← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 226

Sashe 97

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda ya abbakar yazo shima baki ya saki
"Lallai nasan gobe mutuniyar anan zata wuni"
"Ni ya kamata naje yaya,ina babymu nasan ta fara wayi bata san mamarta ba(da yake matarsa ta haihu)"
"Ke dai kawai sai kin ganta,na tabbata ba zata iya haquri har kizo ba", malam ne kawai bai shigo da wuri ba amma ta gaza bacci sai da taga shigowarshi,kusan raba dare sukayi suna hira da shi,zuciyarsa na masa dadi duk sanda ya kalli diyar tashi,babu shakka rayuwa ta soma yi mata kyau,saidai a yanzun yana ganin ya kamata ta fidda abokin rayuwa ta sake aure,ko bai mata maganar yanzu ba zai fara yi mata jirwaye mai kama da wanka,zai tashi haiqan wajen yi mata addu'ar katari da miji na gari ita da 'yan uwanga baki daya,sai wajen sha biyu da rabi na dare suka rabu taje ta kwanta.

******** ******** *******

Washe gari a dakin malam din ta karya,ko wanka bata yi ba kayan bacci ne jikinta rida da dogon wando masu kauri,ta dora dogon hijabinta mai hannu,bayan sun kammala suka ci gaba da taba hirarsu,gayaran murya malam din yayi
"tunda gaki Allah ya dawo dake auren 'yar uwarki ina jin ba zai wuce wata biyu ba,dama su suka matsa da magiyar a bari ki dawo,basa son ayu bikin wai bakyanan,shima kuma abubakar ya goyi bayansu" murmushi tayi ta dan sadda kai a zuciyarta tana lissafin bayan bikin amira da sati hudu kenan?
"Alhamdulillahi,Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
"Amin ya Allahu,gwara ayi,hankalina sai yafi kwanciya,burina naga kowacce dakin mijinta,shine cikakken mutuncin 'ya mace,duk inda kika kai ga isa da dukiya nasaba da ilimi matuqar baki da aure baki kammala zama cikakkiya ba,don shine rabin,sai muyita addu'a,shi dama ibada ne,idan ka dace ka godewa Allah,idan ya jarabceka kayi haquri ka kuma nemi lada a wajensa"
"Haka ne malam,Allah ya tabbatar da dukkan alkhairi" kai ta sunkuyar,jikinta yayi sanyi,ba shakka ta fuskanci zaurencan malam,gugar zana yake mata,ita kam ina zata tsomala rayuwarta a yanzu idan malam ya taso mata da batun aure,da sauri ta nemi tsari kada Allah ya karkato da hankalinsa.

Cikin siyasa da qwarewa ta cikim hirar da suke yake jan hankalinta dangane da halayen rayuwa,babu shakka dukkan maganarsa izina ce kuma abar dauka,sosai taji dadin hirar da shi saboda yadda yayi mata tuni sosai game da wasu lamura masu matuqar muhimmanci ga rayuwar diya mace,ranar malam bashi ya fita ba sai sha biyu na rana,tun mama na leqosu taga ko ya gama shirin fitar har ta gaji ta barsu.

Sanda ta fito zuwa falon mama ashe anty amina matar yaya abubakar har tazo,dariya ta saki tana dubanta
"Tab,wlh anty kwata kwata banji shigowarki"
"Ina zakiji 'yar gaban goshin malam" zainab tayi caraf ta karbe
"Wallahi anty kema kya fada,baki daya faadar malam tata ce" karyar da wuya amina tayi
"Dole malam yaji da sumayya don gaskiya ba daya kuke ba,kun manta yadda rayuwa tayi da ita ne,QADDARA ta wajiga ta?"
"gaya musu dau matar yaya" ta fada tana amsar babyn fuskarta qunshe da fara'a tana cewa
"Ga babbar jika,ga babbar jika a mata" yarinyar kuwa dariya ta dinga bangalawa kamar ta gane wace sumayyan a wajenta,yarinyar kyakkyawa sosai ta biyo jinin gidansu sumayya.

