← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 177 OF 226

Sashe 177

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

       Knocking suka yi mata ta basu umarnin shigowa,amira ke gabasai sumayya,tana zaune a dakin ita da qannenta biyu da yayarta,idanunta kan sumayya fuskarta qunshe da fara'a,yayin da kunya ta yiwa sumayya katutu,don ta tabbata tasan ba gidan suka kwana ita da almustapha ba,a ladabce ta qarasa ta duqa tana gaidasu suka amsa a sake,nabila qanwar ummee wadda itama babba ce don tana da yara samari ke tsokanar sumayya
"Har yau baku kai mana ziyara kano ba,duk da dama wannan sarkin hade gabas da yamman sai sallah sallah yake zuwa mana,saidai ki jisu suna waya da mai martaba,da alama ma baisan jikinsa ya motsa ba bai gaya masa da tuni kin ganshi ya tashi hankalin kowa" dariya suka sanya ummee tace
"So nake kafin ya koma i yayi qoqari ya kaisu baki daya ita da su'ad din,don ita dinma dudud zuwanta nawa?"
"A'ah kibar ta wannan,itakam tunda baquwa ce sai ya kaitan,idan tana da sha'awa da kanta zata ko tasa ya kaita" inji hajiya saudat yayar ummee,hira suke kadan kadan kafin su fice don komawa bangaren anty mamaa,tsabar hadin kai da fahimtar juna ya sanya duk sanda wani abu ya taso cikin gidan walau na hajiya mamaa ne kona hajiya kilishi wato ummee 'yan uwan kowaccensj basa qasa a gwiwa wajen zuwa,run daga kan matasa yammata zuwa manya,akwai hadin kai da fahintar juna mai yawa tsakaminsu,kowanne family sunsan kowanne,haka 'yamnatan kowanne vangare na mu'amala dana kowa,kasanceqar duk sha'ani za'a hadu,sai duka suka zama kamar family daya.

       "Ina almustaphan ya shiga ne?" Akunyace ta amsa mata
"Ya wuce wajen daurin aure ne"
"To masha Allah" inji ummeen dadi yaja ratsata,
"Allah ya saka da alkhairi fa amiran umman khalipha,naji dadin yadda na fara ganin sauyi wajen almustapha,bama ni ba hatta da babansu,Allah ya qara miki juriya da qwarin gwiwa,naji labarin abokiyar zaman taki tazo,ina son inja hankalinki da don Allah kada ki biye mata da duk wautar da zata zo da shi,ki dauke kanki kiyi haquri da ita,idan kika fuskabci akwai abindabtake miki na cutarwa da ba zaki iya dauka ba,ki samu mijinku cikin salama ki sanar masa ya warware muku matsalar,kada ki soma yarda ki biye mata ku dinga abinda ba dai dai ba,kada ki yarda saboda ita ku dinga bata ran mijinku kinji"
"insha Allah ummee"
"Allah yayi miki albarja,ya akbarkaceku da zuriya dayyiba" addu'ar tayi mata nauyi,amira ce ta cafe
"Amin ummee,kai Allah dai ya nuna mana ranar,ummi da ido daya zaki bacci ina jin" ta fada cikin tsokana tana qyaqyata dariya,murmushi ya subucewa ummee
"Kinci gidanku,kin maidani kakarki ko?" Ta fada tana harararta,murmushi itama sumayya tayi,gwara da zancan ya tsaya nan kada ta hanata sukuni gaban ummeen.

       Bata jima ba ta wuce bangarenta,sanda ta shiga babu kowa falon,sai ta shige dakinta ta ware lafayar dake jikinta,kitchen ta wuce kai tsaye ta soma tunanin me zata dafa mishi?,don tuni ta sani wajen ummee baicin abincin taro idan ana yi,yankewa tayi tayi masa jallop din couse,sai ta tanada masa wani abun shan,shine zata gama cikin sauri kafin su shigo,cikin qanqanin lokaci ta hada komai ta dora.

Cikin mintina ta kammala jallop din wadda ta wadata ta kayan lambu da kuma hanta wadatacciya a ciki,kammala komai tayi waje guda ta soma hada lemo,shima bai dauketa lokaci mai tsaho ba ta gama ta kammale komai waje daya ta soma gyara wajen.

