakin fa'iza,a nan ne ta jiyo tashin muryarsa saidai nan din ma bata ji duka abinda yake fadi ba,daga bisani ne ya fito,ta miqe tsaye ta isa gabansa tana kallonsa,tabbas taso ace yau ranar girkinta ne,ta lallashi mukhtar din,saidai sam bata da wannan damar,karyar da kai tayi murya a tausashe tace
"Kayi haquri don Allah yaya mukhtat,komai na duniya mai wucewa ne,jarrabawa ce daga Allah" murmushin qarfin hali ya saki ya shafi gefan fuskarta
"Babu komai my sumy,kije ki kwanta,kuma ban lamunce ki sanya abun cikin ranki ba,ki kwanta kiyi bacci sosai" ya sanya bakinsa yayi kissing  goshinta,sai ya bata kunya har ta dan murmusa,yana tsaye har ta wuce dakinta sannan ya juya nashi.

           Ko da ta isa dakin tuni ta taras da su sun rarrashe kan gadonta,sai yaya yahanasu dake zaune gefan gadon tana huci,abinda take da buqata ta dauka zata fice taji sakin qwafar da yaya yahanasu tayi,ranar kan doguwar kujerar falo ta kwana,saidai tayi qoqari kamar yadda mukhtar ya buqace ta tayi bacci ta qoqarta tayi na 'yan awowi.

*******************

        Cikin kwanakin gaba daya mukhtar ya fita harkar fa'izan duk da cewa daman can ba shiga yake yi ba,saidai duk wani abu da yake haqqinta ne kansa yana sauke mata bakin gwargwado.

           Zaman yaya yahanasu a gidan ya dauki sabon salo,wani irin zama ake a gidan,sosai yaya yahanasun kejin haushin fa'izan gami da ganin baikenta tun farko data daure gindin dan uwanta ya zama miji gareta,sai dai kuma duk da wannan bai hanata jin haushin sumayya ba,gani taje tamkar itace ta shiga tsakaninsu.

          Duk kwanan duniya gari na wayewa da zarar mukhtar din ya sanya qafa ya fice itama fa'izan ke ficewa,ba zata dawo ba sai yaba gab da dawowa koda kuwa ranakun girkinta ne,sai a sannan zata tsiri girkin dare shima tsoron hukuncin mukhtar din ya hau kanta take,ba qaramin horata yayi ba lokacin da ya amshi maqullin locker din abincinsa daga hannunta ba,da rana kuwa saidai kowa tashi ta fishsheshi,shiga su jamila suke kitchen kansu tsaye su girka duk abinda suka ga dama,su din ma ba baya bane wajen iya barnar abinci da ta'adi,sam ko sau daya sumayyan bata taba daga kai ta dubesu ba bare ta gwadawa mukhtar abinda sukeyi cikin gidan,dakinta kam tuni ta sallama musu shi,ta dauke kai baki daya da shi saboda yadda suke abinda suka ga dama cikinsa,wani abun da gayya da gadara suke mata,koda bata tankasu ba sukan bude baki suce "kayan dakin da kudin dan uwansu aka sauya su" sau tari dariya abun yake bata,ta kuma godewa Allah da ya sanya iyayenta masu rufin asiri da zuciyar yiwa iyalinsu ne,suma sun san da haka,babu shakka da Allah kadai ne yasan halin da zata tsinci kanta ciki,hatta da kayan sawarta sai suka fara dauka dai dai da dai dai suna sanyawa idan zasu fita wata unguwa ko biki,ranar da mukhtar ya soma gani ransa ya baci matuqa,bai iya jurewa ba sai da ya kirasu ya musu jan kunne.

            Ganin haka ya sanya mukhtar yace ta debe duk wani abu nata mai amfani ta dawo da shi dakinsa,ya bude ma'ajiyarsa ya adana mata ciki.

            Fa'iza kuwa tsakaninsu da yaya yahanasun da yaran ma baki daya sai harare harare da baqar magana,wanda yawanci ma sunfi yi da jamilan ko sayyada,bata san me mukhtar ya gaya musu ba amma da alama shi ya kawo wannan dan qaramin sauyin da aka samu.

          Cikin wata d'aya kacal mukhtar ya kammala musu gyaran suka tattara suka koma nasu gidan,ko a ranar da zasu tafi din ma sai da ka kusa kwata ta ranar da suka zo din,da zagi suka rabu,ba qaramin qona ran yaya yahanasun abun yayi ba ganin mukhtar din ya gaza daukar kowanne irin mataki,abinda bata sani ba shine ya fita jin takaicin abinda ke faruwar,saidai ya riga da ya tsarama ransa sai sun gama d'aukar darasin rayuwa tukunna.

*********************

           Qarfe takwas na dare ya iso gida tun bayan fitar da yayi da safe sakamakon aiki da suke a shagon sa na kasuwa,sosai yake a gajiye tiqis,saidai yasan cewa abu mafi muhimmanci shine ya adana gajiyarsa,matuqar fa'iza ke da girki babu wani abu da yake iya tsinta ko ya dorar a wunin ranar baki daya,qarin gajiyarsa machine dinsa yau da ya masa tsiya ya baroshi gun bakinike ya tari adaidaita ya iso gida.

         Babu wutar nepa a unguwar tasu hakan shi ya sabba ba duhun da gidan yayi,sai hasken fitila daga dakin sumayya dakin fa'iza da kuma kitchen din gidan.

