← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 226

Sashe 74

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ga lemo bismillah" amiran ta fada tana ajjiye tray data dora lemo da kofuna a kai,kai sumayya ta kada cikin murmushin yaqe tace
"Alhamdulillah,a qoshe nake"
"Al'adar gidan anty maamaa ne,dole kisha wani abu kafin ta fito" ta fada tana tsiyaya mata a cup,kallonta sumayya tayi tana yaba karamcin hakan,sai a sannan taga kamanni da wanda ta kira mahmoud a dazu,da alama kwai dangantaka ta jini mai qarfi tsakaninsu,hannu ta saka ta karba tana fadin
"Na gode"
"Ba komai,bari na duba girki kada ya kama"
"To" sumayyan tace,kurbe daya tayi masa ta ajjiye damuwa ke sakadarta,a haka taji an bude wata qofa dake can wani sashe daban na falon,anty maaman ce ta fito tana cewa
"Ayyah tun yaushe kika zo" murmushi tayi
"Ban jima ba,ina yini" ta gaidata amsawa tayi tana zama tare da amsar ledar humrorin,budewa tayi tana shanshanawa tare da yaba yadda sukayi bala'in qamshi,godiya tayi mata sosai tamkar ba biyanta tayi ba,miqewa tayi tana shirin tafiya
"Umhmmm,za'a gudun ne?" Amira take baro kitchen ta fada tana dan murmushi,waiwayawa tayi tana dubanta itama fuskarta qunshe da murmimushin,sam batayi zaton zata yi sauqin kai haka ba
"Na baro aiki ne a gida shi ya sa"
"Ayyah to sai yaushe?,ko sai na shigo?"
"Allah ya kawoki lafiya"
"Amin,ni sunana sumayya na gaskiya,sunan mamar babanmu ce ake kirana amira,kefa?" Murmushi ta saki
"Nima suna na kenan?" Idanu amiran ta zaro gami da rufe baki
"Kai kai,dama baabaa na kusa ya ganki,yaga mai sunan mamarshi,yana son mai sunan mamarsa wallahi,me ake ce miki to?"
"Shi ake gayan" kai ta kada sannan tace
"Gaskiya ni bazan fadi haka ba,zan dinga kiranki kema da amira,amiran umman khalipha" dariya sosai sumayya tayi
"Shikenan to" ta amsa mata sannan sukayi sallama ta juya da niyyar fita tana dariya amiran,kusan zasuyi shekaru daya da ita,saidai yanayin inda ta taso da gata sai take ganin kanta kamar qaramar yarinya,duk da aqalla zasuyi shekaru ashirin da daya.

A bakin qofar shigowa falon taji tayi karo da abu har yana bangazar kafadarta,da sauri ta ja baya tana fadin
"Subhanallah"
"Mtsweeeeww" taji an tsaki,baya ta sake ja tare da daga kanta tana kallonta wanda ita dinma kallonta take,saidai nata kallon yasha bamban da wanda sumayyan ke mata,kallon farko ta fahimci macace mai izza da jin kanta,haka yake don sumayya bata yi qarya ba,matashiya ce dake jin duniyarta dai dai,wadda a qalla ta doshi shekara ashirin da takwas a duniya,doguwa ce sosai hakanan siririya ce,fara ce itama sosai kamar yadda sauran suke,sanye take da wani baqin hight rise slim leg jeans da v neck t.shirt mai gajeran hannu,hakan shi ya fiddo surar ta da shape dinta baki daya,kanta yane da wani dan kwali mai santsi don ba za'a kirashi mayafi ba,idanunta saye da sun glases da ya kusa cinye rabin fuskarta,wani kallo take wa sumayyan na sama da qasa cikin izgilanci kafin ta zare gilashin nata,tsaki ta ja kafin ta wuce tana taku dai dai tana duban amira
"Maamaa fa?" Ta tambayi amira kamar bata son yin magana
"Ta haura sama" ta fada tana nufo sumayya dake gab da ficewa daga falon,da sauri ta daga murya
"Kiyi haquri sumayya" amiran ta fada cikin damuwa,sai ta waiwayo tana sake mata murmushi tare da fadin
"Kada ki damu", sai da sumayyan ta fice sannan ta dawo da kallonta cikin falon ta saukesu kan wadda ta shigo din,sai ta kada kai kawai ta shige kitchen ganin ta zauna saman kujera tana jiran saukowar maamaan,ta sani sarai ba zata iya haurawa saman ba dama idan ba da wani qwaqqwaran dalili ba,shi ya sanya tayi saurin komawa kitchen don kada ma tace zata aikata.

