← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 192 OF 226

Sashe 192

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*wata rana annabi S A W yazo wucewa ta wasu* *qaburbura guda biyu,sai yace da sahabbansa*
*"haqiqa(mutanen dake cikin kabarin) ana musu azaba,ba kuma wani* *babban abu bane yasa ake musu azaba* *saidai(ma'abocin kabari daya)ya kasance baya suturtuwa daga fitsari,amma dayan* *SHI KUMA YA KASANCE YANA YADA ANNAMIMANCI"*

*sadaqa rasulul karim*

*qalubale ga munafukai,qalubale ga masu daukan zantukan wancan bangare su kaiwa wancan,su dauki naka su kai wa wani bangare,qalubale ga masu haddasa husuma,masu qiren qarya don su haddasa husuma da rigima tsakanin mutane,qalubale a garesu baki daya,GA MAKOMARKU NAN,RUWANKU KU GYARA RUWANKU KUCI GABA*

*FITINA AKWANCE TAKE ALLAH YA LA'ANCI MAI TADA TA*

*FADA CE TA MA'AIKI*

*ABINDA KUKA SHIRYA BAI YIWU BA,SAIKU SAKE SABON SHIRI,NI DA MAMUHGHEE DUKA BA JAHILAI BANE,MAIMAKON SHARRI DA KUKA SO QULLAWA SAI ALLAH YA JUYA ABIN YA ZAME MANA ALKHAIRI,GODIYA TA TABBATA GA ALLAH*

*ubangiji na cewa*

*YAKU WADANDA KUKA BADA GASKIYA DA ALLAH,IDAN FASIQI YAZO MUKU DA LABARI,TO KUYI BINCIKE KADA KU AFKAWA WASU MUTANE CIKIN JAHILCI/RASHIN SANI,SAI KU WAYI GARI KUNA MASU NADAMA AKAN ABINDA KUKA AIKATA*

*HAQIQA DUK WANDA YAYI AIKI DA UMARNIN UBANGIJI BA ZAIYI DANA SANI BA,MUN GODEWA ALLAH DAYA SA MUKA KASANCE CIKIN MASU IMANI*

*ALLAH KA SHIGA TSAKANINMU DA SU,KA FI KOWA SANIN BAMA NUFIN KOWA DA SHARRI,TSARKAKE ZUCIYARKA SAI ALLAH YA KUBUTAR DA KAI*

*muna muku fata Allah ya shiryeku,don wannan mummunan ciwo ne kuke dauke da shi,ciwon dake iya dawwamar da bawa cikin azabar kabari*

*ALHAMDULILLAH*
_______________________________________

           Shiru ne ya ratsa dakin,bata sake cewa komai ba,kamar yadda shima bai sake cewa komai ba har ya gama mata gyaran ya hade mata shi waje guda,tana kwance lamo tunani kala kala cikin zuciyarta,har ga Allah bata marmarin binsa,ba don komai ba saboda ta horu cikin abdallah,tana tsoron sake faruwar wani abun,su da zasu tafi can wata qasa wata uwa duniya,wazai tallafeta idan wani abu ya sameta wanda bata fatanshi?,shi da ba zama yake ba,ko yaushe aiki aiki?.

         Washegari ya sake birkice mata,sanda suka je gaida su baba da ummee,ya sanar musu komawarsu ranar lahadi kwanaki uku masu zuwa,ita dinma ummen so take ya barta nan cikin ya sake qwari tukunna,baya ga haka tana tunanin haukar su'adah kada ta yiwa sumayya saukarsa,tun sanda ta yanki almustaphan take jinjina batun,dannan daga bisani itama tazo raiwa kanta illa,to wayr ba zata iya yiwa ba kuma?,hakan ya sanya kamar tasan zaizo da zancan tafiya ta gayawa baba shawararta,yayi na'am da hakan,don shi kansa tsarin yayi masa,ya wuce da su'ad din ya bar sumayyan bayan wata biyu yazo ua dauketa.