Amina ke ta bin sumayya da kallo har sai data tanka
"Wai sumayya me anty dije ke baki haka,kinga yadda kika koma kuwa?" Dariya ta saki
"Haka kowa ke fada anty"
"Wallahi kin sauya baki daya masha Allah,boyayyen kyawun nan duk ya fito,yau dai na yarda kinfi abban yusra kyau" dariya ta tuntsire da ita,sabida sau da dama suna musu kan hakan amma taqi yarda,sai gashi yau ta sallama.

******* ****** ******

Washe gari qarfe sha biyu na rana ta shirya tsaf cikin african abaya,abaya ce me mix da atamfa wadda tasha kwalliyar duwatsu,tayi kyau qwarai,jaka da takalminta duka marching colour,gidan hajiya tayi niyyar zuwa yau,hajiyan abdur rahman,so take ta wanke kanta,don tasan sam bata kyauta ba,shiru kawai wancan karon abdur rahman yayi mata.

Ita da halima zasu je,saboda zainab ita yau ke da girki,suka yiwa mama sallama suka fice bayan tace su gaida mata hajiyan da bahijja,don shima abdur rahman din kwana biyu kenan bai leqo ba,abinda idan yana gari bai taba tsallake kwanaki biyun bai leqo ba,ba wani tazara ce mai yawa tsakaninsu ba,hakan ya sanya cikin mintuna arba'in mai adaidaita sahu ya saukesu bakim get din gidan suka sallameshi suka nufi gidan.

Tun kafin su shiga abdallah ya soma fadin
"Zamu gun daddy A ko?,gun hajiya da bahijja" kallon mamaki sumayya ke masa kafin ta maida dubanta ga halima
"Kai,wai yaron nan har gidansu abdur rahman ya sani?" Murmushi halima tayi
"Me zai hana,yaron dake wuni a gidan" shuru kawai tayi tana kada kai har suka shiga gidan.

Daga can bakim setting room ta hangi takalma,wanda hakan ke alamta masu gidan na da baqi maza,babu kowa falon sai bahijja dake kwance kan doguwar kujera,sallamarsu ita ta sanyata miqewa zaune,fuskarta taf da fara'a takewa sumayya sannu da zuwa gami da miqewa tsaye saboda murna da mamakin ganin sumayyan,ana haka hajiyan ta fito daga dakin da yake mallakin bahijja hannunta dauke da magunguna,lale marhabin ta shiga yiwa su sumayya suna gaisawa da halima,yayin data ja abdallah jikinta tana fadin
"Matso mai gida na,kwana biyu ban ganka ba,daddynka ya shiga rububi bude asibiti ya hanashi sukuni,hala ma kun ganshi?,don yana sitting room tare da baqi" murmushi sumayyan tayi a aladabce
"Bamu ganshi ba,amma kamar akwai mutane a wajen"
"Masha Allah,mutanen uk,tafiya ba sallama" ta fada cikin zolaya,sai kunya ta kamata ta sadda kai
"Wallahi hajiya,shirin tafiyar duk shi ya cinye lokacin amma naso zuwa"
"Babu komai,ai komai sai Allah ya nufa,kun dawo lafiya yasu dijen,kina wajenta ko?" Kai ta kada tana fadin
"Eh,lafiya qalau suna gaisheku"
"To madalla muna amsawa,bahijja miqe ki sama musu wani abu a kitchen kafin a gama abinci"
"Halan bata da lafiya ne hajiya?" Sumayya ta tambaya tana duban bahijja
"Bata jin dadi,kuma saboda wani iya shege bata da lafiya amma taqi shan magani,ta ina lafiya zata samu"
"Gaskiya kam" sumayya ta fada,ita da halima suka shiga,haka suka fito da snacks ruwa da lemo,yayin da hajiya ta ajjiye maganin ta basu wuri tana dauke da abdallah ko nauyinshi bata ji,yaron itama yana tuna mata mukhtar,akwai tsantsar kama mai yawa tattare da su.

