← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 226

Sashe 71

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamin wani lokaci sun gama kintsa komai,sai da suka ci abincin sannan suka yi wanka kowacce tayi shirin kwanciya,tana saman gadonta lullube da bargo saboda ac da laila ta kunna wayarta ta soma haske sabida ta maidata silent,abdur rahman ne kamar ba zata daga ba saboda bacci take da buqatar yi,amma sai taga hakan bai dace ba,a mutunce ta gaida shi ya shaida mata ya kirata dazun kiran bai shiga,ta sanar masa,mai yiwuwa lokacin suna kan hanya ne ba service,qorafi ya shiga yi mata kan dalilin tafiyarta bata sanar masa yace
"A qalla ko addu'a sumayya na miki ko?,har yau kinqi gayan dalilin da ya sanya baki sona" baki ta bude kamar yana ganinta
"Ni bance ma bana sonka ba abdur rahman,kawai dai ina da buqatar hutu ne cikin rayuwata,har yau zuciyata da qwaqwalwata basu zama fresh ba,kuma ko baya ga haka ma banson na zalunceka,don banajin akwau mahaluqin da zanso kwatankwacin mukhtar,zanfi so na qarashe rayuwata a haka naje na tadda shi a inda yake" shiru ya ratsa wayoyin nasu kafin daga bisani ya sauke ajiyar zuciya
"Wannan ba hujja bace,amma har zuwa yaushe kike ganin qwaqwalwarki zata zama fresh din na daga miki qafa zuwa wannan lokacin?"
"Ban sani ba nima abdur rahman,ban da masaniya" ta fada da alamun ta fara karaya,shuru ya sakeyi,ta tabbata sumayya abar tausayi ce,hakanaj dole ayi mata uziri,amma ya ya iya bazai iya rabuwa da ita ba,tsakanin jiya da yau kawai lissafinsa ya dagule,aikin da ya tafi sokoto domin shi ya gaza aiwatar da komai
"Zan bar miki maganar da baki so har zuwa sanda zaki buqaci haka,saidai ina son don Allah mu maida dangantakar mu ta baya ta wa da qanwa,idan na kiraki ki amsamin kamar dan uwanki kin yarda?"
"Anya hakan ma zai yiwu?"
"Mai zai hana kin manta abdur rahman ne dan zaman dakinki?" Dariya ya sanyata wadda ta taho da hawaye,ya tuna mata wani abu can baya,wani abu da bazai taba goguwa cikin KUNDIN tarihin rayuwarta ba,dadi yaji cikin ransa da ya fuskanci ta sake,bai wani cikata da surutu ba sosai yace ta kwanta tayi bacci zaya kirata gobe yaji yaya kwanan abuja.