       Sanda ummee ke rattabo masa bayanin kanshi na wasa,kusan tare suka daga kansu gaban sumayya na faduwa,kada fa yayi zaton qararshi ta kawo kan ba zata bishi ba?,da hanzari ya daga kanshi yana duban ummee,a hankali ya motsa bakinshi
"Amma ummee nan da can din duka daya ne ai,zata samu dukkan kulawar data dace"
"Ba daya bane almustapha,ka barta nan ta sake koyon yadda zata kula da kanta,a can fa kada ka manta bata da kowa..."
"Amma ummee tana da ni" ya amsa ummin bako kunyar nan fuskarshi,hankalinshi a tashe yake,kawai yadda zai tafi ya barta yake kwatantawa,ji yake sam ba mai yiwuwa bane
"Munsan da kai din ai,awa nawa kake zama a can din....kaga...magana ta wuce tashi ka tafi,kada ayi visa da ita" a hankali ya miqe bai ko dubi sashen da take ba,duba daya zaka yiwa fuskanshi kasan yana cin fushi,ya juya a nutse ya ficea binshi,binshi tayi da idanuwa kamar zata sanya kuka,bacin ran data gani kawai saman fuskarshi ya daga hankalinta
"Amirah" taji ummi na kiran sunanta,da sauri ta maida hankalita wajen tana amsawa
"Kada ki damu kinji,rabu da shi,ciwon 'ya mace na 'ya maca ne,kina wannan halin na yau lafiya gobe babu ta yaya zaki tafi inda baki da mataimaki sai Allah,qyaleshi ko yayi fushi zaya sauko,ni nasan bazai iya fushi dake ba" maganan ummin ta qarshe ta bawa sumayya kunya,sai tayi qas da kanta tana amsawa da to,duk da haka zuciyarta bata nutsu ba.

       Sallamar amira kamar wadda aka jefo ita ta katse maganan da ummi ke gaya mata,da gudunta ta kwaso bata zube gaban kowa ba sai sumayya,ruqunqumeta tayi tana cewa
"Wayyo matar yaya na,kin biyamu wallahi,Allah jiya kasa bacci nayi,labarin yazo mun katsam,anty farida ce ta gayamin,sai naga gari kaman da gangan yaqi wayewa don kada nazo na ganki" kunya ta kama sumayya,zungurinta take kan tayi shiru amma ina amira ma ba fuskantarta take ba,ganin yadda kunya ta kama sumayya ya sanya ummi miqewa tsam ta basu waje,ummi na fita ta dalawa amiran duka a cinya,wajen take sosawa tana dariya
"Ba komai,wallahi koda zafi ni banji zafin ba,bakya laifi ai ko kin kashe dan su'ad" dariya suka bushe da ita baki dayansu sannan sumayya tace
"Kefa iskancin naki ma naga sabon lasisi kukaje ke da saifu aka yi masa,antyn take ma kin daina anty saidai su'ad gatsal,ke kin isa ki kashe mata daa ba sai tayi gunduwarki ba" dariya ta sake saki harda tafa hannu
"Wa ya gaya miki son 'ya'yan take,ai ni tuni na san da wannan.....ke mubar zancan waccar.....amiran umman khalipha da gaske anty farida take?"
"Shafa kiji" ta bata amsa tana hararta,dariya ta saki
"Ai wlh duk wanda ya kalleki yasan da magana.....amma fa kin rame da alama kina shan jiki....Allah ya raba lafiya,kai Allah ya nuna mana wannan rana,zamu karya qugu da kwankwaso"
"Ki komawa saifu a gurguwa ko?"
"Ba komai sai ayi maleji......can na gano mai dakin naki"
"Amira baki da mutunci,waye mai dakina"
"Waye banda yaya maan,waishi kuwa har yau bai daina wannan shegen dacin ran nashi ba,na gaidashi ko amsani baiyi ba ya figi mota ya fice kaman wanda aka yiwa dan banzan duka?" Shiru sumayya ta danyi,wato a fusace yake kuma cikin fushi ya fita kenan
"Ranshi ne a bace amira"
"Haka kullum yake"
"Malama ki kiyayi zagarmin miji a gabana......" Ta fada tana hararta,dariya ta saki sosai harda kwantawa qasa
"Ikon Allah....yau da bani da aure da nasha haushi,gayamin me akayi masa"
"Anqi din" ta fada tana tureta
"Habba....nice fa ta hannun daman" ta fada tana lallashinta,sai data ga dama don kanta sannan tace
"Dubai yakeso mu koma ni shi da su'ad,daren jiya nace mishi su tafi ni sai cikina ya dada qwari zan taho,ya nuna bai amince ba,yau ummi tace masa ya barni a nan,kaman yadda jiya nace masa.....amira zaiyi tunanin na kawo qararsa ne"
"Dai dai kenan....kina zaton a barki cikinki bai qwari ba kibi waccan mai qirar amurkawan ta murqushe mana baby?,sai jikinki yayi qwari yadda baki buqatar mataimaki....ya almustapha kuma qyaleshi,tunda ummee ta fada haka dole zai haqura" shiru tayi tana nazari,kusan maganarsu na kan hanya,ba yau tasan mugun halin kishiya ba,ita sam bata ma yadda da yadda su'ad ke nuna cikin ko a jikinta ba bai dameta ba.

