← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 226

Sashe 143

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       A qalla kusan awanni biyu suka share dakin c.s din saboda mutum biyu suka yiwa,kowanne anyishi successfull,a gajiye yake saukowa daga sama inda sukeyi aikin zuwa qasa,ya sanya maqulli ya bude,ya sanya qafafunshi masinjanshi na biye da shi,da sauri ya dakata sabida tunowa da yayi tana ciki,ya karbi kayansa dake hannunshi ya sallameshi sannan ya shiga ya rufe office din,sai da ya sanya wani sabulu ya wanke hannunshi cikin wani dan sink kana ya doshi qofar dakin,yana tura qofar ta farka,idanunta ta bude baki daya wadanda suka qara girma sakamakon baccin da tayi ta zubesu fes cikin nashi,sai ya janye nashi idanun yana fadi cikin zuciyarsa
"Kaman mayya" bai taba ganin idanun da yake jin nauyin sanya nashi ciki ba ko na waye irin wadan nan idanun,hakan ya sanya yake jin haushinsu,da hanzari ta gayara zamanta daga kashingidar da tayi saboda ganinsa da ya tuna mata inda take,wuceta yayi ya nufi inda kayanshi suke da alama zai canza ne hakan ya sanyata miqewa ganin lokacin azahar yayi,da sauri ta koma ta zauna inda ta miqe din zuciyarta ba bugawa,jini ne digo digo a inda ta tashin
"Yaya akai haka?,yaushe al'adan har tazo mata bata sani ba,bayan dazun nan ta lissafa wata biyu bata ganta ba" kamar wadda aka daure haka take jinta,bayansa tabi da kallo sanda ya kwashi kayansa yana yunqurin ficewa,tamkar ta tsaidashi haka take ji,ya zatayi  da jikinta?,ya zata yi da wajen?,abinda ta dinga fada kenan har ya fice,tana jiyo sanda aka ja waccan qofar ta office dim,wanda hakan ke nuna mata ya sake ficewa ne baki daya,hakan ya bata damar miqewa da hanzari,yaye zanin gadon tayi cikin sanda ta shige toilet din dake cikin dakin da shi,bandaki ne madaidaici wanda aka qawatashi,akwai komai a ciki na amfani harda soson wanka da nau'in sabulai ma ruwa da daskararre,wata roba dake manne da tambarin klien ta bude ta zazzaga ta soma wanke wajen,sai data tabbatar ya fita sannan itama ta gyara jikinta,fitowa tayi da zanin gadon ta baje shi saman katifar don ya matsu sosai,tana qoqarin maida hijabinta ta juyo sallama cikin office din,a hankali cikin sanda ta fito,nurse din dazu ce,cikin fara'a ta miqa mata wata leda wadda ke dauke da tambarin sunan gidan abincin seven thirty tana cewa
"Gashi inji yallabai" murmushi itama tayi mata da alama matar na da kirki ta amsa tana fadin
"Na gode" har ta juya zata fita ta dawo
"Ammm,ranki ya dade ba don kada nayi shishshigi ba da na tambayeki,don Allah matarshi ce ke?" Girma tambayar tayi mata,amma saita waske tana murmushi
"Qanwarshi ce" cikin murmushi ta sake miqa nata hannu
"Naji dadin haduwa da ke,suna na nurse barira" miqa mata yi itama tana murmushin
"Ameera" sakin hannun nata tayi sannan ta fice tana murnar ganin jinin gidansu doctor almustapha.

      Ledar ta bude qamshin da ya daki hancinta shi ya tabbatar mata abinci ne,sau wata ledar wadda tana budewa taga always ce a ciki,idanu ta zaro tana mamakin yadda akayi yasan tana buqatarta,bata wani tsawaita tunani ba ta dire abincin ta ciri pad din ta shiga bandaki ta saka ta jefa saurar a jakarta,gyara zaman hijabinta tayi sannan ta rataya jakarta ta fice a office din.

       Rufe laptop din yayi cikin dakin hutawarshi dake asibitin bayan ya gama kallon duk abinda tayi din,yana iya ganin kowane sashi na asibitin a dakin hutawar tashi ta na'urar cctv camera dake asibitin,ya dire cup din coffen da ya gama sha sannan ya tattare kayanshi ya sauko zuwa qasan.