Suna zaune suna hira bayan sun idar da sallar azahar suka ji sallamarsa,sanye yake da jallabiya ruwan madara mai haske,kanshi babu hula sai takaddu masu yawa dauke a hannunshi,idanu suka hada da sumayya wadda ke amsa sallamarsa
"Hala batan hanya kika yi?,ko ba sumayya bace?" Ya fada tamkar da gaske yake,dariya suka bushe da shi baki dayansu har ita,ya qaraso ya samu gefan hajiya ya zube cikin gajiya yana ajjiye tarin takardun hannunshi abdallah ya maye gurbin takardun ya haye masa cinyar,surutu ya fara yi masa yana biye masa yayin da yake amsa gaisuwar halima
"Hala ke kika tuna mata da mu ko halima?matar da ko ki sanarmin zaki dawo nijeria banyi wannan matsayin ba" Ya fada yana dubanta,hararar wasa tayi masa sabida hajiya ta bar wajen
"Tunda ita ta tunamin sai na tafi sai na tuno don kaina sai na dawo"
"Ni kike harara?,lallai idanunki sai isa yanka" dariya ya bata suka dara sannan ya soma tambayarta gajiyar tafiya mutanen abuja da sauran abubuwa tana amsa masa,saidai ta kasa sakewa saboda wani kallo da yake binta da shi,hakan ya sanya babu shiri qarfe uku na rana tayi haramar tafiya,ko ya lura a takure take ya sanya ya sauke abdallah bayan ya kammala cin abinci yace
"Bari na shiga na watsa ruwa sai na zo na kaiku" kai kawai ta daga ba don taso ba,ta sani dole a yau akwai abinda zai faru,tana tsananin kunya da jin nauyinsa a yanzu,ba yadda ta iya tilas suka jirayi fitowarshi.

Cikin wani yadi ruwan omo ya fito,yayi kyau sosai,yace su sameshi mota sanda suka tsaya yiwa hajiya sallama,ta ajjiyewa hajiyan turare da turmin atamfa data siyo mata,sai wata qaramar jaka mai kyau mai garai garai wadda ke dauke da set na kayan makeuo data siyawa bahijja,murna sosai bahijja ta dinga yi,yayin da ta dauki mayafinta tace zata rakasu dama ta gaji da kwanciya ko zata ji qwarin jikinta,godiya sosai hajiyan ta dinga mata tamkar bata fi qarfin abun ba,dama shi alkhairi dadi gareshi koda wanda ka yiwa din yafi qarfin abun indai yasan karamci.

Duka baya suka shiga ita da shi ne a gaba,bini bini ya juya ya kalleta,wani lokaci su hada ido wani lokaci ta basar,bai dai ce komai bar zuwa sanda wani go slow ya riqesu,wasa wasa sai gashi suna shirin cin mintuna goma bai motsa ba,ga hadari ya soma haduwa ya sanya garin yin duhu duk da har yanzu bai fara zubda ruwan ba sai zafi da ake fama da shi,bata mantawa lokaci iwar haka suka bar nijeria lokacin damina sai gashu sun sake dawowa sanda take shirim kamawa.

Baki daya motar dake gefansu wajen guda uku sun rufesu kasancewar sunfi nasu tudu,sai ta sauke glass din motar qasa,abdallah dake sit din baya ya zuro hannunsa yana qoqarin sanya mata yoghourt a bakinta wanda hajiya ta bashi wai tasha,bata kai ga sha din ba ya zuba mata a jiki,baki daya ya bata saman cinyoyinta
"Ya salam,ya salam abdallah ka bata min kwalliyar mata" abdur rahman ya fada yana laluba gefanshi ya dauko ruwa a cikin jarka ya miqa mata
"Budr murfin motar ki dan wanke gefan da ya baci kafin mu qarasa gida" karba tayi ta balle murfin motar ta dan zura jikinta waje zata soma wankewa,ganin mayafinta na niyyar shiga ya shafa shima ya sanyashi sanya hannu yana janye mata,dai dai lokacin da motar dake daura da su aka sauke nata glass din wanda zafi ya ishi wanda ke zaune sit din baya,tsaki yaja mai qarfi saboda ko kadan baisan a.c din motar ta lalace ba,driven bai gaya masa saboda sabbabi ne ko wata daya basuyi ba,wannan ne kuma hawanshi na biyu zashu rano,yayi niyyar hawan jirgi kuma babu jirgin da zai tashi kano to abuja a irin lokacin da yake son ya taho din,hakan ya sanyashi hawa mota.
Chapter 97 · 0% Book details