        Fitowar ummi ta sanya amira miqewa ta daneta tana cewa
"Ummina,i missed you"
"Nikam bansan me yasa saif ke biyewa shirmenki ba,duka duka yaushe kuka zo gidan nan wai?" Rai ta bata tana janyewa
"Wai ummi nufinki tun yanzu kin fara gajiya da ni,kinsan bazan iya zama ba banzo naga matar yaya ba,qaruwa fa muka samu" ta fadi tana maida kallonta gun sumayya data kauda kai tana mata dariya
"Gaskiya ne,kun kyauta ai" ta fadi tana zama amiran ta zauna tsakaninsu suna gaisawa.

        Kusan nan ta wuni saboda ba ranar kwananta bane bare ta koma gida aiki,zuwan amiran ya debe mata kewa sosai,sunsha hira kaman ba gobe,abinda bata sani ba shine,dawowan almustapha gida uku yana dubata ya tadda bata nan,abinda ya sake qona masa rai kenan,gani yake ita ta kai maganan wajensu ummi,abinda bai duba ba shine daga daren har wayewar gari suna tare baiga ta fita ba,ta ina zata iya kai qararshi.

         Sai bayan magarib ta baro bangaren,a sannan yana saman dining zaune da niyyar cin abincin dare,ya tasa abincin ne kawai a gabanshi,abu goma da ashiri ,ko kusa baya son abincin kuku,sannan ga damuwar sumayya a gefe guda,da sallama ta shiga falon,yana daga can saman dining,binta yayi da kallo cikin bacin rai ba tare da ya amsa sallaman ba,tun kayan safiya ne a jikinta abinda bai taba gani ba,hali take so ta sauya?mema taci wunin yau bayan yasan banda nama saiko shinkafa 'yar kadan take iya sawa cikinta,magungunan ta na yau ya duba baki daya ba wanda tasha,tana dab da shiga balcony da zai sadata da dakunan baccinta ta jiyo dakakkiyan muryarshi a atsawace yana kiran sunanta,hanjin cikinta ya kada ta runtse idanunta kafin ta waiwayo
"Daga ina kike?"daga kai tayi ta dubeshi don maganar ta mata banbarakwai,yana zaune ya hade hannayensa cikin na juna yana dubanta
"wajen.....waj....ummi"ta fada cikin dan daburcewa,sai ya miqe tsaye yana zuba hannayenshi a aljihun wandonshi ya dan tako kadan zuwa bakin step din dining din
"Ba sai kinyi haka ba zaki nuna baki qaunar kasancewa tare da ni,duka ba wannan ce damuwata ba...me kika baiwa babyna yau?,....tsaftar jikinki wanda tun kayan safe ne jikinki"
"Ai naci abincin da amira......"
"Amira?.....amira ita ta tsaidaki kenan ko?,ita tazo?" Ya fada cikin sigar tambaya da jin zafi,shiru tayi bata amsa ba,hakan ya sanyashi cikin hanzari ya fara saukowa daga kan step din zuwa qasa yana fadin
"Na baki mintina goma ki tabbatar kin sake wanka...ki canza kayanki....ki dauki abincinki kici kisha magani..." Ya qarashe maganar cikin huci yana kewayeta ya fice.

         Dariya su'ad ta saki wadda ta riski zancanshi na qarshe
"Sai haihuwa manya.....kinga kadan daga illolinta ko?,har kin fara qazanta kenan.....baki sani ba,bama zama da qazami,hakan yana nufin kin fara saitawa kanki hanya"ta fadi tana saukowa daga sama tsuke cikin riga da dogon trouser qoqarin daidaita kanta tayi kafin ta qiriqiro murmushi
" wani ko zai shekara baici ba wa ya damu da shi?,ke dai kiyi ta kanki,wadda ba'a damu da wuninta cikin gida ko waje ba,koda watar qasar ce kuwa ta shekara can,duka daya wajen wanda ya ajjeta"ta juya ta shige ta bar su'ad abin na mata zafi a rai,da ita take,tana yaba mata magana ne kan zamanta america almustapha na dubai,ranta ya baci qwarai,ta tsaya nan saman matakalar bene tana ciza yatsa.
Chapter 192 · 0% Book details