Tana hanya tana tuna irin kallon da ta yi mata,a qa'ida ita ta bigeta,ranta yaao baci amma sai ta dorama kanta laifin,ko ba komai ita tazo musu gida,tana isa gidan ta bawa anty dije labarin amiran,
"Amira kam akwai son mutane ai haka take ita da mahmoud ai mutane na ne"
"Eh kam na ganshi shine ma ya rakani wajen anty maamaa,yana da kirki sosai"
"Shine d'a na uku a wajen ummee"
"To ita amiran 'yar waye ne anty,yau tana can gobe tana nan"
"Itama d'iyar ummee din ce"
"Ita ummin bata da yara ne?" Hararta tayi tana cewa
"Yau kin zama 'yar jarida,to ban sani ba,ai baki son jama'a ne,banda haka watanki nawa a gidan nan yaci ace kin gama saninsu,tunda alhamdulillah mutane ne masu kirki karamci da son jama'a" dariya sumayyan tayi tana kame bakinta da yatsunta
"Ni dama amiran nake son na san 'yar ina ce kuma an gayan" sai suka yi dariya anty dije na qorafin qib sakin jiki na sumayyan.

Da daddare dukkansu suna zaune a qasa suna cin abincin dare har da mai gidan,sumayya ce kawai ke zaune can gefe tana cin nata,babu yadda anty dije da uncle farouq baiyi ta dinga cin abinci cikinsu ba amma ta kasa,kunya gareta,bata da sabo sosai idan ba wajen yara qananu ko mutanen gidansu da suka taso tare ba,tun suna qorafi har suka suka haqura suka zuba ido a haka suka saba saboda sun lura halittarta ce ba zata sauya ba.

Sai da suka kammala baki dayansu sannan hafiz yace cikin doki
"Abba,wanne albishir ne da kace sai mun gama cin abinci zaka yi mana?"idanu ya zaro yana murmushi yana duban hafiz din
" ummm,wannan zumudi haka?"
"Eh wallahi abba nima na qagu ya rigani fada ne kawai a baki" juyawa yayi yana kallon lailan,wannan karon dariya ce ta subuce masa
"Au kema?"
"Eh abba" ta fada itama tana dariyar,sai ya dubi anty dije
"Kefa madam?" Murmushi tayi tana gyara zama
"Ai yara sun gama magana,nima na zaqu inji wanne albishir ne?" Dariya ya sake yi
"Uhmmm,shine kenan to tunda bakinku yazo daya" ya fada yana gyara zamanshi,sumayya na gefe tana satar kallonsu,yanayin rayuwarsu tana burgeta,soyayya dake tsakanin uncle farouq da anty dije kullum kamar wasu sabbin aure,waiwayawa yayi ya fito sumayyan da hannu
"Taso kema ya shafeki" sai tayi qasa da kanta sannan ta miqe ta qaraso tana murmushi,gefan laila ta samu ta zauna,duk sukayi shiru suna sauraronsa.