       Idanu ta shiga rabawa ganin babu motar data kawota babu alamarta,da alama ya gaji da jiranta kenan ya tafi,babu mamaki,tun qarfe tara na safe suke gashi yanzun har uku tan gab da yi,bata ga laifin drivan ba ba,haka kawai ya wani tsareta bayan bata ga alfanun tsaretan da yayi ba,hakan ya sanya ta soma takawa a hankali don taje titi ta samu abun hawa gangar jikinya da zuciyarta duka a gajiye.

Tana yunqurin fita mai tsaron qofar wanda yake dattijo ne ya qaraso cikin girmamawa fuskarsa qunshe da fara'a
"Ranki ya dade,ai ya tafine wanda ya kawoki,yallabai yace ya tafi zaku tafi tare,yace ki tsimayeshi idan kin fito" murmushi tayi cikin gajiyawa
"Babu komai zan samu abun hawa,ina sauri ne kuma bai kammala abinda yake ba" ta sake sanya kanta zata fice sai ta kuma jiyoshi yana cewa
"Ranki ya dade gashinan ya fito ma ai" ya tunkaro get din yana qoqarin bude masa,tilas ta ja birki ta koma da baya ta soma takawa zuwa wajen get din saboda yadda idanuwa suka yi mata yawa,batasan me mutanen ke kallo tattare da ita ba haka.

Gidan baya ta sanya hannu ta bude ta shige ba tare da tayi tsammanin a bayan yake zaune ba,sai data rufe qofar sannan ta ankara da shi,yana zaune hakimce abinsa,maimakon suit dake jikinsa dazun yanzun shadda ce jikinsa mai gajeran hannu,iyakarta gwiwa da dogon wando
"Zaki ci wuyar zama da ni matuqar zaki kasance mai taurin kai da rashin jin magana" ya fada cikin muryarsa qasa qasa,ta gefan idanu ta kalleshi wayarshi yaje dannawa kafin ta maida idanunta kan titi,wayar ya ajjiye gefansa ba tare da ya sake cewa komai ba.

A tunaninta zasu maidata gida ne sai taga sun canza hanya,dubanshi tayi tana sake kallon titin
"Ba nan bace hanyar" ta yi magana tana kallon titin,sai da ya shaqi isaka sannan ya amsata
"Wacce hanya kenan?"
"Gidanmu mana"
"Baki da abinda zaki koma gidanku kuyi,so kin taho kenan" idanuwa ta zaro tana kallonshi cikin mamaki,wannan wacce iriyar magana ce haka?,me hakan ke nufi?,kallon mamaki taci gaba da yi masa kafin tace
"Ban gane ba,kawai daga zuwa asibiti sai ka zarce wani gun da ni haka akeyi?"
"Haka baba yace nayi,idan kuma ni din kwartonki ne sai ki gayan" ya fadi yana balle kwalin lemo ya kai bakinsa,ci gaba tayi da kallonsa baqinciki fal zuciyarta,so yake ayi abunda ba'a taba yinshi ba cikin tarihi kenan,idan wani ya fahimta wani bazai fahimta ai,wani zai iya dauka ita ta kai kanta
"Amma ba haka al'ada ta tanadar ba ai"
"Addini fa?,me ya tanadar?" Ya maida mata amsa cikin yanayin ko in kula,bata haqura ba dai duk a qoqarinta na fahimtar da shi,duk da yadda ranta ke baci
"Ko 'yar tsana ce ai tayi sallama da mu......"
"Shut up,idan kika sake magana zaki fitarmin a mota!" Ya fada cikin hargagi wanda ya tsoratata ya sanyata yin shiru,kanta ta kwantar jikin kujerar motar,bata ankara ba hawaye suka fara bin kuncinta tana daukesu,wai me yasa ba tun fari bata zabi abdur rahman ba?,ta tabbatar da cewa koba komai da tuni tana can cikin farinciki,itakam gaskiya bata jin zata iya da wannan mutumin mai shegen girman kai izza da taqama.

