← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 226

Sashe 26

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

          Wani kuka ta saki bayan da taji tashin motarsa,meke shirin faruwa?,mukhtar ne yau ya tafi zance gun wata a gaban idonta bayan ya ganta tana kuka,mukhtar din da baison bacin ranta balle har yaga hawayenta?
"Ya rabbi yassir amrih" ta dinga fada bayan ta zame ta kwanta saman gadon tana digar hawaye.

          Kimanin awa biyu sai gashi ya dawo,lokacin qarfe goma har ta dan gota ma,a dakin nasa ya sake taddata kwance,da sauri ya isa gareta ya dagata ya zaunar yana duban idanunta da suka kumbura
"Subhanallahi.....sumayya meye haka?" Kamar jira take ta kuma fashewa da kuka,tsawon mintina talatin ya ciyo kanta bayan ya tursasa mata sunci abinci,sai da suka kammala sannan ya nemi magana da ita.

           "Ta hanyar yaya yahanasu zainab ta biyo sumayya,babu yadda za'ayi na iya bijirewa maganar,ni kaina ina jin yadda da auren cikin zuciyata bansan dalili ba,ba kamar auren fa'iza ba hakan ya sanya nake zaton QADDARATA ce zainab" yayi shiru yana jin quna can qasan zuciyarsa da wata iriyar takura,saidai daga sama yana jin kamar dole ake masa ya auri zainab.

         Jin shiru bata ce komai ba ya sanya shi cewa
"Yanzu haka cikin satin nan suke da buqatar na kai kudi a kuma saka rana baki daya,idan da alkhairi sai kiga ta haifa mana yaro ta sanadin haka kema ki samu naki" maganar sai tayi mata duka biyu,batasan sanda ta fashe da kuka ba
"Ta haifa maka dai yaya mukhtar,ni sumayya kam banda cikin haihuwa ai" tayi maganar tana mai niyyar miqewa ta bar masa gun,yunqurin riqota yayi ta kauce tana fadin
"Ka qyaleni kawai ya mukhtar,ka qyaleni kaje kayi aurenka,ka auri wadda zata haifa maka yara,na yarda nikam juya ce" ta qarashe maganar cikin gunjin kuka kamar zata shide,da azama ya riqotan ya rungumeta yana lallashi,sam sai kalmominsa suka gaza yin tasiri cikin zuciyarta,ta kasa bashi hadin kai wajen yin shiru da haquri
"Nace ma ka sakeni kaji ko?!" Ta fada cikin gunjin kuka.

         "Naqi na sakekin!" Ya fada a tsawace
"Yaushe kika koma haka sumayya?,yaushe kika koyi shegen kishi haka?" Ya fada yana kwantar da murya,a hankali ta daga kai tana dubansa,ta karaya sosai wannan karon,banbanci take hangowa qarara cikin idanun mukhtar din,sai ya janye idonsa daga kanta yana tuhumar kansa akan tsawar da ya mata,a tausashe ya janyeta gefan gado ya zaunar da ita sannan ya zauna daura da ita,cikin sanyin murya yace
"Kiyi haquri sumayya,baki na bazai gaji da baki haquri ba yau da gobe da kullum har ABADAN ma sumayya,abu daya zan iya gaya miki shine inaji a jikina dole ne nayi auren nan,bazan iya haqura da shi ba,ki yafemin sumayya,ki yafewa mukhtar dinki mai qaunarki kinji sumayyata" ya fada cikin raunin murya tamkaf mai shirin yin kuka,abinda bata taba ji daga gareshi ba kenan,idanunsa kadai zaka kalla ya tabbatar maka da gaskiyarsa,take tausayi so da qauna sukayi tasiri a kanta,ta rungumeshi tana fadin
"Babu komai ya mukhtar,Allah ne ya halatta maka,kaji tsoron Allah kawai ka kuma yi adalci"
"In sha Allahu sumayyata,ki tayi ni da addu'a" ya fada yana kuma qanqameta.