"Alhamdulillah,Alhamdulillah" ya fara cewa
"Wato a yau labari ya iskemu gwamnatin tarayya ta aiko da takarda ma'aikatarmu,ta zabemu mu goma zamu tafi london bayan sallahn nan mai zuwa da sati daya,zamu qaro karatu don samun qwarewa kan aikinmu na tsawon shekara guda" ya fada yana sauke numfashi,duk sai fuskokinsu suka sauya,kowa da abinda ya fara yawo cikin zuciyarsa,suna wassafa yadda zai tafi ya barsu da yadda zasuyi kewarsa,dariyan da ya saki ita ta maido hankalinsu kanshi
"Jibi fuskansu,to gwamnati ta bamu daman tafiya da iyalanmu amma kada su wuce mutum hudu,shine babbar matsalar,gashi mu mun kai mu shida,tunani daya wa za'a bari da wa za'a tafi?" Shuru dakin ya dauka,murna ta soma komawa ciki,kowa na zulumin kada ace shi za'a cire,banda sumayya da farinciki ya mamayeta zata koma kano kenan har tsawon shekara daya,don dama ko a mafarki bata zaci ma zata bar state dinta ba balantana akai ga qasarta,ganin ba wanda yace komai sai sumayyan tayi gyaran murya don fidda abinda ke cikinta,dubanta uncle farouq yayi yace
"Ummm,me zaki ce?" A ladabce tace
"Dama uncle.....cewa nayi.....ni mai zai hana a cireni a lissafi sai na koma kano kafin dawowar taku?"
"Shawara bata karbu ba" anty dije ta fada kanta tsaye,sai ya saki dariya yana kallon sumayya
"To kinji abinda antynki tace" yana maganar tare da mai da hankalinsa kan anty dije
"To ke hajjaju mai zai hana cikin taskarki din nan da ake boyo ki dauki nauyinmu baki daya?" Ya fada cikin zolaya wanda hakan ya sanyasu dariya baki dayansu,sai da suka nutsa sannan yace
"Ni a binda nake gani,hafiz,kai zakayi haquri saboda karatunka a yanzu yake buqatar nutsuwa da dagewa,kai zamu bari a nan garin,sumayya kuma kema 'yar mu ce,kinga kuwa mai 'ya mace bazai dinga barinta wani gu ba,ni zan yi mata passport da visa a kudina,shikenan madam?"murmushi ta saki
" yayi yallabai,mun gode Allah ya saka da alkhairi ya qara arziqi"hafiz wanda sam baiji dadi ba har cikin ranshi,amma da yake yarone mai hankali da haquri,da wuya ka gane bacin ranshi sai yace
"A wanne gida abba Zan zauna?"
"Duk inda ka zaba,ko gidan inna(kakarsu da yake nan ya dawo da ita,ba wata tazara bace mai nisa tsakaninsu),ko gidan baabaa prof,kayi haquri kaji hafiz,girman kenan kaji?"
"Ba komai abba" ya fada,sai ya baiwa antu dije tausayi
"Ni har ka tunan ma abban laila,ina zuci zuci sukai sumayya ta gaidata,innan tace wai ba zata iya gane sumayyan yanzu ba"
Yana miqewa yace
"Kinsan tsufa sai a hankali,ai babu damuwa ko zuwa gobe ko jibi sai suje"
"Allah ya kaimu" injita,miqewa hafiz din yayi yabi bayan abban nasa da ya kirashi yace yazo ya karbi wani abu,take falon ya sarqe da murna,laila anata wassafa kai a jirgi,sumayya na dubanta tana dan murmushi duk da hankalinta ya kasu kashi biyu,ran qwashi anty dije ta zuba mata tace kota nutsu ko ta saka a cire sunanta a saka na hafiz take ta kame bakinta duk da bata fasa mutsu mutsun murna ba.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣8⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*KO KUNSAN ACIKIN 'YAN WUTA WAYE MAI QANQANUWAR AZABA MAFI SAUQI?,WANDA AKA FI SAUQAQAWA??*

*Shine wanda za'a sanya garwashin wuta a tafin qafafunsa guda biyu,kowanne tafi daya garwashi daya,sai qwaqwalwarsa ta dinga tafasa*

*ALLAHUMMA AJIRNA MINANNAR*

__________________________________

      Falon anty dije ta basu tana fita laila ta dora daga inda ta tsaya,har gwada irin shigar da zata dinga yi take idan suka tafi,sumayya na gefe tana kallonta tana dariya,can qasan ranta kuwa tana ta jujjuya maganar,wai itace zata wata qasa wata uwa duniya a jirgi har london?.
Chapter 74 · 0% Book details