Bata fahimci airphort suka zo ba sai da motar ta tsaya ya fice yana bata umarnin fitowa,binsa kawai take jiki a sanyaye baki bude,qarar wayarta ta dawi da ita hayyacinta,number malam ta gani cikin hanzari da daga
"Jirgin naku bai tashi bane sumayya?" Cewar malam din,mamaki ya cikata,me kenan?,malam ya sani ne dama,kamar yasan me yake kai kawo a ranta yace
"Drivan muntari da ya dawo ya sanar mana shi mustaphan yace abuja zaku wuce,Allah ya tsare hanya,ki riqe aurenki da kyau mamana,kiyi biyayya kiyi kuma haquri,ki kauda kai ki zama mai kara,ki ninka haqurinki,in sha Allah ba zaki tozarta ba,ni nasan ba zaki taba wulaqanta ba gidan muhtari,Allah ya tsare hanya ga mamanki"
"Daga zuwa ganin likita sai ki gudu abinki kuma?" Cewar mama cikin salon tsokana,a zaton sumayya da gaske maman take sai ta sanya kuka
"Wallahi mama ban san shine ba,bansan tafiya zaiyi da ni ba"
"Keee,a kul na sake jin kukanki,wanne irin shirme ne wannan daga tsokana?,to dama me zaki dawo kiyi?,dukka qannanki fa kowa ta tafi nata gidan"
"Amma mama ni kadaice ba'a rakani ba,banyi muku sallama ba babu"
"Sallamar me zaki mana,sannan abujan baquwarki ce da sai an rakaki,mu kuma ba gashi muna sallama ba,kibi mijinki sumayya kiyi biyayya,yi nayi bari na bari,ki girmamashi ki tuna waye shi a wajen mahaifinki,kada ki sake yayi kuka da ke" nasiha tayi mata qwarai mai ratsa jiki,duk sai ta tafiyar da wani zafi da take ji cikin zuciyarta,kafin suyi sallam ta wanke mata zuciyarta fes da kyawawan kalamai sukayi sallama,bata ajjiye wayar ba sai data kira nafisa ta gaya mata tahowarra,jin ta fara cikata da tsokanar amarya ya da biyo miji haka babu ko 'yan rakiya,sai tazo tsuma amarya wai,sai ta kashe tana kada kai,tsokana cikin nafisa ita da amira tana da yawa,anty dije ta sake laluba ta kirata ta gaya mata,bata damu ba itama da jin tahiwarta ita da shi,saima farinciki daya cikata ta musu addu'ar isowa lafiya tare da shirin tarbar sumayyan,tayi niyyar kiran amira amma ta fasa,sai kawai ta tura mata tex ta kashe wayar.

Bayan ya gama sallamar drivan ya tako a hankali zuwa inda take tsaye don batasan abunyi ba,wayarshi dake aljihu ta dauki tsuwwa,ya laluba ya cirota yana duba mai kiran,su'ad ce,shafa wajen ansawar yayi ya daga ya kara kunnenshi
"Mustapha ina tafe zuwa abuja a daren yau ba sai gobe ba,ina son kafin na qaraso ka tabbatar ka saki wannan kidahuma bagidajiyar yarinyar mai yawo a hijabi,idan ba haka ba wallahi sai na tashi abuja" tsawa ya daka mata cikin matsanancin bacin rai tamkar tana gabanshi
"Kin manta da waye kike magana?,kin manta waye almustapha?,ok.....naga alamun kin manta,amma ina jiranki idan kika iso zan tunasar dake waye muhammad almustapha" ya datse kiran cikij bacin rai,ya zuqi iska mai zafi yana fesarwa,ya kashe wayar baki daya ya jefa aljihu yayi gaba,yana jin lallai wannan karon idan su'ad batayi wasa ba zai juna mata qaramin hauka ta iya ga inda ake babban,zai koya mata darasi mai girma,binshi tayi cike da tsoro da taraddi,haka yake da fada?,haka yake da saurin hawa?,wace tayi kiransa ya dugunxuma haka?,baki ta tabe tana biye da shi koma meye ba sabgarta bace.
Chapter 143 · 0% Book details