        ***       ***     ***

       Cikin abinda bai wuce sati uku ba aka kai kudi bayan sati daya mukhtar din ya hada kayan sa rana akwati biyu,bai shawarceta ba hakanan batasan zaya yi ba sai ganinsa tayi da kayansa,yace ta duba tace basai ta duba ba Allah ya sanya alkhairi,haka ya janyesu ya miqawa yaya yahansu,suna guda suna gwalli suka je suka kai kafin lefe ya qaraso,fadi suke Allah ne ya karya alqadarinta,wannan karo kam ta gamu da mai qarfin kurwa,kuma in sha Allahu zama daram tazo.

         Daga can bangaren zainab din ma haka suka gaya mata,sumayya bata barin mace ta zauna da mukhtar ko anyi auren saita tarwatsa abun,dariya zainab din tayi,don tasan komai game da sumayyan,tasan sarai akwai qarin gishiri cikin maganarsu,ta lura mutane ne masu jarabar son kansu da nasu,tilas tayi maganinsu tun da wjri,din ba zata lamunci abinda sumayyan ta lamunta ba,duk da hakan ba zama zatayi ta zubawa sumayyan idanu ba,koba komai diyar malamai ce bata san nasu shirin ba.

          Sosai sumayya ke ganin banbanci wannan karon,ashe da sam ba aure mukhtar din yayi ba,wani rawar kai sosai take gani dangane da shi,sabbin dinkuna yake da lissafe lissafe,tuni ya maida kai wajen ganin an kammala abinda bai kammalu ba na ginin sabon gidansa,ita kanta yace ta kwashe duka kayan dakinta ta siyar ko ta bayar zai sauya mata komai da sabo itama zata tare,saidai abinda ke daure mata kai wani lokaci sai ya hau qunci shi kadai yana fadin baison auren nan,sgifa yana jin tamkar ya fasa,bata san meye matsalar ba,data gaza gano haka sai taci gaba da addu'a kan Allah ya sassauta lamarin ya kawoshi da sauqi,don zuwa yanzu ta tsinke da lamarin kishiya,ashe a da tabbas quruciya ke cinta,batasan dadin mijinta ba sai yanzu,bata san meye kishi ba sai yanzu.

          Kayan lefe ya mata itama yadda ya yiwa zainab kowa akwati hurhudu,bata yi mamaki ba saboda budin da mukhtar din keta samu dai dai gwargwado.

          Biki ya rage saura sati biyu abdur rahman ya kawo mata ziyara,ta tarbeshi yadda ta saba,suka gaisa cikin mutunci,saidai wannan karo babu walwala da zolayar da suka saba,da ya tambayeta batayi qasa a gwiwa ba ta sanar masa,sosai ya mata nasihar da ta sake kwantar mata da hankali,ya jaddada mata ta riqi addu'o'inta,sosai taji dadi ta kuma gode masa,bai jima ba sukayi sallama ya tafi dama mukhtar din yazo nema kuma bai taddashi ba ya tafi zance gun amarya zainab.

Saura sati daya bikin ta shirya ta je gidan anty dije,da biyu taje don ta samu mai bata shawara,don sosai taji dadin shawarwarin da ta bata wancan karon,wuni tayi mata sur ta kuma qaru matuqa da gaske,taji dadin maganganunta wadanda suka sake kwantar mata da hankali.

Ranar da akema amarya jere ranar itama aka yi mata nata jeran cikin sabom gidansu,sai ya zama na tamkar amare biyu ne zasu tare,sosai zainab tayi rawar ganin hadawa kanta kayan daki,duk da haka babu abinda zata gayawa sumayyan,don itama wannan karon dai komai sabo ne,babu abinda ta shiga da shi tsoho banda sutura su dinma kusan rabinsu sababbi ne.