           Bashi da sha'awar yin tozali da fa'izar ko kadan,saboda haka ya bude dakinsa ya shige da zummar zuwa ya rage kayan jikinsa ya koma bayi ya tanadi ruwan wanka,hular kansa ya cire ya jefata saman gadonsa,ya balle maballan rigarsa ya zareta ya ajjiye sannan ya nufi window dinsa ya yaye labulen don ya bawa iska damar shigowa.

            Kamar wanda aka kira idanunsa suka sauka kan kitchen,fa'iza ya hango,da farko yayi niyyar dauke kansa,saidai wani abu da ya hango shi ya ja hankalinsa,idanu ya zuba sosai don yana son ya tabbatar da abinda idanunsa ke gane masa,baiso yayi hukunci bisa kuskure zato ko tsammani.

            Sakin labulen yayi sannan a hankali ya fita izuwa kitchen din cikin takun sanda,bakin window ya isa sannan ya lafe daga jikin bangon yana kallon komai tar kamar yadda idanunsa suka soma nuna masa daga cikin dakinsa,yana tsaye harta sheqe da dariya sannan tace..............

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣8⃣

______________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*innal laha huwar razzaqu zul quwwatil matin*
______________________

"Mukhtar!,mukhtar!!,hmmmmm" haka ta fadi sannan ta maida murfin food flask din ta rufe tana ci gaba da dariyarta cike da nishadi da jin dadi.

A hankali ya zare jikinsa,cikin tafiya ta sand'a kamar yadda yazo haka ya koma,bakin gado ya zauna ya dafe kansa da dukkan hannayensa biyu,zuciyarsa na rawa saidai baiso ya bata dama,oh Allah!,tun yaushe?,tun yaushe ya fara turawa kansa wannan qazantar?,me ya samu yaya yahanasu ne har udanunta suka rufe ta kai ga nannade hannu zata jefashi ramin halaka?,me ta gani ne wai gun fa'iza ya burgeta har ta nemi suyi tarayya wajen hada zuriyya.

Sallamarta ta katse masa zaren tunaninsa,ya daga kansa wanda idanunsa suka kada jazur ya dubeta,tayi ado yau cikin shadda koriya sgar,bakin nan ya sha jan jambaki tamkar ya digo,zai iya rantsewa da Allah yau ne karo na farko da zai iya cewa ya ganta tayi wata aba mai suna kwalliya tun bayan qare kwanakinta bakwai na amarci.

Wani kwarkwasa na musamman yau din take masa,wanda dai dai da qwayar zarra bata qara farashin qaunarta cikin zuciyarsa ba face rageta ma da tayi,haushi takaici da baqinciki suka cika shi amma yayi namijin qoqarin dannewa
"Sannu da zuwa yaya mukhtar,yau kam ka jima baka shigo ba,Allah ya sanya lafiya" ta fada tana zama dab da shi tare da kashe masa ido,tausar zuciyarsa yayi don yana son ya ga gudun ruwanta,don idan baka iya kama b'arawo ba shi sai ya kamaka,tsawon zamansu duk iya inda ya kai darensa indai ba a dakin sumayya bane to shi ta shafa bata da damuwa,koda wasa bata taba tambayarsa ba
"Lafiya lau" ya fada yana miqewa tsaye,sai ta dubeshi gabanta na faduwa tana fatan ba asarar aikinta zai mata ba yau ma dai
"Ina zuwa yaya mukhtar gashi na shirya maka abinci?"
"Wanka zan shiga nayi" ya fada bayan yayi kamar bazai amsa mata ba,ta miqe tana fadin bari ta hada masa ruwan wanka sai ya dakatar da ita kan ta jirashi.

Kai tsaye dakin sumayya ya shiga,tana kwance saman doguwar kujera hannunta riqe da wayarta tana kallon wani film 'DAN KUKA,dariyarta take mai sanyi a hankali cikin nutsuwa,ya jima tsaye kanta yana dubanta cike da qauna da burgewa har sai da ya sanya hannunsa ya zare wayar sannan ta miqe a firgice tana ambaton
"Bismillahi,hasbunallahu wa ni'imal wakil" sai suka hada idanu,ta shagwabe fuska cikin muryar shagwaba tace
"Kai yaya mukhtar wallahi ka tsoratani" girarsa qwaya daya ya dage mata
"Eh amma naji dadi da kika ambaci sunan Allah yayin da kika tsorata din,haka akeso" murmushi ta danyi,duban screen din wayar yayi ya tsayar da film din,cikin shagwaba shima yace
"Wato yau ko ki nemeni ko my sumy?,hala ma kin daina damuwa da ni,kina nan kina kallonki kina ta dariya abinki bayan bakiji shigowar sahibinki ba ko?"idanu ta zaro tare da dafe baki sannan daga bisani ta hade hannayanta guri guda alamar roqo
" ka yimin afuwa don Allah,wallahi kewarka ce ta dameni shi yasa ma kaga ina rage lokaci da kallon,ai kasan yaya kallo ba damuna yayi ba ko?"ta qarasa maganar da sigar yarinta,idanu yasa yana kallonta sosai,babu shakka yana daya daga abinda ke sake rura qaunarta cikin zuciyarsa wannan shagwaba da quruciya tata,murmushi ya sakar mata
"Na miki sumayya ta,ai baki laifi a gurina" ya fada yana miqa mata wayar tate da cewa
"Zan shiga wanka"
"A fito lafiya ranka ya dade"
"Allah yasa my sumayyata" ya fada sannan ya juya ya fice yana murmushi.
Chapter 20 · 0% Book details