Cikin takun isa da izza ta shigo kitchen din,ta sauya kaya kamar yadda ya umarceta,a yanzun tana sanye da fitted gown na wanu lace mai azabar kyau da tsada,saidai bata daura dankwalin ba,sam sumayyan bata ji shigowarta ba,sai takun takalmanta masu tsini wanda ke haduwa da tiles din wajen suna bada wani sauti,a hankali ta waiwayo ta dubeta,sai ta dauke kai taci gaba da aikinta ganin ta shigo mata ne ba tare da sallama ba,bata tsaya ko ina ba sai data ci birki a gaban sumayyan wadda ke wanke sink data kammala amfani da shi,wani kallon sama da qasa ta yiwa sumayyan cike da tsantsar raini wanda sumayyan bata ma san tana yi ba bare ya dameta,aikin gabanta kawai take ci gaba da yi,itakam bata hango komai tattare da ita ba banda kyau da take da shi,sai tsantsar duhun kai,idan banda haka meye hadinta da daura zani?,meye na shiga kitchen tamkar matan daa?
"Ke" ta ambata cikin gatsali,sam bata nuna ta san da ita take ba,hakan ya quleta
"You african women dake nake" nan ma tayi banza da ita taci gaba da dauraye wajen tana gogewa da qaramin towel dake hannunta,hannu ta dora kan kafadar sumayyan ta juyo da ita suna fuskantar juna,murmushi sumayyan ta saki sannan ta dora hannunta saman na su'ad din ta saukeshi daga kafadarta tana fadin
"Sallama ya kamata ki soma kafin shigarki waje a matsayinki na diyar musulmi" ta juya taci gaba da aikinta,wani abu ya tsaya mata,itama za'a koyawa abinda ya dace
"Banga dama ba kuma bazanyi na,domin bani da shamaki cikin shiga duka inda naso a cikin gidan nan,gida dai na mijina ne so mallakata ne,ba wanda ya isa hanani shiga duk inda naso a sanda naso" waiwayowa tayi ta sake saki mata murmushi,mata na baki mamaki a yawancin lokuta,wato su duka son kansu ya musu yawa ne?,babu zaman lafiya idan su suka sameka cikin gidanka kamar yadda babu zaman lafiya idan kai ka tadda su,saidai zuwa yanzu ta tsike ya kamata itama ta shiga a dama da ita
"Oh sorry fa,may be labarin shafa fatihar dake tsakanin sumayya da almustapha bai isa kunnenki ba,idan kuwa har ya isa kunnenki to ya kamata kisam cewa nima matarsa ce kamar yadda kike matarsa,so kinga kenan matsayinmu daga,babu wanda nima zaimin shamakin shiga inda nakeso,saidai ni nawa addinin ya gayamin duk inda zan shiga na nemi izinin mai mallakin wajen kafim shigar tawa,wannan kadai shi zai sanyani neman izini bawai don nima ba matar doctor mustapha bace" kalamanta sunyi matuqar qona mata rai,ita take kallon idanuwanta take gaya mata cewa itama matar almustapha ce,sai ta gyara tsaiwa fuskarta na sauya launi saboda kishi
"Anzo point din,dama abinda nazo na baki shawara kenan a kai,ina mai baki shawarar sawunki a likkafa ki fita rayuwar mustapha,ki tattara ya naki ya naki ki koma gidan ubanki tun baki gamu da tuggun kishiya ba" abun ma sai yaso baiwa sumayya dariya,ta matse towel din data gama wankewa bayan ta gama goge gogenta ta dubu su'ad
"Ina zaton ke din farin shiga ce kan tuggun kishiya ko?,to mu ba yau muka fara gani ba,zagi kuwa ban tashi naga ana yi ba,don nasan makomar wanda ya zagi iyayen wani,shawara kuwa da kike ambata ai ciwo ce,baya ga haka ma kina iya riqe abarki wataqila nan gaba zata miki amfani" daga haka ta juya kan qafafunta ta soma takawa da niyyar barin kitchen din,zage zage su'ad din ta soma yi,tana son yayuaba baqa kamar yadda aka gaya mata saidai babu cikakkar hausa,hakan ya sanya ta dinga hadin gambiza da turanci
"Idan baki wasa ba nice ajalinki" shine kalmar qarshe data shiga kunnen sumayya yayin da take niyyar fita,hakan ya sanya ta waiwayo tana sake jifanta da murmushi
"Idan numfashina a hannunki yake yau kada na kwana a duniya" ta juya ta fice abinta,sam ko a jikinta,tasan sarai zata fuskanci sama da haka ma daga wajenta,saidai ba yau farau ba balle zuciyarta ta quntaya,meye ba'a yi mata ba?,har farautar rayuwar tata anyi.

Toilet ta fada ta sake wanka,sannan ta shirya cikin atamfa plain zani da fitted riga,ta fuskancu shigar na yawan qawatar da almustapha,yakan yawaita binta da kallo duk sanda ta yita,tana tsaka da shafa mai bayan ta sanya kayan ta jiyo sallama,hakan ne ya sanyata fitowa daga dakinta ta ratsa ta corridor dinta ta fito falon,abida ce matar hamza,cikin farinciki ta tarbeta ta jata sukayi dakinta
"Wai wannan wawuyar ta dawo ne na sameta tana zirga zirga tsakanin falo da dakinta ta kasa zama" abidan ta fada sanda take shirin zama saman doguwar kujerar dake dakin,sumayyan na saman dressing chair tana kwalliya,baki sumayyan ta tabe kana ta saki murmushi
"Gata kuwa kin ganta"
"To Allah ya kyauta,sai ki sake zage damtse ki rungumi mijinki" dariya ma ta baiwa sumayyan har sai data dara,daga nan suka shiga hirarsu,tana gaya mata ai ta dan jima ma wajensu ummee,hamzan ne ya sauketa ya wuce wajen daurin aure su da lamin,ta nan zasu dawo idan an kammala daura auren.

Bata fi minti talatin ba ta jiyo sallamarshi cikin muryarshi mai cike da izza da kwarjini,kamar wadda aka yiwa allura ta miqe,dariya abida ta saki sumayyan ta kalleta cikin dan jin nauyi don ta tabbatar qila yadda taga tayi saurin miqewan take wa dariya
"Mene ne" kai ta kada
"A'ah babu komai jeki abinki ina nan ina jira" ta fada tana miqewa saman kujerar,feshe jikinta ta sake yi da turare sannan ta fice.
Chapter 177 · 0% Book details