*WAI INA ZAINAB NE?*

Tun sanda aka kaita asibitin ta soma gane Allah da girma yake,ga cutar qanjamau dake cin kowane sashi na jikinta,ga qafa wadda ta tasamma rubewa koma ace ta rube,ga hannu daya kullum daurw da ankwa jikin qarfen gado,gwajin farko aka gano cancer ta shiga ciwon saboda haka tilas a yanke qafar kada dayar ma ta harbu,kuka ta dinga yi wiwi da idanuwanta sanda aka nemi kudin da za'a biya ma a samu a yanke qafar aka rasa,ita ta shawarci mamarta da cewa
"Mama,ko kadarorina dake cikin dakina za'a diba a saida a biya tunda ku kun kasa biyamin,bakusan bala'in da nake kwana nake tashi a cikinsa ba" kallon banza maman tayi mata ganin cewa har yanzu bakin zainab din bai gama rusuna ba,duk da halin da take ciki
"Wadanne kadarori kuma kike da su,bayan wadanda kika aiko zinatu ta diba ta saida miki ta kaiwa alqali kudin don ki samu nasara kan shari'arki,da yake Allah ba azzalumin bawa bane gashinan abinda kika aikata yana bibiyarki" ihu ta kwarara wanda ya janyo hankalin jami'an tsaron dake gadinta,wadanda basa rabuwa da ita koda tayi bacci,rantse rantse ta shiga yi kan cewa ba ita ta aiko zinatu ba,maman taje ta nemota duk inda take damfararta tayi,kudin da take sa ran za'a dinga juya mata ana aiko mata da su don tayi rayuwa mai kyau da'yanci cikin kurkuku(kujifa,ita da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai amma zuciyar da sauran buri har wata rayuwa mai kyau take hangowa kanta),rirriqeta ta jami'an tsaron sukayi sannan suka sanya likita yazo ya danna mata allurar bacci maman na kallo,a hankali jikinta ya saki har bacci ya dauketa,kuka maman ta sanya bayan 'yan sanda sun aikata waje don basa bari ma a ga zainab din,tausayin 'yar tata kuma sai ya kamata,duk da irin tsiyar da zainab din ta shuka tun tana budurwa kawo yanzu,asirin data yiwa maman ma kusan sai da aka daureta gidan yari ya saketa, ta sani cewa maiyiwuwa zaluncin da itama ta tafka tsakanin kishiyoyi zamanin mijinsu na raye shine alhakin ke bibiyarta Allah ya sauko mata da wannan jarabawar,wato shi sharri kare ne maishi yake ba,hakana sharri dan aike ne,duk inda yaje gun wanda ya aikeshin yake dawowa.

******* ******** *******

Washegari da gyaran gidan suka tashi kasancewar 'yar aikin anty dijen itama ta tafi garinsu,babu tabbacin dawowarta ma don suna tsammani aure za'a yi mata,basu samu kansu ba sai la'sar sannan suka kammala komai,daki sumayya ta shiga tayi wanka sannan ta fito ta shirya cikin riga da zani na atamfa,ta zura hijabinta kenan zata tayar da sallah wayarta ta dauki ruri,mama ce sai ta koma bakin gado suka gaisa,sannan daga bisani ta buqaci ta kaiwa dije zasuyi magana ta kira nata layin a kashe,kiran ta katse sannan tayo falo don ta haura sama ta miqawa anty dijen wayar.

Kyakkyawar budurwa ce tsaye a bakin qofar falon,farace mai matsakaicin tsaho,sanye take da yadin material plain mai santsi da kauri ruwan makuba(maroon)tayi rolling da mayafi ruwan hoda wanda ya sauka iya kafadunta,takalmin qafarta mara tudu(plate)ne shima ruwan hodar,fuskarta fayau babu kwalliya sai kwalli kawai,kallo daya zaka yi mata kasan cewa akwai hutu kwainane da boko zalla a gun,a qalla zasuyi sa'anni da sumayya,minal na tsaye gabanta tana ta tsalle,yayin da budurwar ke qoqarin budewa minal choculet data shigo mata da ita,daga kai tayi suka hada ido da sumayya,sai ta maida kanta ga minal,hakan ya sanya sumayyan itama dauke kanta don bata santa ba ta nufi matattakalar benen don ta haura sama,sai muryar anty dije dake saukowa ta dakatar da ita
"A'ah amira ya kike tsaye,samu gu ki zauna mana"
"Ba komai umman khalipha,sauri nake zamu fita ne da anty su'ad,sai malam alqasim yace min yaga dawowarku na shigo inga mutuniya ta" dariya anty dijen tayi tana qarasa saukowa
"Mutuniyarki kam ai gata nan,yasu maamaa"
"Maamaa lafiya tace in gaidaki"
"Ina amsawa,kice su'ad anzo kenan" dan murmushi tayi
"Eh wlh,bari na wuce umman khalipha"
"Af tsaya mana na baki saqo wajen maamaa"
"Umman khalipha sauri nake,amma may be idan mun dawo da wuri zan biyo na karba mata,banso ma akai su'ad na nan" ta fada a shagwabe kamar wata qaramar yarinya,dariya anty dije tayi don tasan dawar garin
"To shikenan,sai kun dawo"
"Tom" ta fada tana jan kumatun minal tana mata bye bye bayan ta dan sake duban sumayya dake danna wayar ta tana laluben mama don ta kira ma anty dije ita sannan ta miqa mata wayar,karba anty dije tayi tana fadin
"Kun gaisa ne da amira" kai kawai ta kada
"Kai amma dai baki kyauta ba,da na ganku tare ai na zaci kun gaisa sumayya"
"Bansanta ba anty,kuma ko da na fito bata min magana ba,hasalima dauke kanta tayi"
"Qaniyarki,ba gidanku tazo ba" dariya tayi cikin tsokana tana rufe baki
"Af,na manta gidanmu fa tazo afuwa umman khalipha" itama ta fada,sai ta baiwa anty dijen dariya,saboda kusan da wuya kaga sumayyan na zolaya ba al'adarta bace sai lokaci zuwa lokaci,daki ta juya ta shige tana fadin
"Idan kin gama anty ki bawa laila don Allah ta samun chargy"
"To" anty dijen ta amsa tana amsa kiran wayar.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣6⃣