Ana ya gobe za'a kawo amarya ta tare,tare da 'yan rakiyarta suka je,sosai gidan ya burge kowa,duk da ba wani kantameme bane amma da girmansa dai dai gwargwado,da fari compound ne wanda ya dauke motar mukhtar din da wani space din daban,sai qofar da zaka bude wadda me dauke da babban falo guda d'aya,daga hagu da dama corridor ne guda biyu,daya na sumayyan daya na amarya,kowanne cirridor akwai daki falle biyu da toilet,daga falon akwai qofa biyu,daya ta kitchen dinsu ne mai yalwa wanda ka masa tsarin tsohon kitchen dinsu kowa da kantarsa,daya qofar kuma idan ka bude baya ne inda aka yiwa 'yan shuke shuke,anan falon mukhtar yake da bedroom dinsa shima,gida yayi dai dai gwargwado sai son barka.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

2⃣4⃣

_____________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*Man ja'a bil hasanati falahu ashru amsaaluha,wa man ja'a bis sayyi'ati fala yujza illa misluha*
_________________________________

      Bata gayyaci kowa ba baya ga mutanen da suka mata rakiya suka ga gida suka kama gabansu,hakan ga sanya randa za'a kawo amarya ita daya ce qwal,cikin dakinta tayi zamanta saboda falon nasu cike yake da 'yan kawo amarya,wadanda tun daga motsinsu ta karanci yanayinsu,su din ma dukkan alamau sun nuna babu arziqi,saboda haka tayi musu aji guda ta sanya su.

       Bata fito ba sai da taji motsin 'yan uwan mukhtar wadanda da su aka dauko amarya,fuska sake ta fito falon tana musu maraba,saidai kowanne wanu irin kallo yake binta da shu,ganin babu dole ya sanya ta juya ta koma dakinta tun kafin su yarfata cikin jama'a,yanzun kam ba da bace da quruciya ke dibarta balle ta nace sai an kula ta ko ta faranta ran wanda bai damu da nata farincikin ba.

            Ganin tara na dare yayi hayaniyar ta sarara da alama sun watse sun bar masu gidan da gidansu,sai ta miqe ta sanya turaran wuta cikin dakinta zuwa corridor dinta a burner din da anty dije ta siya mata guda biyu kyauta,take qamshin ya karade ko ina har zuwa falon nasu,wanka ta shiga ta tsala ado cikin wani marron material wanda aka yiwa ado da golden din zare,sosai ya fidda salsalar farar fatarta wanda jan lallen da tayi ya sake bada gudun mawa,baga wani cika kwalliya ba ta dai yiwa kanta barin turare kama daga humra,body spray body mist zuwa perfume na kaya.ta yane kanta da mayafi golden ba tare data buqaci daura dankwali ba ta kame gefab gadonta tare da janyo wayarta ta soma 'yan danne danne don ta dauke mata abinda take ji cikin zuciyarta.

          Qarfe goma taji sallamar mukhtar din cikin falonsu,burus tayi tamkar bata jishi ba,wani kishi da matsananciyat faduwar gaba suka ziyarceta,sai ta dakata da abinda takeyi din tayi shiru tana sauraron motsinsa da kuma bugun zuciyarta.

         A hankali ya yaye labulen yayi sallama,ta amsa ba tare da ta dubeshi ba,idanu ya zuba mata,ta masa kyau sosai tamkar yau take amaryarsa,wanu qaunarta ke taso masa ta wani lungu can dake saqon zuciyarsa wanda wani abu da baisan ko meye ba ke qoqarin fatali da abinda yake ji din,ya rasa me yaje ji cikin zuciyarsa a yau din,koda zaka ritsashi da bindiga ha zaya iya gaya maka ainihin me yake ji ba,farinciki koko baqinciki,ya jima cikin wannan yanayin wanda baisan sanda ya shige shi ba,da yayi yunqurin wani tunani kuma sai ya shagala,tunanin ya qwace masa.

        Ganin bata da niyyar cewa komai ya sanyashi qarasowa gefanta ya zauna yana zube ledojin hannunshi a qasa
"My sumy.....yau kan arziqin sannu da zuwan ma ban samu ba" ya fada cikin marairaicewa,a hankali ta dago kai ta kafeshi da idanunta wanda suka sanya yaji wata fargaba da kamashi,yayi kyau cikin shadda butter colour dinkin babbar riga,yasha askin saisaye da gyarab fuska wanda ya sakw fidda shape sin kyakkyawar fuskarsa.
Chapter 26 · 0% Book details