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Wa wassainal insaana bi walidaini ihsaanaa*

*mun yiwa mutum dan adam wasiyya/umarni da kyautatawa iyaye(uwa/uba)kyautayawa(matuqar kyautatawa)*
________________________________

      Tana idar da sallar minal ta shigo dakin da gudu
"Anty kizo ana kiranki a waya"
"Waye yake kirana?" Bata amsa mata ba yarinyar sai jan hannunta da ta soma tana nuna qofa da yatsarta,murmushi tayi don tasan halin minal din,sai kawai ta miqe ta bita,tayi tsammanin wayarta dake gun anty dije ake kira,saidai bata tsaya ko ina ba sai kitchen,ta dangana da ita zuwa bakin wayar su ta landline
"A nan ake kiranki" cikin mamaki tace
"A nan kuma,ba wayarku bace ta gida,saidai ko anty ake kira ko?"
"A'ah sumayya suka ce" inji anty dije dake shigowa kitchen din,cikin shakka da ko kwanto ta daga bayan wayar ta sake sakin qararrawa.

      Nemam wajen zama ta soma yi jin muryar namiji,gabanta ya yanke ya fadi tsoro ya kamata,ta tsani abinda zai hadata da namiji,ta amsa gaisuwar da ake mata sannan mamallakin muryar ya soma magana
"Nasan baki sanni ba duk da kin taba ganina sau daya,amma nasam zaki iya tunani,shekaran jiya na ganku a wani restaurant dake kaduna ke da qannenki da yayarki,so naso na tare ki na miki magana sai kuma kunyar idon mamanki ya hana,na lura akwai sanayya tsakaninku da masu wajen,gurinsu na amshi lambarku ta gida"
"To sai kuma akayi yaya?" Ta fada gabanta na faduwa tana neman wajen zama saboda sanyi da jikinta yayi,tana mai fatan alaqar ta yanke daga nan,murmushi yayi wanda har sai data jiyo
"Haba yi a hankali mana beauty,ni da nake so mai qulla dangantaka da alaqa mai kyau?"
"Me kake nufi?" Ta tambayeshi gabanta na faduwa
"Kin gane,tun ranar da na dora idanuwana a kanki Allah ya dora min qaunarki,duk duniya naji babu wata diya mace da zuciyata ke so da qauna sai ke,hakan ya sanya na kasa haquri da ke,ina kuma fatan zaki karbi maganar da hannu bibbiyu"
"Hmmmm,Allah sarki" tayi qarfin halin fada tare da kife kan wayar ta miqe ta fice daga kitchen din,baki daya jin zuciyarta tayi ta quntata,itakam duk yadda take qoqarin killace kanta bata tsira ba?.

       Kusan ragowar ranar baki daya a daki tayi ta,dadin abun ma suna tare da su laila,kwanakin qarshen mako ce,sai jibi litin zasu koma.

  *******   *******   *******
Chapter 71 · 0% Book details